← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 65

Sashe 38

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin bata amsata ba yasata karkatowa tana dubanta, ta yab'e baki tace "An tab'o ubanki Attahiru ai dole ki gimste fuska, toh kifi shanu, ke nifa had'e ku zanyi daga ke har Attahirun na wanke ku tsaf babu ruwana ehe, wllhi idan dai akan maganar aurensa da wancan mai k'irar jiminar ce saidai kuyita fushi, idan kun gama zaku sauk'o da kanku...." ta k'arashe maganar tana goga ashwakinta a bakinta...

Sallaman Ashfaq ne ya kaste Hajiya, mik'ewa tayi tana gyara d'aurin zani ta nufo parlor tana fad'in "Ah'ah wa nake ji kaman Keenafas, lale-lale maraba likita bokan turai, shigo abinka..."

Ashfaq yayi sallama had'i da d'ago labulen parlorn ya shigo fuskar sa cikeda fari'a.

Saman carpet ya zauna yana gaida Hajiya, ta amsa masa cikeda sakin fuska suka soma tab'a hira don Ashfaq babu laifi akwai barkwanci, nan yake tambayarta Maryama..

Tab'e baki Hajiya tayi ta yunk'uro ta lek'a k'ofar d'akin kafin ta rage murya tamkar mai rad'a take fad'in "Gata can ta d'ane bakin, wai fushi take dani nace kar taje bikin Attahiru.."

Ashfaq ya murmusa yana mai jin dad'in hiran Hajiya kana yace "Ai ya kamata taje Hajiya, tunda nazo ai sai na kaita..."

Hajiya ta kuma tab'e baki kana tace "I yayi, ai sai ki fito keenafas ya kaiki, nasan idan bakije ba kwana zakiyi kina min zunb'ure zunb'uren baki,... Ina kike ne.." ta fad'i tana d'aga labulen d'akin.

Still fuskarta babu walwala ta fito, ta d'an k'ak'aro murmushi tana gaida Ashfaq da ya kafeta da idanu yana sakar mata sassanyar murmushi...

Kallon Hajiya ta d'anyi don ita sam ba so take Ashfaq ya kaita ba tunda tasan Uncle baison irin hakan.

"Hajiya fah Uncle yace zai turo malam Habu ya kaini, nasan k'ilama yana hanya." ta fad'i a shagwab'e.

"Yo saidai idan kin fasa zuwa muyi zaman mu, ke wai yaushe kika koyi wannan felek'e da d'an banzan ra'ayi irin na Attahiru ne, idan baki zuwa keenafas kayi zamanka abunmu mu sha hira."

Marayama ta turo baki ta cika tayi fam, Ashfaq duk sai yaji babu dad'i, baison ganin ranta a b'ace.

Duban Hajiya yayi kana yace "A'a Hajiya mu jira mai zuwa d'aukan nata ya iso tunda Ya Dr zai turo sa..." yayi maganar yana satan kallon Maryama. Ita kanta Maryaman sai taji babu dad'i, kaman bata kyauta ma Ashfaq ba.

Mik'ewa tayi don tasan idan taci gaba da zama yau sunyita haurawa da Hajiya kenan, ta d'auki d'an handbag d'inta tace "Ya Ashfaq muje ka kain pls.."

Ta juyo ta dubi Hajiya baki a ture tace "Na tafi..."

"Toh Allah Ya tsare, Keenafas ka kula min da d'iyata, idan suka k'ala maki wani sharrin wllhi ko zan masu diran mik'iya don na sansu dangin Kulu dangin jaraba, dangin tsiya.."

Maryama tazo wuya, yanzu a gaban Ashfaq Hajiya ke maganar nan ko oho babu ruwanta, cikin sauri ta fice tana fad'in "Hajiya sai na dawo..." Ashfaq ma sallama yayima Hajiya ta kuma jadadda masa ya kula da walta.

Shaf ya mance da batun kai Maryama event d'in Shema'u, cikin sauri ya tattara files d'insa ya katse ganin patients ya fice, sosai yake falfala gudu saman kwalta.

*********

Ba k'aramin dad'i taji ba ganin yanda ya kuma damuwa da ita, ta nemi bak'in cikinta ta rasa, a hankali ya bud'e mata marfin motar ta shige fuskar sa d'auke da mayaudarin murmushi mai narkar da 'yanmata, tana shigewa ya tada motar.

Ashfaq da karyo kwanar su kenan yaga sanda Sajida ta shige cikin wannan bak'ar motar, tsaf ya gane motar jiya a ciki ya ganta ta fito, yau gashi sun fice. Zuciyarsa ta cika da shakku, ya juyo ya dubi Maryama data dafe face d'inta daga kauce ma hasken rana, da alama bataga abinda ya faru ba, baice komai ba ya had'iye zancen amma sam zuciyar sa bata kwanta ba da wannan bak'ar mota mai bak'in gilashi ba dukda bai tab'a ganin mai motar ba.

Sosai Maryama ta masa godiya zata shige ya ambato sunanta a hankali, juyowa tayi tana dubansa ganin ya mata k'uri yasata sadda nata kan k'asa.

Murmushi yayi kafin yace "Inaso na ce maki sunan mahaifiyata gareki so ina respecting sunan sosai, if you don't mind zan fara kiranki lil sis."

Murmushi itama ta masa kafin tace "Babu komai Big bro..." a tare suka sakar ma juna murmushi kafin sukayi sallama....

Yana tada motar sa ya soma tunanin ta wani hanya zaibi ya cimma su cikin sauk'i dukda abinda yake shirin yi shisshigi ne bana kad'an ba..

************

Sai faman huci AT yake jin Ashfaq ne ya fita da Maryama, wato bata jin maganar sa saida yace mata baya son tana shiga motar kowa idan ba shi ya umarta ba, tabbas zata sa yayi firing Ashfaq...

Ya d'ago a karo na biyu yana duban Hajiya kafin yace "Amma Hajiya ai na hana tana shiga motar kowa ko, meyasa kika bari Ashfaq ya kaita ba tareda sani na ba...?"

Jakar uba, tsegege Hajiya ke dubansa baki a hangame,

"Eaaah...! Sannu Malam Sallau Mai Hula uban Fad'ima, Kaine ma ka haife ni Attahiru dole ka gindaya min sharad'i, toh ba'abi dokar taka ba, kai dokan wa ka bi, kai ank'i abi dokar taka sai ka had'e mu gaba d'aya ka daka,. Kai wllhi ka fita a idanu na kaji na fad'a maka, toh waima meye nufinka na tak'ura ma yarinya inyi, kan wani bokon banza, kai da anyi magana sai kace karatu kake so tayi, toh alimantari d'in ma yaci uwashi (alimentary), bazatayi karatun ba, wanda tayi ya isheta, aurarta zanyi idan yaso ka had'iye zuciya... Kai uban waye ya tsare maka naka jin dad'in, ince kaima auren kayi, toh na gane take taken ka shine ka hanata manema koh, toh koh wllhi baka isa ba kayi kad'an ehe, kai shanyayye ma irinka.. Fice min a gida, kuma wllhi kayi wani abin ma yaron nan nida kaine.." ta k'arashe tana d'aga masa labule...

*Sameena Aleeyou Mrs*
💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*31*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

*Aysha Balarabe (My fastidious friend aka Maman Shema'u 🤣) and Aysha Malumfashi shafin yau naku ne ❤🤝🏻*

Gaba d'aya zuciyarsa a cunkushe take, tamau ya d'aure fuska babu alamun walwala a tareda shi, shi abin na Hajiya wata rana sosai yake damunsa, at least sai ta ringa ragar masa tunda shi ba k'aramin yaro bane amma idan ta soma tsefe sa bataji bata gani, kai shi da ace yanada k'anne yasan da ta rage wani abin...

"Zaka fice koko.?" Muryarta ya kuma kaste masa tunani.

Mik'ewa yayi jiki babu laka kafin ya furta "Kiyi hak'uri.."

"Ai ko Damo nan ya ganni ya barni wajen hak'uri tunda na k'yaleka ka auri wancan roba-robar, maza fice min a gida ehe.." ta k'arashe tana gyara labulen sosai.

D'an jim kawai yayi kafin ya soma tafiya uwa kazar da aka tsamo a ruwa.

************

"Malfar uba.!!" Shema'u ta furta a hankali ganin Maryama da kayan da AT yayita kwad'aita mata ta d'auka rananr da suka shiga store domin shi ya rakata sayyan kayan auren nata, bata d'auka ba ta d'auki wani kalan ashe ya zaga ya saya ma wannan shegiya bak'ar yarinyar mai ido uwa ta mujiya, zufa ya shiga keto mata take ta soma tunanin karfa hasashen Hisham ya zamo gaskiya, AT son wannan yarinyar yake, d'iyar cikinsa, yarinyar da ko hankalin kanta bata gama mallaka ba.. Taci gaba da huci tana tafarfasa sanda Maryama ta k'arasa wajen Maama Juu tana tambayar ta Sajida..

Shema'u dai zuciyarta tamkar ta fito waje ta tawarwatse haka take ji, lallai kuwa watan cin uwar yarinyar nan ya kama, tayi wata kafiran murmushi a hankali kafin ta furta "Maryama" _daga ke har uwar tasa mai d'aure maki gindi sai nayi maganin ku, sai na b'atar daku a kwanyar AT wllhi sai na shafe ki a babin rayuwar sa, babu wanda ya isa ya shiga tsakani na da Tahir, he's mine...._ a zuciya tayi wad'an nan maganganu kafin taci gaba da k'are ma Maryama kallo, tayi wata kafiran murmushi sanda tuna ta raba AT da matar sa uwar 'ya'yan sa kuma 'yaruwa a gareta balle wannan k'aramar yarinyar wanda tasan da salo da kaloli na makircin ta zata shafeta.. Ta fuzar da iska kurum ta shiga jona wayoyi suna spark a kwanyarta....

***********

Yama rasa ta wani hanya suka bi, gaba d'aya ya zama lost... Runtse idanunsa yayi sanda traffic lights ya nuna masa Koren wuta, cikin sauri ya karya kan motar ya soma bin hanyar da yake tunanin nan suka bi.

Buzu ya shafi red lips d'insa yana wani tamke fuska irin bai gama hucewan nan ba..

Ta d'an turo baki tace "Kayi hak'uri mana pls, nimafa ba son raina bane..."

Saida ya shafi sumarsa da suke a kwance luf kafin yace "Ya wuce amma ki sani ba'a rejecting kirana, gwanda Karma ki d'aga da kiyi rejecting, and na maki uziri is like baki tab'a soyayya da wani a baya ba . Na kula ni ne first love d'inki, ki gane tsan-tsan soyayyarki ce a cikin zuciyata banida bad intentions, amma kaman baki yarda dani ba, sannan irin haka a soyayya is norms ba wani abu bane tunda ni aurenki zanyi, amma idan baki sona fine I won't force myself on you..." ya k'arashe yana d'aga gira sama had'i da d'aga kafad'u da tab'e baki...

Idanun Sajida yayi rau-rau jin har an kawo peak d'in da Haris masoyinta ya soma irin wad'annan kalaman, gaskiya she don't wanna lose him, tana son shi sosai..

Satan kallonta yayi yaga kaman hawaye a udanunta, cikin sauri yayi parking a gefen hanya. Cikeda kulawa ya soma fad'in "Baby me ya faru kuma, why those tears, com'on fad'a min me yasaki kuka, na fad'i wani abinda bai maki ba koh... Oh I'm sorry I didn't mean it kinji, oya come here bana son ganin hawayen nan...." ya k'arashe maganar yana rungumota tsam cikin jikinsa...

Ita kuwa narkewa tayi tana mai ci gaba da kuka harda shesshek'a, ga sanyin k'amshin turaren sa ya sai yawo yake cikin hancinta don kuwa tsam ya matse ta cikin k'irjinsa..

Yana jin yanda k'irjinta yake bugawa da sauri-sauri..
Chapter 38 · 0% Book details