Sashe 64
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sajida tasa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata tana wani irin huci ta soma fad'in "Allah Ya Isa tsakanina dake Shema'u, wllhi wllhi wannan kad'an kika soma gani, kin kashe mutanen da nafi so a rayuwata kin kashe mahaifiyata kika jani a jiki don kin salwantar da rayuwa ta, kika nuna mana soyayyar k'arya don ki saye zuciyar mahaifin mu, toh ki sani Allah shine masanin al'amuran da muke k'ulla a fili da kuma a bayyane.... You know Shema'u I don't feel sorry for you, babban burina shine naga kinfi haka wulak'anta sannan ki k'are miserable days d'inki a gidan kurku..... You shameless witch...." ta k'arashe tana kuka sosai tana k'ok'arin kaima Shema'u duka saida Hajiya ta rik'ota.... Daidai lokacin aka turo Momma aka shigo da ita tana zaune saman wheelchair.
Kallonsu one by one Momma tayi hawaye na gangaro mata kafin ta k'arasa gaban Hajiya, tana kuka take bawa Hajiya hak'urin duk wasu abubuwan da suka shiga tsakanin su a baya, ciki harda taimaka ma Shema'u da auren Tahir da tayi, da ace tasan bak'in k'ullin dake cikin zuciyar Shema'u da bata kai ga had'asu ba....
Hajiya ta durk'uso ta kamo hannayen Momma kana tace "Kulu nima ki yafe min nasan nayi maki abubuwa da dama na yafe ki nima ki yafe ni.."
Momma ta share hawayenta kafin tace "Tabbas mu iyaye muke kula da rayuwar yaranmu, na zalunci yarana tun daga lokacin da nafi nuna fifiko akan guda, sannan kuskure d'aya tak nayi ta bibiye rayuwata hak'ik'a 'yanmma kuyi hattara domin kuskure d'aya zaki iya yi ta bibiyi rayuwarki har abada..." ta k'araso ga Sajida ta kamo hannayenta kana ta soma fad'in "Ku yafe ni Sajida ni na kawo maku annoba cikin gidanku, ku yafe ni jikokina, na sani I don't have much time left, amma inaso na kuma rungumar ku sannan na samu yafiryar ku ko ubangiji na zai sassauta min lamura na...." Saurin rungumarta Sajida tayi tana hawaye take fad'in "Momma ki daina fad'in haka, kema Victim ce, kema kin fad'a tarkon Aunty Shema'u.... Mu gode ma Allah da ya ganar damu komai...." Momma tayi murmushi had'i da hugging Sajida dukda k'arfin hali kawai take...
Koda suka fice daga d'akin Momma bata fice ba saida ta k'arasa wajen d'iyarta Shema'u, Shema'u ta ringa surfa mata ashar tana fad'in duk laifinta ne ita ta jawo, itace silan komai, nan Shema'u ta sanar da ita cewa ita ta kashe mijinta Alh Mukhtar sabida ta jima da sanin ba shine mahaifinta ba shiyasa suke wareta suke nuna sunfi son d'iyarsu Aysha sama da ita....
Momma ta soma gani bibbiyu lallai Shema'u ta wuce tunanin mutum cikin kuka take gungura kekenta ta k'arasa tana kai duka ma Shema'u dake faman dariya ta ko ina.... K'arfen abin drip Shema'u ta jawo ta shiga ruza wa Momma a tsakar ka duka zogin ciwo dake addabanta... K'arshe ta k'are ta hankad'e Momma ta fad'i akan zuciyarta lokaci guda ta Saki wani k'ara...
Gaba d'aya suka nufo d'akin nan suka ga Shema'u sai dariya take ga Momma rik'eda k'irji tana salati.. Shema'u kuwa sai dariya take uwa tab'ebb'iya k'arshe fiffincike bandage d'in da aka rufa mata da jikinta ta ringa yi tana had'awa harda naman jikinta tana ihu....." Dole aka kwasheta aka canza mata asibiti....
Momma kuwa mintoci kad'an ta k'ara tace ga garinku, rai yayi halinsa.... A gidan AT akai ma Momma komai taredasu Hajiya, gaba d'aya sunsha kuka barin su Sajida, haka su Maryama da Hajiya suka ringa lallashin Su suna basu baki....
*****
Hannun Mommy ya rik'e yana kuka tana kuka sanda ya sanar da ita duk yanda sukayi da Daddy... Haidar yaci gaba da fad'in "Mummy pls ki sanar dani asalina , wanene ni....?"
Mummy ta shafi gashin kansa tana mai ci gaba da kuka take fad'in "Gaskiya ne Haidar Juwariyya itace ta haifeka, ta kasance tana yimin aikatau a lokacin dtazo da kai kana jariri domin mahaifinka ya rasu tun kana ciki ma'ana tun ba'a haifeka ba, ni kuma tuntuni inada son yara saidai Allah bai bani haihuwa ba.... A dalilin haka ta damk'a mana kai kyauta ko bayan ranta, koda nazo na sami cikin Nabila na haifeta sai na damk'a mata rainon Nabila gaba d'aya har zuwa ranar da muka wayi gari wuta ya k'one su..."
Haidar ya share hawayen sa kafin yace "Mummy basu k'one ba, Daddy bai cimma burinsa akansu ba Allah Ya tseratar dasu kuma suna rayuwa a wani waje nasan watarana Allah zai had'a mu...."
Mummy ta gyad'a kai kafin tace "Haka ne Haidar, sai yanzu nasan dalilinka na bijire wa Mahaifinka, hak'ik'a mutane sun zama mushirikai sabida neman duniya, sun fifita duniyar su sama da lahiransu wacce lahira itace rayuwa ta har abada, Fu'ad ya zalunce ni, ya cutar damu.... Bana k'aunar na kuma ganin fuskar sa har abada...." ta k'arashe cikin tsananin kuka...
*******
Gida suka zo ita da Hajiya don d'iban kaya sabida Tahir da iyalansa suna tsananin buk'atar su, nan Maryama ta wuce sashen Maama Juu ta d'auko d'an akwatin tan nan na sirri... Hannunta dafe a wuyanta tana shafe sark'anta tana mai mata addu'a cikin zuciyarta ta shiga bud'e akwatin... 'yan kunnaynta ne yawanci tun tana Baby irin a yaye lafiya d'in nan, abun har saida yasanya Maryama yin murmushi... Har zata rufe kaman ance ta karkad'e nan wata wasik'a ta fad'o....
Gaban Maryama ya yanke sanda ta d'auki wasik'ar zata soma karantawa kenan ta jiyo sallaman Ashfaq da wata Mace wanda ya sanyata fad'uwan gaba...
Hajiya ta fito daga d'aki tana fad'in wa nake ji kaman Keenafas...
Haidar na murmushi ya k'arasa shigowa Mummy ta take masa baya.. Hajiya da Haidar na ma juna barkwanci Maryama kam da Mummy tuni sun makare a kallon juna...
Idanun Mummy suka sauk'a kan sark'an dake mak'ale wuyan Maryama, take ta soma recalling komai sanda tabawa Mama Juwaira wannan sark'an tace ta ajiye mata domin a ranar Nabila wuni tayi tana wasa da sark'an...
Mummy na hawaye ta k'arasa har gaban Maryama baki na rawa take nunata tana furta "NABILA!! " Ba Maryama da tayi turus ba tana kallon Mummy gaba d'aya su Hajiya ma tsareta da idanu sukayi....
Haidar ya k'araso yana duban Mummy da kyau kafin yace "Mummy itace Nabila koh, Maryama itace Nabila koh.... Kenan matar da na zata mahaifiyarta ce wacce nake gani a mafarki itace mahaifiyata koh.... Mummy mahaifiyata ta rasu, bazan ganta ba kenan..."
Rungume Maryama Mummy tayi tana fad'in "Nabila Nabila ta, Allah yayi zan kuma ganin ki, ina Mama Juwaira...."
Hawaye Maryama keyi tana bin matar da kallo tana girgiza kai, ta kuma saurin sunkuyawa ta d'au wasik'ar da take k'ok'arin karantawa wasik'ar da Maama Juu ta fayyace mata komai a ciki, asalinta da sunan mahaifanta da kuma ita d'in ko wacece da dalilin da ya sanyasu gujewa daga gida...
Kuka Maryama take shar-shar da hawaye sanda Ashfaq ya amshi wasik'ar yana karantawa da bud'edd'iyar murya.... Gaba d'aya parlour ya kaure da kuka.....
Al'ajabi ya cika Hajiya.... Nan kuma bayan hankula sun dawo jiki aka zauna aka soma fahimtar juna, Mummy da Haidar sosai sukaji mutuwar Maama Juu, Babu kaman Haidar da bai sami Chance d'in kasancewa da ita ba a matsayinta na mahifiyar sa.. Allah Ya k'addari hakan saidai su bita da addu'a...Allah sarki Maama Juu ta cika mai halin k'warai Allah ya kai haske makwancinta..
Mummy tamkar ta maida Maryama cikinta haka take ji, gaba d'aya suka d'unguma sukayi gidan AT... Mamaki da Al'ajabi ya cika su gaba d'aya, kodashike ba'a mamaki da ikon Allah lokaci guda ya warware komai..
Mummy gaba d'aya rasa bakin godiya tayima Hajiya da Ahmad Tahir... Babban abinda yafi mata dad'i shine auren Tahir da Nabilar ta, lallai sun cika mutane masu karamci...
Maryama dai bata wani sake da Mummy ba tana nan mak'ale da Hajiyarta, saida Hajiya ta tilasta mata ta tafi wajen mahaifiyarta su kwana tare suji d'umin juna kafin Maryama ta mik'e ta tafi wajen mahaifiyarta... Hira Mummy ta ringa janta dashi na labarin rayuwarta kafin daga bisani tace maza ta tashi ta tafi wajen mijinta yafi kowa buk'atan ta a hali yanzu tunda bashida lafiya...
Maryama ta d'an turo baki had'i da zaro idanu tace "Mummy fah zai iya kwan, nidai ki barni naji d'uminki..."
Mummy tayi murmushi ta shafi kumatunta kafin tace "Baby babu kalan d'umina wanda bakiji a jikin Hajiya ba, yanzu d'umin mijinki yafi d'umina mahimmanci a gareki kinji koh..."
Cikeda kunya Maryama ta sadda kanta k'asa.. Har k'ofa Mummy tayi mata rakiya had'ida saka mata albarka...
A stirs ta had'u da Sajida zata sauk'o k'asa... Gaban Maryama ya yanke ya fad'i don gani take Sajida ta fahimci d'akin mahaifinta zata tafi...
Murmushi Sajida ta sakar mata kafin ta iso yanda take, a kunnenta ta rad'a mata... "Aunty Sis kin k'yale min Daddy na shi kad'ai bayan kinsan bashida lafiya..."
Dariya Maryama tayi ta kai mata dukan wasa tace "Zaki sani ne..."
Dariya Sajida ma tayi kafin tace "Eh mana ai gaskiya na fad'i koh, ga wannan yayan naki Keenafas d'in Hajiya ina cikin bacci na ya dameni da waya wai sai na had'a masa shayi... Likitoci akwai kad'ifiri wai basu cin solid food da dare..."
Ganin Maryama na watso mata kallo yasata k'unshe baki tace "Oh I'm sorry ashe ke matar likita ne..." ta k'arashe tana wucewa da gudu...
Murmushi kawai Maryama tayi kafin tayi wucewarta d'akin masoyinta....
Yana tsaye gaban full length mirror yana k'ok'arin cire rigarsa da hannu guda sabida ciwon sa, kaman daga sama sai jiyo hannunta yayi tana taimaka masa... Annuri ya cika zuciyar sa, gently ta k'arasa cire masa rigar...
Juyowa yayi ya d'an kamo kunkuminta da hannu maras ciwon kafin yace "Allah Ya maki albarka Baby.."
Bata iya amsa sa ba sai sadda kai k'asa da tayi domin kuwa gaba d'aya nauyinsa take ji...
AT ya murmusa kafin yayi masu masauk'i saman chaise lounge, tana zaune saman laps d'insa ya d'ago fuskar sa yana dubanta kafin yace "Why the face Baby, ko baki so zuwa wajena bane, I thought da Hajiyarki zaki kwana har na cire rai...."
Turo baki ta kuma yi kafin tace dashi a shagwab'e "Ba Mummy bace tace sai na zo..."