Sashe 65
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
AT ya murmusa had'i da d'an jan hancinta kafin yace "Gaskiya Mummy ta kyauta min, ai Mummy ta fiku gaskiya keda Hajiya, ku kun faye son kanku yanzu nima kunga na sami mai sona tunda tana tausayi na..." Maryama ta kuma turo baki..
Rungumeta yayi cikin jikinsa had'i da lumshe idanu... Nan yaji hawayenta na sauk'a a kafad'ansa.... SSaurin d'agowa yayi yana tambayarta meke faruwa.. "Ko kina son ki tafi wajen Hajiya ne..."
Girgiza kai tayi kafin tace "Uncle na kasa aminta mahaifina mutumin banza ne, shin dama hakan ka iya kasancewa ga mutum, meyasa mahaifina why him... Rayuwa ta mana sauk'i, mun zama family d'in da muke mafarkin zama na samu Mahaifiyata, na auri mijin da nake so but.... I'm still hurting deep inside....."
AT da jikinsa yayi sanyi saurin rungumeta yayi kafin yace "Ki daina irin wannan tunanin Baby, Allah yakan jarabci bayinsa tako ina, babu laifinki ko na mahaifiyarki don mahaifinki ya kasance haka, kar ki manta Allah yana cire rayayye a cikin matacce sannan yana cire matacce a cikin rayayye wannan fad'insa ne, kasancewar mahaifinki haka doesn't mean you can't be accepted by other people, because we all are imperfect no one's perfect sannan babu wanda zai sami irin rayuwar da yake so perfectly dole ta wani wajen ka sami nak'asu.... Kar ki manta Annabi Nuhu alaihissalam Annabi ne kuma manzo sannan d'ansa da matar sa sun kasance 'yan wuta... Asiya matar fir'auna wanda yafi kowa kafirci a duniya ta kasance cikin mataye masu daraja kuma 'yan aljannah dukda cewa daga iyalan gidan Fir'auna take.. So ki daina damuwa Baby wannan shike tabbatar wa mu 'yan Adam ne bazamu sami komai yanda muke so ya kasance ba kinji koh..."
Murmushi tayi had'i da gyad'a masa kai kana ta kwanta cikin jikinsa a hankali ta furta "Ina sonka Uncle..." Ido a lumshe shima ya furta "Ina sonki nima Baby..."
"Keenafas ka k'yaleni naje nayi bacci tunda na kawo maka shayin pls..." ta k'arashe tana had'e hannayen ta waje guda..
Murmushi Haidar yayi kafin yace "Saifah kinmin labarin saurayinki Buzu kafin na k'yaleki..."
Harara ta galla masa kafin tace "Kaga ka daina tam, ni dai bana so...."
Haidar ya k'unshe dariyar sa kafin yace "Toh saurayin ki Keenafas fah...?"
Dariya itama tayi kafin tace "Kai gaskiya Hajiya ta iya saka suna sosai, kuma fah kayi kama da Kidnappers d'in...."
Dariya ya kumayi kafin yace "Gashi kuma zanyi keenafas d'inki ba...."
Kaman daga sama sai ganin Hajiya sukayi ta lek'o tana goga aswakinta kana tace "Kafin kayi keenafas d'inta ka tabbata ka biya sadaki ehe....."
Daga Haidar har Sajida dariya suka ringa yi harda sunkuyawa... Hajiya kuwa ko a jikinta ta fad'i ta koma d'aki abinta.....
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!
*A nan na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai taken SHAK'UWA CE, kurakuren da nayi cikinsa ina rok'on Allah Ya gafarta mani, fad'akawan dake cikinsa Allah Ya amfane mu dashi baki d'aya.*
*Dukkan yabo da godiya sun tabbata GA Ubangijin talikai wanda ya aramin rayuwa da lafiya har na kammala wannan rubutu nawa...*
*K'ungiyata ta KAINUWA na gode maku k'warai bisa goyon bayanku da jajircewan ku a gareni har wannan sak'o da nake son isawar ya kammala, Allah Ya saka maku da alkhairi ya k'ara had'e kanmu baki d'aya... Ameen!"*
*''Yar uwa aminiya k'awa a gareni RALIYA GARBA aka RALLY GARBA, banida bakin godiya a gareki saidai naci gaba da maki addu'an alkhairi.... Allah Ya rabamu da sharrin mutum ko aljan... Wannan littafi nawa mai taken SHAK'UWA CE kacaukam d'insa sadaukarwa ne a gareki My Sisi... Tabbas SHAK'UWA CE mai k'arfi abtsakanin mu, Allah Ya bar k'auna... Amen...!*
*Masoya na a duk yanda kuke a fad'in duniya nima ina sonku ina k'aunar ku... Nasan cewa SHAK'UWA CE mai tsanani a tsakanin ku da wannan labari zakuyi kewan shi kaman yanda shima zaiyi kewarku.... Alkhairin Allah Ya kai maku a duk yanda kuke...*
_*SAMEENA ALEEYOU aka QUEEN SAMY ke maku fata na alkhairi 🤝*_