← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 65

Sashe 37

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hisham yayi murmushi mai sauti kafin yace "Billahillazi kar kiyi gigin zuwa gidan Hajiya yanda take cikeda haushin auren ki da AT, duk barinki ki ina mai shawartanki kiyi wani makircin daban amma kar ki kwashi sawayenki zuwa gidan Hajiya, kin gannin nan namu batazo d'aya ba shiyasa ma kiga ban faye zuwa ba, idan kikaje kuma you'll regret..."

Shema'u sai faman huci take takaicin Hajiya ya cikata, kafiran murmushi tayi kafin tace "Nasan abinda zanyi, sai munyi waya..." Daga haka ta katse kiran.

D'aki ta dawo ta sami Ni'ima a kwance saman kujeran ta tak'ure waje guda har kaman baccin wahala na son d'aukanta...

Hannu tasa ta mintsileta, yarinyar ta tashi firgit zatayi ihu Shema'u ta toshe mata baki da hannun ta...

Zare idanu tayi tace mata "Quite" shiru Ni'ima tayi tana kallon Shema'u uwa taga dodo..

Shema'u ta sassauta rik'on data mata lokaci guda ta marairaice fuska ta rik'e hannayen Ni'ima kafin tace "Baby I'm sorry, I'm sorry kinji, I'm not a monster, spirit d'in Mummyn ku ne ya shige ni shiyasa na zama Monster, itace real monster, and idan kika fad'a ma Daddy abinda ya faru zata dawo ta kuma shiga jikina tasa na yanka ki da knife kema ki tafi yanda ta tafi ki dawo Monster kema, kina so ki dawo Monster..?"

A razane Ni'ima ta girgiza kai alamun a'a. Shema'u ta murmusa kafin ta gyad'a kai tace "that's my girl, oya let me call your Daddy, kiyi kuka sosai kice masa you want see him, kinji koh, idan bakiyi duk abinda na saka ki ba, spirit d'in Mummyn ku Monster zai shige jikina na yanka ku gaba d'aya harda Daddy dasu Jamal..." tsoro ya bayyana a idanun yarinyar..

***********

Yana shirin mik'ewa wayar Shema'u ke shigo masa, aiko yana d'agawa yaji kukan Ni'ima tana fad'in ya dawo gida, Shema'u daga can sai zare mata idanu take tana mintsilinta lokaci guda ta kashe murya ma AT tana fad'in "My AT pls kazo gida tak'i yin shiru and kaman tanada fever ma...."

Ai a sukwane ya mik'e yana fad'in "Fever!! Gani nan zuwa, pls Shema'u don't leave her side, just take care of her yanzu zan iso" daga haka katse wayar yayi yanai ma Hajiya sallama... Ta bisa da kallo kurum cikeda tausayi a fili ta furta "Ya Allah bana cutar da kowa da harshe na idanba shiga hurumita kayi ba, Ya Allah ka yaye ma Attahiru k'ullin dasu Kulu suka masa.." ta k'arashe zuciyarta cikeda tausayin d'an nata. ...

***********

Bata bar Ni'ima ta tafi wajen Maama Juu ba koda suka gama wayan da AT, saima kunna mata cartoon d'in _Moana_ da tayi a iPad d'in kafin ta mata umarni da kar ta fice, d'akin Sajida ta nufa yanda ta ganta tayi jigum dukda ga hayaniyar mutane 'yan biki a parlorn k'asa amma Sajida ta k'ule a d'aki tasan akwai wata a k'asa, tana son ji ko akwai improvement da aka samu tunda har yau bata samu tayi waya da Buzu ba tunda aka soma biki .
[8:09AM, 3/14/2018] ‪+234 803 315 3757‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*30*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

Zaune ta hangi Sajida tayi jigum ta k'ura ma window idanu da alama ta jima a hakan.

Maida k'ofar tayi ta tura a hankali kafin ta d'aura murmushi saman fuskarta ta k'arasa shigowa cikin d'akin, zama tayi gefen Sajida had'i da dafe kafad'un ta, sai sannan Sajida tasan Shema'u ta shigo.... Fuskar tausayi Shema'u ta saka lokaci guda ganin Sajida ta kasa furta mata komai sai rungumarta da tayi...

"My Sajee meke faruwa, pls sweetheart share it with me, kinsan bana son ganinki cikin damuwa, fad'a min meke damunki sweetheart..." ta k'arashe fuska uwa zata kurma ihu.

Sajida ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta soma fad'in "Aunty wllhi ina son shi, bansan abinda na mashi zai b'ata masa rai ba, he's not answering any of my calls, na masa text bai min replay ba, Aunty pls banaso na rasa shi wllhi kullum k'ara sonshi nake..."

Shema'u ta shiga had'e tunani tana waresu kafin ta kamo hannun Sajida tace "Sajee tell me, fad'a min me ya had'a ku...?"

D'ago idanu Sajida tayi kaman zatayi magana sai kuma ta fasa, don batama san me zata soma fad'a mata ba. Shema'u ta tsareta da idanu sai sak'e-sak'e take tana warwarewa... Ganin Sajida ta kasa fad'a mata komai yasata tunanin wani babban abin Buzu ya mata, kuma ga dukkan alamu Sajida bataji dad'in abin ba...

Murmushi ta sakar mata kafin tace "Sweetheart idan baki so ki sanar dani fine, na fahimce ki, sannan wannan shi ya nuna min kina son Haris sosai, karki damu relationship ya gaji hakan, ki kwantar da hankalin ki kinji babu wani abu, dole dama zaku samu sab'ani sannan ku fixing abunku da kanku kin fahimta, yanzu kar ki sake kiransa zakiga da kanshi zai nemeki, kamar yanda sukace if they love you they'll come back. Kar ki damu kinji sweetheart, trust me kiyi yanda nace da kanshi zai nemeki, don nasan babu namijin da ya kai ya wulak'anta min daughter ta sabida every man's type ne..."

Sajida ta murmusa kafin ta rik'e hannun Shema'u tace "Aunty wllhi bansan yaya zanyi ba without you, thanks for everything, Allah Ya baku farin ciki mai d'aurewa keda Daddy, ke kad'ai tol babu k'ari, our family is complete bamu buk'atan wata..."

Dad'i kaman ya kashe Shema'u, hugging Sajida ta kuma yi tana wani kashe murya take fad'in "Oh sweetheart Allah Ya amshi bakin ki..."

Tana ficewa daga d'akin nata d'akin ta wuce har lokacin Ni'ima na zaune tana kallo, Shema'u ta sakar mata murmushi kafin ta shige bathroom, layin Buzu ta shiga dialing, bugu uku ya d'aga murya a tamke..

Cikeda masifa tana huci ta soma fad'in "You such an imbecile, banga wani improvement ba saima tsoronka da ka haifar mata, fad'a min what really happened..."
Saurin katseta yayi yana fad'in "Hey.. hey just hold on, don't you dare call me an imbecile or whatever, you talk to your niece first, kinsan ban saba hark'a da k'anan yara irinta ba, hugging d'inta kawai nayi shikenan tayi fushi, ina kiranta har tana rejecting, babu macen da take min haka coz duk macen da kika ganni da ita nemata tayi, mace d'aya nake so and ita kad'aice zatayi yanda take so dani... Maryama, Maryama ce kawai zan d'auki duk abinda zata min, sannan idan kika tak'urani zan ajiye maki aikin ki..."

Shema'u ta shafi goshinta had'i da d'anyi k'ara kafin tace "Wllhi k'arya kake, wllhi sai ka lalalata ta idan kana so ka mallaki Maryama, remember Dr AT shine a matsayin mahaifinta and nice matar sa ni zan bada shaida akan ka, idan mun gama da Sajida ni nasan yanda zamuyi mu zama rid of her, daga nan kai kuma sai ka mallaki Maryama.... Amma idan kak'i bin umarni na...." tayi wata kafiran murmushi kafin tace "Wllhi kana ruwa, zaka tashi a tutan babu, bazaka tab'a samun Maryama ba, the love of your life, so ina mai shawartan ka mu k'arasa abinda muka fara... Tana sonka take advantage of that love, if not I'll take advantage of the situation and ruin you, so is up to you boy, kaci gaba da aiki da ni ka sami biyan buk'ata..." Daga haka bata jira cewar sa ba ta katse wayar tana wani irin huci takaici ya cikata, don by now ta zaci Sajida ta k'ware a iya romance, ita wllhi sam ta raina ma barikin Buzu, yanda yake huld'a da manyan mata ta zaci yafi haka iya bariki... Tsaki ta buga had'i da finciko k'ofa ta fito dai-dai lokacin da AT ya murd'a k'ofan d'akin ya shigo da sallama.

Abunka da maras gaskiya tuni ta razana da ganinsa, shi kuwa a tamanin yayi wajen Ni'ima yana tattab'a jikinta yana tambayarta meke damunta..

Rungumesa yarinyar tayi tana satan kallon Shema'u dake narka mata harara a sace tana mata alamu da tayi shiru..

Gefen AT ta zauna tana k'ok'arin shigewa jikinsa take fad'in "My AT wllhi fever d'in ya sauk'a kaga har kallo ma take.

AT ya murmusa yana rungume da Ni'ima kafin ya dubi Shema'u yace "Nasan you'll take care of her, idan kina tareda su banida haufin wani abu zai same su..." ya k'arashe maganar with a smile on his face.

Shema'u sai wani kwarkwasa da mad'e take, Ni'ima na son tafiya wajen Maama Juu AT yak'i sakinta don tsoronsa d'aya kar Shema'u ta kusanto sa, har addu'a yake cikin zuciyar sa...

**************

Bayan azahar aka soma gudanar da liyafar da Shema'u ta had'a. Tana d'aki tana shiryawa ta kira layin Buzu bugu biyu ya d'aga.

"Hello kanajina, ka cika aikin ka yanzu, take her out and treat her like a queen... Yauwa ka dai gane, no hankula sun kasu sabida hidima, just take advantage of the situation... Yauwa, don't fail me pls..." Daga haka katse wayar tayi tana wata kafiran murmushi...

**********

Shiryawa tayi tsaf cikin sabuwar rigar da Uncle ya kawo mata, tayi kyau har ta gaji, Hajiya ta dubeta ta tab'e baki ba tareda ta furta komai ba domin kuwa sam bataso Maryama taje bikin wannan watsesttiyar matar.

"Hajiya nayi kyau.?" ta tambaya tana kuma duban kanta a mirror.

"Yo bikin rahama zakije da zan ce kinyi kyau, ai koma kinyi kyau ni dai baki yimin ba tunda bikin sharri kika nufa, wannan aure sam banji akwai albarka a tattareda shi, shi dai Attahiru da Allah Ya riga ya jarabta da auren tsautsayi saidai na bisa da addu'a don bana masa baki ba, wannan bakin uwa ya kamasa saidai kuma yabi bola, tunda Kulu sun riga sun juya masa kwanya baya gane gabas baya gane yamma, addu'a dai shi zan tayi masa har Allah Ya warware wannan bak'in asiri da suka masa...."

Tunda ta fara magana Maryama tayi kicin-kicin da fuska, tasan batason auren Uncle da Aunty Shema'u amma sam bataso taga Hajiya na fushi da Uncle tunda ko bata tofa ba fushinta ka iya tasiri a rayuwar sa...
Chapter 37 · 0% Book details