← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 65

Sashe 10

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ran Shema'u wani irin haske da dad'i yayi mata, tabbas amfani da Sajida sam bazai mata wahala ba, don ta lura yarinyar asalin d'iyar fari ce, akwai wauwauta sosai akanta. Saida ta d'anyi gyaran murya kafin ta soma fad'in "Haba Daughter kaman bakije school ba, wake yin haka yanzu, wake trusting wata k'awa a wannan zamani da muke ciki, ke bakisan duniyar nan baki da aminiya sai mahaifiyar ki ba ko, har yaushe zaki yarda da k'awa ki barta ta sami kusanci da saurayin da kike so kike mafarkin kasancewa tare dashi..? Toh bari kiji na fad'a miki, ki bud'e kunnuwar ki da kyau kiji ni, the moment kika bawa k'awa dama har SHAK'UWA ta shiga tsakanin su da saurayin da kike so before you know it shak'uwar ce zata rikid'a ta koma soyayya,. Ke bakiga irin kallon da yake ma Maryama ba, sannan itama bakiga yanda take gwale masa baki tana murmushi ba, only lovers can do that. Ki kula da kyau kiyi nazarin abinda na fad'a maki, sannan da ace tana sonki dashi, da tuni ta soma yin wata hanya koda dabara ne kun soma soyayya koda a b'oye ne, da zaran lokaci yayi kinga yasan yanada ke kema kinada shi, saidai kawai a gabatar da iyaye.."

Sajida ta d'an dubeta kafin tace "But Aunty bana son na zama me b'oye rayuwar da nake ciki wa iyaye na, sabida Momy da Maama Juu kullum gargad'in da suke min kenan kar na zama mai yin wani abu maras kyau bayan idanun su..."

Parking a gefen titi Shema'u tayi kafin ta karkato sosai tana mai duban Sajida, fuskarta fal damuwa kafin ta soma fad'in "Sweetheart try to understand me, I'm not saying you should be hiding things, shiyasa ma nace maki ki zama free ki zama open dani, yau da ace Momyn ki tana nan, the same abinda zata fad'a maki kenan, besides sonshi kawai kike da manufa mai kyau ba da niyyan lalacewa ba right.?"

Sajida ta gyad'a kai tana duban Shema'u. Shema'u ta kuma shafa fuskarta kafin taci gaba da fad'in " Ehen, ni na sani, My Daughter is a good girl, bazaki tab'a yin wani abu maras kyau ba tunda kinsan makomar wanda ya lalata rayuwar sa, sannan hanaki yin abinda kike so da Daddyn ki zaiyi shine zai jefa ki cikin rayuwa maras inganci, sannan hanaki yin abinda kike so zaisa ko karatun ma da yake so kiyi kizo bakiyi ba, kinga kuwa ai ba'aci riba ba ..... ki saurare ni da kyau ki gane me nake nufi, shi Daddyn ku namiji ne, ba lallai ya fahimci irin hakan ba, shiyasa ake cewa ciwon d'iya Mace ta d'iya Mace ne, shiyasa Uwa take zama babbar aminyar D'iya da zaran ta doshi irin shekarun ki, ni na tabbata if Aysha was still here hakan zata fad'a maki.. Sajee I love you and I want your happiness, bana son wani abu da zai ruining maki rayuwa, daga baya na tabbata Daddyn ki zai fahimci hakan, sabida tak'ura ma yaro bashida wani alfanu especially a Teenager like you..... Kin fahimce ni Sweery.?" Ta k'arashe cikin tsantsan sadda murya tamkar mai shirin yin kuka.

Sajida ta gyad'a kai kafin tace "Wllhi haka ne Aunty, tak'urawar bashida wani alfanu. Toh yanzu yaya zanyi nayi grabbing attention nasa Aunty.?"

Shema'u ta d'anyi murmushi kafin tace "Thanks for understanding me, kar ki damu duk lokacin da kike sonyin waya dashi zan rik'a baki wayata kuyi waya har lokacin da Daddyn ki zai sai maki naki tunda saura k'alilan ne ki kammala Jarabawar k'arasa sakandaren. Sannan yanzu ki sami ita Maryama da zancen cewa tasan yanda za'ayi ta had'aki da Buzu, duk yanda kukayi sai ki sanar dani. Kinga idan kinyi haka baki zama mai b'oye Al'amranki ba tunda kin sanar dani, sannan da Aysha ta tana nan da ma ita zaki fad'i, tunda bata nan sai ki sanar dani, bazan daina fad'a maki bakida masoya kaman dangin mahaifiyarki ba kinji Sweetheart.... Hakan yayi maki.?"

Da sauri Sajida ta shiga gyad'a kai tana fad'in "Aunty wllhi shiyasa nake jin ina k'ara sonki sabida kina fahimta ta a koda yaushe. Thank you Aunty Shemah, please kar ki bar rayuwar mu sabida bansan yaya zamuyi ba.."

Rungumeta Shema'u tayi tana mai fad'in "Ohh My Sajee insha Allah bazan tab'a barinku ba.. Oya zo ki tuk'a mu.."

Sajida ta ware idanu tana dariya kafin tace "Aunty ai ban iya driving ba, da idan nace ma Momy take koya min sai tace sai na kai 18,."

Shema'u ta murmusa tana mai goge k'wallan makirci kafin tace "Allah sarki My Aysha my Baby Sis, I never thought zan tab'a rabuwa da ita, tunda tayi aure na kasa Aure sabida SHAK'UWAR dake tsakanin mu, yau gashi mutuwa tai mana me kankat.... " Nan fah Shema'u tayi bursting cikin tsananin kuka.

Sajida ma hawaye ne suka soma kwararo mata kafin tayi saurin rungume Shema'u tana fad'in "Aunty ki daina kuka pls, idan kina kuka ni kuma me zan yi, don Allah ki daina kuka... " Ta k'arashe itama cikin kuka.

Da sauri Shema'u ta rungumeta tana lallashin ta, kallon glass d'in marfin mota kurum take tana wata kafiran murmushi mai cikeda ma'anoni..... Saida ta tabbata Sajida tayi shiru kafin ta soma cheering nata da zantuka masu dad'i tana sanar da ita zata soma koya mata driving kwanan nan tunda ta kusan harin 18.

***************

"Wai ni meye ke damunki kika saka abinci gaba kika kasa ci ne inyi.?" Hajiya ta tambaya Aswakin ta na mak'ale a bakin ta, ( Kar kuji inata cewa Aswakin Hajiya na mak'ale a bakinta, sosai ta rik'i wannan Sunnah na goga Aswaki shiyasa ma dukda tana cin goro kullum hak'waranta k'al suke babu dottin goro)

Kaman bazata amsa Hajiya ba sai kuma ta mik'e k'afafunta tana kuma shinshina hammatar ta kafin tace "Hajiya wai don Allah ina wari.?" Tayi tambayar fuskarta cike da damuwa.

Mik'ewa Haiya tayi ta k'araso dab da Maryama tana k'ok'arin kai hanci jikinta... Maryama ta kauce tana fad'in "Haba Hajiya bafa cewa nayi ki manna hancin ki a jiki na ba."

"Auho inji cewa kikayi naji maki ko kina wari, nidai banji warin bane sai k'amshi shiyasa kika ga ina kawo hanci na, kuma banda iyayi da felek'e duk zamana dake, yo ai idan kina warin kinsan zan fad'i tunda kinsanni banida b'oyo."

"Toh fah, yau kuma ta sami Maudu'i" ta fad'i a hankali kafin taci gaba da fad'in "Nifa kurum tambayar ki nayi Hajiya..."

"Fad'a min uban waye yace kina wari.?" Hajiya ta fad'i tana gyaran d'aurin kallabin ta.

Maryama ta kalleta kafin tace "A bar zancen tunda kince banayi."

"Auw bazaki fad'i min ba ko, naji ko a gidan uban sa ake k'eran man k'anshi da yafi naki tsada da kyau, yo ko agwagwa nan ya ganki ya barki wajen wanka, dukda wankan bak'i asaran ruwa ne, amma ke naki ba asaran bane, ki fad'i min wa yace kina wari...?" Cike da masifa take maganar.

Kaman bazata fad'a ba, tasan ma idan bata fad'a ba wllhi maganar bazai tab'a mutuwa wajen Hajiya ba. Baki a ture tace "Aunty Shema'un nan bane tace wai bana shuwa da body spray, kuma wllhi kullum sai na saka, Hajiya ai ke shaida ce."

Sakare Hajiya tayi tana dubanta kafin tace "Au dama wancan mai suffan aljanai da mayun ne tace kina wari, Meye kuma Shuwa d'in ince man hammatan nane,... Ki sha kurumin ki Allah kai mu gobe suzo d'aukar ki tsaf zan rama maki, Karma ki b'ata ranki."

"Hajiya don Allah kar kice mata komai, dama dai kawai ina son sanin ko da gasken warin nake shiyasa na tambaye ki... "

Ko tankata Hajiya batayi ba ta nufi uwar d'aki tana tunanin kalan rashin mutuncin da zatayi ma Shema'u tunda ta tab'a mata Maryaman ta.

*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:54PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊

*SHAK'UWA CE*

馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊

*09*

*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*

_馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_

Misalin k'arfe takwas da wasu 'yan dak'ik'ai su Sajida suka iso gidan Hajiya d'aukan Maryama.

Shema'u sai kareraya ake mayafi rufe saman kanta sai ka rantse wata mutuniyar aziki ce. Sajida ce akan gaba sai faman rangad'a kira ma Hajiya take.

Hajiya na Kitchen tana taya Atine karin kumallo ta kafe Shema'u da idanu tana karantar ta, murmushi tayi a hankali kafin ta wanke hannunta ta fito daga Kitchen d'in.

"Hajiyar mu kinaji inata rattaba maki kira kikak'i amsawa koh." Sajida ta fad'i baki a ture daidai lokacin da Maryama ta fito tana saka hijabin ta.

Hajiya ta kalli Sajida ta watsar don daga ita har Shema'un haushi suka bata. Saida ta isa saman farin kujera dake barandar ta zauna kafin tace "Yo wannan kira da kike min sekace makahon da ya rasa d'an jagora."

Dariya Sajida tayi kafin suka soma gaisawa don wannan dama halin Hajiya ne tsaf ta saba da hakan... Kaman daga sama sai jiyo muryar Shema'u sukayi tana gaida Hajiya daga nan yanda take a tsaye.

Musamman Hajiya ta kaikaito tana duban Shema'u kafin tace "Lafiya, Almiski sarkin k'amshi.."

Ganin Hajiya zata Saki layi yasa Maryama saurin d'aukar jakkan ta kafin tace "Aunty Shema'u ina kwana."

Shema'u ta amsa da sakin fuska, cikin sauri Maryama ta soma fad'in "Hajiya mun tafi kar muyi latti.."

Hajiya bata sami zarafin amsa Maryama ba sai k'are ma Shema'u kallo da take, tun daga sama har k'asa wanda hakan yasa Shema'u shan jinin jikinta sosai ta tsargu da wannan kallo da Hajiya ke mata..... Jiyo muryar Hajiya sukayi tana fad'in "Yo ashema warin man Bilica (Bleaching) kike." Tayi maganar baki a tab'e..

Sajida sam bata gane ina Hajiya ta dosa ba hankalinta yafi karkata kan Solution d'in wani equation da Maryama ke nuna mata, Maryama kuwa tuni ta d'ago Hajiya, kai wato dai Hajiya bata barin kota kwana. Sai faman k'yafta idanu take ma Hajiya sam tak'i kallonta balle tayi shiru.
Chapter 10 · 0% Book details