Sashe 48
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikin Hajiya gaba d'aya yayi sanyi ganin yanda Ashfaq ya susuce gaba d'aya yana fad'in irin soyayyar da yake ma Maryama.
Tun Hajiya tana d'aukan abin nasa kaman wasa hardai ta soma jin tausayin sa sosai. Allah Ya had'a jininta da Keenafas tana jinsa tamkar d'an data haifa a cikinta, koda Attahiru zaik'i auren Maryama da Ashfaq muddin Maryama ta amince da soyayyar da Ashfaq ke mata toh fah sai yanda k'arfinta ya k'are...
Ashfaq ya kuma marairaice fuska yace "Hajiya wllhi da gaske nake son Maryama, Hajiya mahaifyata ta damu nayi aure sannan ni Maryama kawai nake so wacce Daddy na yake so na aura sam batada kamun kai, Hajiya ki taimaka min don Allah....."
Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya Hajiya tayi kafin ta d'ago ta dubesa.
*Sameena Aleeyou Mrs*
[9:28PM, 4/5/2018] +234 806 652 0501: 💘💘💘💘💘💘💘💘
*SHAK'UWA CE*
💘💘💘💘💘💘💘💘
*39*
*©Sameena Aleeyou...✍🏼*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
"Ni sam bazan k'i aurenka da Maryama ba mai sunan larabawa, kasan sunan naka wahalan fad'i yake bani nafi ganewa na kiraka da Keenafas..."
D'an murmusawa Ashfaq yayi domin sosai Hajiya ke burgesa.
Hajiya taci gaba da fad'in "Ni hakanma da sai yafi min dad'i, amma muddin d'iyata bata amunce ba toh fah gaskiya babu abunda zan iya akai domin amincewarta shine nawa..."
Ashfaq ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin yace "Shikenan Hajiya kiyita mata addu'an alkhairi, Allah Ya zab'ar mata da abinda yafi alkhairi, iyayena suna k'asar Saudi mahaifiyata ta tafi jinya muddin suka dawo banyi aure ba mahaifina zai Aura min waccan yarinyar da nake fad'a maki....." Da sauri Hajiya ta katse sa da fad'in "Allah Ya tsareka da auro irin matar Attahiru, shidai da Allah Ya jarabta da auren Roba-roba bana fatan wannan wak'i'a ta kuma sauk'a kan wani nawa, insha Allahu sam bazaka auri fentettiya ba....."
Allah shi maka albarka ya zab'ar maka abinda yafi alkhairi...."
Ashfaq ya amsa da ameen Hajiyar mu...
Tana k'uryar d'aki tana sauraren conversation d'in nasu, tausayin Ashfaq ya cika zuciyarta, lokaci guda tana tuno yanda suka rabu da Sajida, this the only way for her, ta haka ne kurum Sajida zata aminta cewa ita d'in mai k'aunarta ne, sann Ashfaq ya cancanci ya mallaketa koda babu soyayyar sa a zuciyarta, sannan haka ne kawai zaisa ta daina yaudaran kanta da rud'in kanta wajen tunanin Uncle. Mik'ewa tayi ta zura hijab d'inta k'irjinta na dukan tara-tara ta nufo parlor...
Daga Hajiya har Ashfaq kallo suka bita dashi..... Ashfaq ya d'an mik'e yana fad'in "Hajiyar mu ni zan wuce...."
Hajiya ta amsa masa kana sukayi sallama, ya kuma kallon Maryama kafin ya nufi k'ofa....
Har ya d'aga labule ya jiyo muryarta tana kiran sunansa.
"Ya Ashfaq"
Juyowa yayi yana dubanta ba tareda ya iya furta koda kalma ba.
Cikin sanyin muryarta ta soma fad'in "Na amince ka zama miji na....."
Baki sake Ashfaq ke dubanta, maganar tamkar ba daga bakinta ya fito ba...
Hajiya kuwa kaman talabijin haka suka zame mata wajen kallo, ta dubi wannan ta dubi wancan. Fari'anta ya kasa gushewa, farin cikinta ya bayyana sosai... K'arasowa tayi ta rungume Maryama tana fad'in "D'iyar albarka Allah dai ya saka ki a aljannah, ni na sani bazaki watsa min k'asa a idanu na ba..."
Ashfaq dai samun kansa yayi da raahin yarda da abinda Maryama tace, gaba d'aya yama kasa furta komai.... Bai bar gidan ba saida ya sami yin magana da Maryama.
Sosai abin ya dami Ashfaq yanda Maryama ta sauya lokaci guda tamkar ba ita ba, abun nata akwai ayan tambaya amma sam baiso yayi wani matsalan rashin yarda ya shiga tsakanin su.
Bayan ya tafi suka k'ule a d'aki itada Hajiyarta, Hajiya na tambayarta ta tabbata tana son Keenafas.?
Maryama ta gyad'a kai kana tace "Hajiya inaso kowa ya kasance cikin farin ciki, na tabbata idan Allah Ya yarda aurena da Ya Ashfaq shi zai haifar da farin ciki ma kowa, sannan kin manta tun ina k'arama na sha fad'a maki cewa duk abinda kike so nima shi nake so, tunda kina sona da Keenafas d'inki nima ina sonsa, sabida nasan bazaki tab'a zab'a min abinda zai cutar dani ba, Ummi ta Allah Ya gafarta mata, haihuwa ta kawai tayi amma rainona gaba d'aya kece kikayi, banida tamkar ki bayan Ummi a dinuya..."
Hajiya dai kallonta kawai take tana murmushi k'walla na neman ciko idanunta, gaba d'aya ta kasa fad'in komai sai rungumar Maryama da tayi su duka suna k'ok'arin zuban hawaye.
Hajiya ta rik'e hannayen Maryama kana tace "D'iyata kenan kin amince bazaki ci gaba da karatu ba kaman yanda kikeda burin hakan, sai kinyi auren ki ci gaba kenan...?"
Maryama ta murmusa tasa hannu ta goge hawayen da ya gangaro ma Hajiya kana tace "Hajiyata, duk abinda kike so nima shi nake so, nasan kina so kiga aurena tun da sauran k'arfinki, ina so na faranta maki shine samun albarka na..."
Gaba d'aya jikin Hajiya ya kuma yin sanyi tabbas ranar da aka ce Maryama zata bar gidan zata sha kuka, domin kuwa tsan-tsan SHAK'UWA CE a tsakanin su..
AT dake daskare bakin k'ofa ya gama sauraren su, kasa motsa koda d'an yatsan k'afarsa yayi, shin da gaske abinda yake jiyowa gaskiya ne, Maryam d'insa bata bari ya zab'a mata miji ba kaman yanda yake da buri,.. Shin ta yaya zai soma aurar da Maryam yanzu, gani yake she's too young for that, aside from that he's afraid ko wani irin miji take so sai yayi k'wakk'waran bincike akansa sabida Maryama marainiya ce amana ce a hannunsa... Kasa shiga parlorn yayi sai komawa da baya da yayi.....
Yana tafe cikin motarsa yana ci gaba da tunanin, dole ya nutsu yasan ma waye zai damk'a wannan amana da Allah Ya bar masa. Tabbas namiji da macce ba d'aya bane, tunanin mata ya banbanta dana maza su idan suna son mutum shikenan, k'wakk'waran bincike akansa bazai zame masu abin damuwa ba, bacin haka ta yaya Hajiya zata aminta da Ashfaq kai tsaye ba'ayi k'wakk'waran bincike ba, dukda shi Ashfaq d'in baida matsala ga dukkan alamu amma ya kamata ayi bincike akansa kafin a soma maganar aure..... Gaba d'aya tunanin da ya kusan kwana yanayi kenan.
************
Yau tunda Mummy ta d'auki wayar Haidar ta gane na cikin farin ciki nan ya labarta komai duk abinda ya faru. Mummy ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "Haidar anya bakayi kuskure ba, ina ka tab'a jin anyi wannan irin aure da b'oye kai, aure fah abune da yake buk'atan gaskiya a komai, ka bayyana asalinka nasan they'll accept you for who you are. Amma b'oye kai bashida wani alfanu.."
Ashfaq ya d'anyi jim kafin yace "Com'on Mummy na fad'a maki dalilina, ke kinfi kowa sanin idan Daddy yasan zanyi aure wllhi bazai bari ba, sannan ni kuma rantsuwa nayi kwabon sa bazan kuma ci ba, we're just related by blood nidashi bacin haka bana fata wani abin ya kuma had'ani dashi..." ya k'arashe kaman zaiyi kuka...
Cikin d'an fad'a ta soma fad'in "Bakada hankali ko Haidar, wacce irin magana kakeyi, idan kak'i dukiyarsa sabida shi politician ne sabida kana tunanin dukiyarsa tana gauraye da haramun ne da kuma hakkin jama'a ka tabbata da hakan, ka tabbata Daddynka ba guminsa yake ci ba... Haidar ka rage wannan zuciyar taka fah kullum ina maka fad'a.
Hak'uri ya soma bata don baiso plans d'insa su wargaje kafin yacigaba da fad'in "Mummy pls don't say no, kinga zan had'aku da Maryama da Hajiya a waya sai ku gaisa, karfa ki mance ki kirani da Haidar, my name's Ashfaq to them, daga baya gyaran da nake son yi idan ya tabbata kowa sai yasan ko ni waye, .. And maganan biki kuma banso ki saka family ciki, Aunty Deena k'awarki kawai ta isa tunda nasan aminiyar ki ce, and na gama magana da Baffah Yawale zai tsaya akan komai pls Mummy kar ki bari ku baro Saudiya sai anyi auren nan kinji...."
Gaba d'aya dai Mummy kam gani take anya kan Haidar bai kwance ba, ita ina ta tab'a jin irin wannan aure kai ko a wasan kwaikwayo, yama maida auren wasa kenan... Gwara ta lallab'asa idan hakan yake so tunda ya tabbatar mata idan dai yayi auren zai dawo gare su...
_Maryama and Mummy I'm doing this for the both of you, nasan mafarkina bazai zama shirita kawai ba, there must be something behind it...._ ya fad'i haka cikin zuciyar sa.
**************
Sanda AT ya tari Hajiya da zancen tass ta salle sa...
"Inyi, saika hana yarinya yin aure, ka fice a idona Attahiru, da yardan Allah sai naga d'iyoyin Maryama kafin na bar duniya, banda felek'e kasa ido akan taka d'iyar mana, Maryama d'iyata ce, kai idanma baka bada auren nata ba ni nan zan bada idan yaso ka had'iyi zuciya....."
Gaba d'aya bai gane me take fad'i illa zuciyarsa dake masa zafi, sam Hajiya bata tsayawa ta fahimcesa sai ta soma fad'a shi kuwa sam baison abinda zaisa ranta yake b'aci, hak'uri kurum ya bata kafin ya mik'e ya fice yana neman layin Ashfaq, sanar dashi yayi yana nemansa ya same sa a gidan sa ... Cikeda ladabi Ashfaq ya amsa masa...
Ta window d'in d'aki Maryama ke hangosa gaba d'aya sai taji babu dad'i, ko kad'an bata son yanda Hajiya kema Uncle fad'a, tana jin Hajiya ta shigo tana ci gaba da sababi tayi kwanciyarta tamkar mai bacci...
*************
Saman fararen kujerun roba dake farfajiyan gidan suka zauna, Shema'u na mak'ale daga window tana hangosu....
Tun daga ganin yanayin AT Ashfaq ya sha jinin jikinsa, tambayoyi ya ringa masa uwa d'an jarida fuska babu walwala, haka Ashfaq ya ringa amsa masa tambayoyin nasa ya k'arada Wan mahaifinsa zaizo shi daga Katsina cikin satin nan..
AT ya jinjina kai kafin yace "Shikenan dukda zaizo shi zan kuma bincikawa kaji koh..."
Ashfaq ya jinjina kai alamun amincewa cikeda ladabi.
AT ya dubesa kafin yace "Kana iya tafiya.." Godiya Ashfaq yayi ya mik'e cikeda rusunawa... Har ya soma tafiya Tahir ya kira sunansa.
Dawowa yayi ya zauna mazaunin sa.