Sashe 32
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idanun Momma sukayi rau-rau, kai Shema'u bala'i ce, harga Allah ita batayi wannan bin mazan ba gashi Allah Ya jarabce ta da samun 'ya haka, Kuskure d'aya tayi tak a rayuwarta, ji take kaman a fasa wannan aure amma babu yanda ta iya, jikokin ta zasu tsaneta...... Bata gama tunanin da take ba ta jiyo muryar Shema'u tana ci gaba da fad'in "Momma duk lalacewan naka naka ne, nasan tunanin ki bai wuce kar nabawa jikokin ki wannan tarbiyar ba, kar ki damu wllhi bazan tab'a abu makamancin haka ba, ina sonsu tamkar yanda nake son 'yaruwata mahaifiyar su, hasalima zuwa wajen Alh Aminu da zanyi sabida su zanyi, and I promise you wannan shine na k'arshe bazan kuma pls Momma kifahimce ni, nasan kina sona kina son su Sajida pls kar kiyi abinda zai zame mana tarin danasani dagani har ke..." ta k'arashe tamkar zata runtuma ihu idanunta sur k'walla.
Momma dake zaune kurum k'walla sun ciko idanunta, a hankali tasa bayan hannunta ta goge hawayen bata iya furta komai ba sai sanyi da jikinta yayi tamkar an tsoma a freezer....
Shema'u tana ganin haka ta mik'e tana wata kafiran murmushi ciki-ciki kafin ta shafi fuskar Momma tace "Anfani uwa kenan kullum ta tsaya ma family d'inta, ta zama very responsible.." daga haka mik'ewa tayi ta bud'e wardrobe ta d'auko hijabi har k'asa sannan ta d'au black Vail tayi nik'ab dashi.... Har ta kai k'ofa Momma ta k'araso gabanta ta rik'e hannayen ta tace "Goggonayen Attahiru zasu tafi dake da zaran an gama d'aurin aure don basu so ayi dare..."
Shema'u ta murmusa kafin tace "Kar ki damu Momma komai zai tafi yanda na tsara, ki dai san yanda zakiyi ki kare Amarya just in case ana nemanta..." Daga haka ficewa tayi cikin sauri ba tareda kowa ya ganeta ba...
Komawa Momma tayi ta zauna saman gado hawaye taji suna bin k'uncinta, ta sani ita d'in mai laifi ne ta sani ita d'in mai yawan son nata ne tak'i na wani, ta sani ita d'in mai son abun duniya ne amma tana tsoron kar hakkin Tahir ya kamasu, anya ta kyauta ma d'iyarta Aysha idan ta bar Shema'u ta zauna akan iyalanta.... Wata zuciya tace "Bakida zab'i muddin kika hana wannan aure toh har abinda kika jima kina b'oye ma Shema'u zai iya bayyana, sannan jikokin ki zasu tsane ki, ita kanta Shema'u zata tsaneki, Hajiya Fad'ime zata maki dariya, gashi babu Mukhtar babu Aysha, wad'annan su kad'aine family d'inki a yanzu, yin shirun ki shine maki mafita, iyakaci kibi Shema'u da addu'an shiriya.... Kifa kanta a wajen tayi hawaye suna sauk'o mata....
***************
*Kano*
Gidan a d'an kwai mutane wanda yawanci 'mdangin Hajiya ne da na mahaifin AT wato mutanen Rano 'yan taran Amarya.
Tana kwance saman gadonta suna chatting da wayar da Shema'u ta bata, nan yake sanar da ita ya d'an fita shan iska sabida zafi, Sajida sai murmushi take tana jinta a uwa wata duniya, nan ya tambayeta abinda take itama, kai tsaye ta sanar dashi tana d'aki tana kwance chatting with him, ya turo mata bugun zuciya wato Heart, nan yace ta turo masa pic d'inta a yanda take kar tayi makeup kar tayi komai..... Alamun rufe idanu ta tura masa kana tace tana jin kunyar sa...
Ya tura mata sad face kafin yace shi bari ya tura mata nasa...Hotonsa ya turo mata yasha kyau a bakin pool , babu riga a jikinsa sai wando 3quater gashin nan nasa sun kwanta luf-luf, babu macen da zata gansa a haka bai burgeta ba...
Sajida ta tsinci kanta da fad'uwan gaba, saida taji wani yarrr a jikinta ganinsa a haka da tayi... Kiran da taji Maama Juu na k'walla mata ya katse masu hirar tasu, nan ta d'aga k'asar pillown ta ta tura wayar ciki...
Gyare-gyaren d'akin Babanta Maama Juu ta sakata tunda ita ba shiga zatayi ba, Sajida dai gaba d'aya hoton Buzu ya kasa b'ace mata a k'wayan idanunta, kyaun halittan sa na fizganta, har alla-alla take ta gama gyaran su ci gaba da hirar su...
Tana gamawa ta dawo ga wayarta, zamanta a d'aki har ya d'an dami Maama Juu tunda tasan Sajida da son shiga mutane musamman yanda 'yanuwan su yau suka d'an cika gidan, wata zuciya tace "K'ila tunowa da mahaifiyar ta tayi shiyasa ta k'ule a d'aki, don haka Maama Juu bata kuma bin ta kanta ba...
Daga chatting k'iranta yayi ya sanar da ita gashi a layinsu tunda tak'i nuna masa hoton ta yazo ya ganta da idanunsa, sabida he's dying to see her pretty face... Dad'i kaman ya kasheta, mik'ewa tayi ta soma shiryawa, harda wani d'an makeup tayi akasu fesa turare....
************
*Taraba, Jalingo*
Toilet ta shige ta kintsa kanta bayan sun k'arashe bidirinsu da Alh Aminu, tana tsaye k'ofar toilet d'in tana jan zip d'in rigarta take jiyo muryar sa yana waya.
"Allah Ya taimaki his excellency, yayi wata murmushi cikeda rusunawa kafin yace "Wasu kala kake buk'atan 'yanmatan , farare, bak'ak'e ko wankan tarwad'a.... Ya gyad'a kai kafin yaci gaba da fad'in "Toh an gama rankashi dad'e, 'yan Sha biyar zuwa shatakwas kenan, yauwa an gama.. Allah Ya taimake ka your excellency, yauwa za'ayi duk yanda za'ayi su isa Abuja a gobe, daga haka yayi hanging...
Shema'u ta k'araso tana wata kafiran dariya kafin tace "Kace ba'a nan kawai ka tsaya ba my Alh, toh shi kuma waye ka gama waya dashi..."
Alhaji yayi dariya kafin yace "Ai yau ko me kika tambaye ni kai tsaye zan baki amsa domin kin jiyar dani dad'in da baki tab'a jiyar dani a baya ba... Wannan manyan mu kike ji na Abuja, bokayen su suna sakasu lalata da k'anan yara a ko wace wayewan gari sabida cimma burinsu, ba mata zalla ba wani jik'on harda yara maza..." ya k'arashe yana k'ok'arin kai mata wani sabon capka...
Dariya ta fashe dashi a zuciyarta ba komai ta tuna ba sai yanda za'ayi ta mik'a Sajida... Sauri-sauri ta tarkasa ya nata ya nata tayi wucewar ta don idan ta biye na Alh Aminu sai ya kusan had'iyeta a yau sabida naci da jaraban sa...D'an gyaran da akayi ma ango ya kwashe...
Tana isowa ta samu 'yan d'aurin aure suna dawowa alamun an d'aura, daga cikin napep d'in da take tana hango AT yanda yaketa gaisawa da jama'a yayi kyau cikin faran shadda k'al da hula ash color, wani dad'i ya mamayeta yau wannan mutumi maiji da class ya zama mallakin ta, lallai tanada sa'a a rayuwa, cikin sauri ta fice ta shiga gida a sace tamkar bak'uwa....
************
Buzu ya karkato da kyau yanai mata wani irin duba kafin yace "Miss Beauriful kinmin kyau.."
Sajida ta murmusa had'i da rufe fuskarta da tafukan hannu..
Murmushi shima yayi kafin yace "No pls ki bud'e min fuskar ki don bana gajjiya da kallo, those lips, those eyes.... Kai komai na fuskar ki na min kyau Miss Beauriful, wani kalan lipstick ne kam kika shafa don gaskiya ni ban tab'a ganin lips d'in da suka min kyau irin haka ba, kodai bakin naki ne haka, shiba red ba shiba pink ba, okay pitch ne koh..." ya k'arashe yana wani kashe idanu...
Murmushi Sajida ta sakar masa kafin tace "Ban shafa komai ba sai lipgloss..."
Buzu ya murmusa kafin yace "Toh gaskiya kinada kalan baki mai d'auke hankalin samari, nifa har naji kishin ki kar wani ya gane min ke haka tunda kince bikin Daddyn ki ake nasan maza zasu zo.."
Murmushin jin dad'i ta kuma yi kafin tace "Ai Daddy bazai yi wani event ba, Aunty Shemah ce dai zatayi liyafa gobe."
Buzu ya murmusa kafin yace "Har naji sanyi a cikin raina." ya sauk'o da idanunsa yana k'are ma jikinta kallo, saida ya d'an muskuta kafin yace "D'inki ki yayi kyau sosi dukda kin rufe da mayafi bana gani, amma dai ya kamata a nuna min na gani..." yayi maganar cikeda shagwab'a...
Shiru tayi bata ce komai ba sai murmushi k'asa-k'asa da takeyi...
"Pls mana Beautiful, gani fah kawai zanyi.."
Ba tareda ta kawo komai ba a zuciyarta ta d'an bud'e gyalenta tace "Ka gani ..."
Kallo ya bita dashi kafin ya murmusa cikin ransa yace _Not bad_ a fili kuwa cewa yayi tailor d'in nan yaci na masa kyauta, kodayake bama fah d'inkin bane yayi kyau jikin ki ne yasa d'inkin yayi kyau, you're beautiful..."
Murmushi kurum tayi kafin tace "Ai ka fini kyau.."
"Inji wa, ai ni my whole life ban tab'a ganin mai kyaunki ba, and babban buri na shine ki zama matata, da Daddy zai gane ma da an had'a bikin mu da nashi ne..." yayi maganar uwa gaskiya.
Zaro ido waje Sajida tayi kafin tace "Tab! Ai Daddy bazaimin aure yanzu ba zaice I'm still young kuma karatu yake so nayi sosai, Daddy ko waya bai bani ba har yanzu, wayata ma Aunty Shema'u ce ta bani without his knowledge."
Buzu ya gyad'a kai kafin yace "Na lura kinaji da Auntyn nan naki nima har kinsa naji ta burgeni, sabida a koda yaushe tana share ma princess d'ita hawaye, she's indeed kindhearted."
Sajida ta gyad'a kai tana murmushi kana tace "Gaskiya ne tana sonmu sosai.."
"Miss Beauriful nima fah na matsu ki zama matata, anya zan iya jira har lokacin da Daddy zaiyi accepting d'ina..." ya k'arashe kaman zaiyi kuka..
Idan yana mata shagwab'a dariya yake bata a wani b'angare kuma sosai yake burgeta sannan tana jin wasu feelings na musamman idan yana mata hakan.
Hira sosai suka sha kafin Buzu ya dage sai ya masu hoto kafin ta sauk'a a motar, sam bata son mata musu sabida tsananin soyayyar sa dake fuzganta, tanaji ya matso daf da ita jikinsu na gogan na juna ya masu hoton, zata kai hannu jikin marfin mota ta bud'e yayi saurin rungumo cikinta yana fad'in "Saura d'aya mana Princess.."
Saurin d'ago idanu tayi tana dubansa ganin yanda ya rik'e mata ciki... Cikin sauri ya saketa kafin ya soma bata hak'uri yana fad'in he didn't mean it.