Sashe 2
Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sajida ta gyad'a kai kafin tace " Ehen shiyasa nake fad'a maki Momy yau dole ta mance damu koda Daddy zaice ta d'auko mu tunda yau Aunty Shemah da Momma sun zo, ba lallai ta tuna da mu ba.. " Ta k'arashe tana sab'a jakar makarantar ta a kafad'.
Mik'ewa Maryama tayi ta kakkab'e rigar uniform d'inta kafin tace " Shikenan muje, Allah sa mu sami a daidaitan don kin san idan yamma tayi layin nan ba'a faye samu ba."
Suka jera suna tafiya yayinda Sajida taci gaba da fad'in "Wllhi har wani dad'i nake ji gobe babu wann shegen lesson d'in mutum zai koma gida da wuri. "
Murmushi kawai Maryama tayi sanda suka k'arasa bakin titi don neman abin hawa."
********
A razane ya mik'e had'i da damk'e wayar jikin kunnen sa cikin hannayen sa yana fad'in "Hisham me kake cewa, Innalillahi wa inna ilaihirraj'un,." Bai gama jin abinda Hisham ke fad'i ba yayi jifa da wayar ya fito a guje cikin tsananin birkicewa, gaba d'aya duk yanda ya wuce cikin asibitin kallon sa suke cike da firgici, basu tab'a ganin sa cikin irin yanayin ba... Wasu nurses maza guda biyu suka biyo bayan sa suna masa magana, inaa ko kulasu baiyi ba, bai ma san me suke cewa ba, motar sa dake ma'ajiyan ta kurum ya k'arasa, ya mata key kafin ya fice a guje cikin tsananin tashin hankali...
**************
Sanda Dr Ahmad Tahir ya iso wajen daidai lokacin Ambulance ta iso, chan k'asar gada ya hangi motar matar sa ga mutane sunyi chaa a wajen, ciki harda aminin sa kuma coworker d'in sa wato Dr Hisham..
Hisham dake tsaye yana matsan k'wallan munafunci yana hango AT yayi saurin k'arasowa yanda yake, AT d'inma k'ok'arin gangarowa k'asar gadan yake cikin tsananin tashin hankali, tamkar mutum mutumi haka yake tafiyar..
Rik'e sa Hisham yayi yana k'ok'arin saita kansa kafin yace "Friend, I shouldn't have called you in the first place, but babu yanda na iya ne Tahir ka..." Saurin katse sa Tahir yayi kafin yace "Hisham ina Aysha? " Daidai sanda aka soma fito dasu daga cikin motar....
Hango Ayshar sa da zaiyi ana zak'ulo ta cikin jini ya sauk'ar masa da wani irin jiri.. Ya nemi kalma guda saman harshen sa ya rasa, baisan sanda ya k'arasa wajen a guje ba ana d'aura ta saman gadon ambulance ya jawota ya rungume cikin jikin sa..
Shema'u da aka d'dd'ura mata bandage d'in k'arya sai nishin munafunci take sai ka rantse jin jiki take...
Cikin wani irin tsananin tashin hankali yake fad'in " No no Aysha, don Allah kar ki tafi ki barni, bazan iya ba...." bai kai aya ba wani irin kuka ya kufce masa yana rungume da ita cikin jikin sa.
*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:49PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊
_*SHAK'UWA CE*_
馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊
02
*漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�*
_馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_
"Maryama don Allah ki bari mu wuce gida mana gaba d'aya." Sajida tace sanda suke shiga kwanar Janbulo.
D'an jim Maryama tayi kafin tace "Kar ki damu Sajida idan dai naga jikin Ummi da sauk'i sosai zan biyo Uncle idan yazo gaida Hajiya sai mu kwana tare."
Sajida ta murmusa kafin tace "Shikenan na amince, Ki gaida (Maama Juu) da jiki." _Maama Juu shine sunan da Sajida da k'annen ta suke kiran Ummin Maryama da shike itace ta raine su gaba d'aya tun daga kan Sajida har zuwa kan autar su Ni'ima._
Maryama ta gyad'a kai tana mai amsawa da zata ji, kafin sukai sallama ta shige gida, Sajida na fad'in "Ki gaida birkitacciyan tsohuwar nan."
Dariya sukayi gaba d'ayan su Maryama tace "Zaki sani ne ai idan dai Hajiya ce." Ta shige gida suna masu waving ma juna.
Zaune Maryama ta hangi Hajiya k'asar bishiyar mangwaron da ya zamto wajen shak'atawar ta a can farfajiyan gidan. Hajiya na hangota ta washe baki tanai mata lale domin kuwa Allah Ya had'a jinin ta dana Maryama.... Duk tsangwama da masifah irin ta Hajiya batayi ma Maryama, hasali ma ita ke taya ta kwana, dukda kuwa cewa harta mahaifiyar Maryaman ba wai ta sha bane a hannun Hajiya.
"Hajiya ta barka da yammaci." Ta fad'i sanda take kwab'e sandals d'inta tana mai zama bisa darduman.
"Yauwa barka Maryama d'iyar albarka, an taso daga bokokon." Hajiya ta amsa sanda take karyan goro....
Maryama ta d'an tab'e fuska kafin tace " Wai ke Hajiya bazaki daina cin goro kina tara cuta ma cikin ki ba koh, kin dai ji abinda Uncle yace makomar mai cin goro.."
Tsegege kurum Hajiya ke kallon ta kafin tace "Tohhh wato kema Attahiru ya koya maki felek'e da firirta irin tasu ta 'yan bokoko ko,..? Ke kekam kikayi nisa a bokon bansan k'ak'a za'a k'are ba, inaga shinkafa ma sai kin haramta mana cinta... Kodashike ba laifin ki bane, SHAK'UWA CE da kikayi da Attahiru shi ya cusa maki wannan ra'ayin, inyi haba..... "
Maryama saida tayi datasanin soma maganar nan domin kuwa tasan shikenan yau kuma Hajiya ta sami maudu'i, idan ta soma batayi shiru ba.
Mik'ewa Maryama tayi had'i da d'aukar Jakarta kafin ta furta "Bismillahi.... Hajiya ni na shiga ciki.."
Hajiya ta k'ek'ashe idanu tana duban ta kafin tace "Ina Attahirun inji shi ya kawo ku?"
Maryama ta girgiza kai kafin tace "Adaidaita muka biyo."
Hajiya ta tab'e baki kafin tace "Agogo sarkin aiki yana can yana aikatuwa saikace inji."
"Toh ai lada yake samu a aikin nasa." Maryama ta fad'i sanda take saka sandals d'inta.
Hajiya ta kuma tab'e baki kafin ta warware bakin zaninta ta ciro wayar ta ta mik'a wa Maryama tace "Ungo maza kira mani lambar sa."
Maryama tasa hannu ta amshi wayar snn ta soma dialing layin AT. Ta kira yafi abinda yafi ba'a d'aga ba. Haba nan fah Hajiya ta soma sababi babu ji babu gani, wai da gangan yak'i d'aga wayar ta.... Ummi dake can sashen su saida tajiyo sababin da Hajiya take, ta fito don ganin da waye Hajiya take fad'an nan, ganin babu yara masu d'iban ruwa sai Maryama abin ya bata mamaki don tasan ko meye Maryama ta mata basa fad'a, kai idan sunyi fad'ar ma Maryama ta mata yaji da kanta take zuwa tayi bikon ta ta dawo da ita, don kuwa ba kad'an take k'aunar Maryama ba..... Kai harta Ilu mai gadi saida ya baro benchin sa ya nufo wajen shima.... Haba nan fah ta kuma kaure su da fad'a... Maryama kam me zatayi banda dariya, kai har tana Alla Alla Uncle yazo ta labarta masa.
**********
Sajida tana shigowa ta tarar da Momma zaune a parlor tana kallon tashar wasan kwaikwayo. Fad'awa jikin ta tayi a guje had'i da zama bisa cinyar ta.... Momma ta rungume ta tana fad'in "Inye lallai jikar tawa ta k'ara girma sosai, saura kawai ta kawo mana miji mu sha biki."
Sajida ta turo baki kafin tace "Haba Momma 'yar ni d'in nan, ai yanzu na soma karatu, sai na gama karatu na soma aiki kaman Aunty Shema'u kafin nayi aure..."
Momma dai murmusawa kurum tayi kafin tace "Bani fatan ki dad'e babu aure kaman Shema'u, duk maneman ta koran su take, toh yanzu dai da alama wannan likitan abokin mahaifin ki bazata korasa ba."
Sajida ta mik'e tana fad'in "Wai ina suke ne ma, nasan yau Momy da Aunty Shemah za'a k'ule a d'aki ana labarai."
"Auw! Ba tare kuke bane? " Momma ta tambaya.
Sajida ta girgiza kai kafin tace "A'a ni yanzu sauk'ata daga adaidaita, Daddy baije ba Momy ma haka, kuma malam iro bashida lafiya kwana biyu dama baya zuwa. Ce maki tayi zata d'auko mu ita Momyn.?"
Momma ta jinjina kai kafin ta dubi agogon bangon dake mak'ale a parlorn tace "Oh ni Kulu, wato dai Shema'u da Aysha idan suka had'u sai yanda mai ya k'are masu, wai fah gidan k'awarsu zasu a nan Hotoro amma kinji shiru har yanzu, kuma ita Ayshan da tayi waya ma Daddyn ku ta fad'i masa zasu fita tabbas yace su biya su d'auko ki makaranta, sunje sun shantak'e sun sami surutu."
Sajida ta murmusa kafin tace "Momma ai gashi na dawo, dama Aunty Shemah da Momy suka fita kam ai sai an gansu, nasan gaba d'aya Malls d'in garin nan sai sun zaga tas..... Bara naje na cire uniform" ta k'arashe tana d'an tsalle jaka da hijabi duka a hannu ta nufi upstairs.
Momma na nan zaune na tunani, haka kurum take jin gabanta na fad'uwa kaman wani abu zai sami yaran nata, musamman idan ta tuna Aysha ba k'oshin lafia bane da ita, k'aramin juna biyu gareta.... Tana cikin tunanin wayar ta dake saman center table Ya d'auki ruri ... Saida ta d'an firgita kafin ta d'au wayar.
Ganin bak'uwar lamba ce ya kuma sauk'ar mata da wani matsanancin fad'uwar gaba... Hannu na b'ari ta d'auki wayar tana amsawa.
Wani k'ara Momma ta Saki babu salati balle ambaton Allah ta shiga rusa kururwa tana fad'in "Wayyo ni Kulu na shiga uku, 'ya'ya na, wayyo 'ya'ya na... Wayyo Allah na...." Ai a tamanin Sajida dake d'akin ta tana zura riga ta nufo downstairs, su Jamal da Ni'ima harda Baba Delu suma suka nufo parlorn a tamanin...
Hajiya tana ganinsu ta k'arasa ta rungume su gaba d'aya tana kuka.... Tambayar ta suke meke faruwa amma ko kad'an bata sami zarafin amsa su ba... Ta dubi Baba Delu kafin tace ta tsaro masu tasi su tafi.... Momma ko la'akari da k'arancin shekarun Jamal da Ni'ima batayi ba haka ta dinga kuka ta kwashe su suka tafi asibiti, suma yaran haka suka dinga kuka ganin kakar tasu na kuka......
**********
Yana rungume da ita cikin jikin sa, kansa na kwance bisa k'irjin ta haka yake kuka kaman k'aramin yaro, su Hajiya Ummi da Kuma Maryama suna gefe suna nasu kukan suma, Dr Hisham sai k'ok'arin janye AT yake amma fir yak'i sakin Aysha, dole haka ya k'yalesa still yana rungume da ita yake kuka tamkar k'aramin yaro.