← Book details Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 65

Sashe 31

Shaquwace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai kawai Maryama keyi still hawaye na bin k'uncinta, ji take inama kowa zai fahumci Shema'u kaman yanda ta soma fahimtar ta, don tun farkon had'uwarsu da ita takeda wannan feelings d'in gameda ita, bata kuma cewa komai ba sai shigewa k'uryan d'aki datayi.... Maama Juu ta bita da kallo cikeda mamaki....

**************

AT ya girgiza kai a karo na biyu kafin yace "Hisham gaskiya ina tsoron fushin mahaifiya, Hajiya tayi fushi yanda baka tsammani, kawai inaga dai zan janye maganar neman auren Shema'u tunda dama bamuyi wata magana da ita ba, zan bata go ahead kawai ta Aura min koma waye d'in tunda ni dama ba auren soyayya zanyi ba...." ya k'arashe maganar yana bud'e maidaidaicin fridge dake a cikin office d'in nasa...

Hisham yayi shiru yana sauraren sa kafin yace "AT ya kamata ka sake tunani akan lamarin nan, fad'a da fushi halin Hajiya ne wanda i zuwa yanzu yaci ace ka saba da hakan, Allah yaga zuciyar ka yaga niyyar ka, kuma na tabbata daga baya Hajiya zata fahimici baka yanke mummunar hukunci ba, think about it, yaya yaranka zasuji idan sukaji 'yaruwar mahaifiyar su da take d'auke masu kewar mahaifiyar su itama zata tafi ta barsu, zasu fara tsoron SHAK'UWA da mutane tunda kowa tafiya yake ya barsu, kai kanka kasan dagan da aka sha da Hajiya kafin ka auri Aysha, Allah Ya jik'an Baba Shattima shi yayi tsayin daka har auren nan ya yuwu, grudges d'in dake tsakanin Hajiya da Momma shine kurum yake kawo cikas amma ba komai ba, kai ai kasan zaman hak'urin da Aysha tayi da Hajiya har tayi winning nata over, toh ina mai tabbatar maka hakance zata kasance da Shema'u ma, ..... Sannan AT you can't deny the fact kanada feelings for Shema'u, ko ba haka bane....?" ya k'arashe fuska cikeda alamun tambaya...

AT ya d'an yamutsa sumarsa da ystaun hannun sa kafin yace "Am I that obvious..?"

Hisham yayi wata murmushi kafin yace "Mutumi na idan kowa bazai fahimce ka ba kasan banda ni, ba jiya ba na sanka Tahir, so shawarin da zan baka ka sami Shema'u kuyi magana ta fahimta sannan ka tafi Rano kazo ma Hajiya dasu Baffa Ado tunda nasan su zasu fi mata bayani ta gamsu...." Ya k'arashe yana tsiyaya ruwa a cup...

Nazarin maganganun yake kafin ya shiga gyad'a kai yace "Na gode Hisham, I'll see what I can do..."

Hisham ya gyad'a kai yana mai kurb'an ruwansa.. A zuciyarsa kuwa fad'i yake _I won't rest till you're completely ruined, wllhi AT sai na rabaka da filin mahaifina kaman yanda ka rabani dashi..._

***********

Tunda AT yazo ma Shema'u da maganar aka rasa wa yafi wani farin ciki tsakanin ita kanta uwar gayyan wato Shema'u da kuma Momma kai harta yaran AT su Sajida,...

Tsalle Sajida tayi ta rungume Shema'u tana fad'in "Aunty na fiki farin ciki, dama idan Daddy zai yi aure toh it should be someone like you, yanzu bamuda fargaban zaki tafi ki barmu wata rana, you're staying here for good..." ta k'arashe tana k'ara hugging Shema'u.... Ai Shema'u kam har yanzu gani take tamkar a mafarki, ko iya amsa magana batayi sabida murna sai gyad'a kai kurum uwa k'adangariya..

Shi kansa AT yasha mamakin ganin Shema'u ta amince dashi lokaci guda, wata zuciyar tace " k'ila tsananin son yaranka da take yasata amincewa da kai lokaci guda...

Washe gari ya d'auki hanyar Rano, Baffah Ado k'anin mahaifin sa da kuma Kawu Sunusi yayan Hajiya sunji dad'in batun Attahirun sosai, gaba d'aya sun goyi ba suka kuma d'unguma suka taho Kano don mara ma d'ansu baya, tsarin da Attahiru ya yanke shine dai-dai ko a shari'a hakan yayi babu laifi..

Hajiya kuwa cewa tayi ai da bai sha wahalan d'add'ago su ba, daga nan iyanin da d'aurin aure suka shige don ita tuni ta masa addu'an dacewa, bata nuna masu komai ba, su kansu sun sha mamaki don sun san fad'anta sunyi tunanin bazasu wanye lafiya ba...

Shirye-shirye ake babu Kama k'afan yaro idan ka d'auke Maryama da Hajiyar ta wad'anda suka koma gaba d'aya babu walwala... Maama Juu tuni ta koma gidan AT kasancewar Momma tareda Shema'u zasu wuce Jalingo don gudanar da shirye-shiryen biki...

Tana zaune saman gadon Hisham yana shafe bayanta kaman tsohon maye yana fad'in "My Allied yanzu zakiyi tsada sosai idan kika shiga gidan AT."

Shema'u ta murmusa had'i da juyowa suna fuskantar juna kana tace "Kar ka damu nida kai bazamu rabe ba ai, amma ka sani da zaran ka mallaki abinda kake so daga gareshi zaka k'yale min shi..." Ta k'arashe tana rungumo wuyar sa..

Dariya ya fashe dashi kafin yace "Niko zanga yanda za'ayi ki mallaki Tahir shi kad'ai ki rabasa da mahaifiyar sa da 'ya'yan sa.."

Shema'u ta murmusa sannan taci gaba da fad'in "Wannan mai sauk'i ne don na gama tsara yanda zanyi, Jarabebbiyar tsohuwar can zan d'an sa ayi brushing bakinta ne a rage mata wargi, ita kuwa babbar d'iyarsa mai shirin zama k'aramar karuwa da zaran ta haife masa shege zai sallameta, su kuwa k'ananan idan basubi hanyar da uwarsu tabi ba zan salwantar dasu ta wani hanyar..." ta k'arashe maganar tana tuntsirewa da dariya..

Hisham kuwa wata kafiran murmushi yayi cikin zuciyarsa yake fad'in _Ni kad'aine nakeda abunda zanyi destroying d'inki lokaci guda Shema'u, idan kika betraying d'ina I won't think twice, zan shayar dake mamaki..._ ya k'arashe zancen zucin nasa yana kai mata capka...

*Sameena Aleeyou Mrs*
[2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘

*SHAK'UWA CE*

💘💘💘💘💘💘💘💘

*26*

*©Sameena Aleeyou...✍🏼*

_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_

A zabure ta mik'e tana kuma karanta sak'on, ita kad'ai take girgiza kai ba tareda ta iya furta koda kalma ba. Mata mai mata gyaran jiki dai kallo ta bita dashi ganin yanayin ta, a d'an kid'ime ta furta "Lafiya Amarya..?"

Shema'u ta d'an saita kanta kafin ta sakar mata murmushi tace "ba komai Dakura, ina zuwa..." Bata jira amsarta ba tayi ficewarta zuwa wani d'an store dake tsakanin corridor, tana shiga ta maida k'ofar ta rufe sai waige-waige take, Momma da fitowar ta kenan ta sallami wasu bak'i ta hangi Shema'u ta shige store, gabanta ya yanke ya fad'i, me Shema'u zatayi cikin store?.... Bata gama tunanin ba wasu 'yanuwansu suka yi sallama haka dole tayi ta kansu ta fita sabgan Shema'u amma zuciyarta sam bai kwanta ba da yanyin da taga Shema'un.

"My Alhaji pls ka tsaya ka saurare ni wllhi nima bansan su Momma na shirya wannan auren ba sai da abin ya k'arato, kaga yaran nan ne sam basu yarda da kowa ba sai ni basu SHAK'U da kowa ba sai ni ever since their mother passed away, pls ka tausaya min kar kayi....." Bata kai aya ba yace "Rufe min baki and don't take me for a fool, jiya na sanki da zaki wani kashe murya kina min k'aryar banza, dama tunda naga kin mak'ale a gidan Daktan nan nasan da abinda kike shiryawa, kin maidani ATM machine d'inki koh tun yaushe nake binki da maganar aure amma kink'i amince min da shike idanunki sun rufe da soyayyar mijin k'anwarki koh... Ko ki fasa auren nan ko kuma nazo har wajen d'aurin auren na fad'a ma mijin who you really are.."

Huci kawai Shema'u keyi ga zafin store da ya addabeta, zufa tako wani sak'o tsattsafo mata yake, take wani tunani ya fad'o mata ta Saki wata kafiran murmushi kafin ta soma fad'in "Alh Aminu don't you dare do that, I won't go down alone, tareda kai zamu ruguje idan kayi tunanin rusa min rayuwata, Shema'u nake, komai nasa a gabana sai nayi nasara, kasan inada labarin zaka tsaya takarar d'an majalisa...." ta kuma yin murmushi kafin taci gaba da fad'in "Wllhi wllhi zan maka sharri irin wanda imagination d'inka bai tab'a baka ba, zan ruguza maka rayuwarka dana iyalanka, wllhi idan kayi yunk'urin rabani da Tahir da iyalansa sai na rabaka da kowa naka, kai sai na maida kai abin kwatance, wllhi 'ya'yanka sai sunji su kashe ka da hannayen su shi yafi masu sauk'i..... So a shawarce mu ci gaba da rufawa juna asiri tunda ni nasan jikina kake so kar ka damu bazaka daina samu ba muddin zakabi dokoki na..." ta k'arashe tana kashesa da murmushi...

Tsoro ya cika Alh Aminu, tabbas baya fatan ya rasa kujeran da yake nema tunda gashi har ajiye aikinsa yayi ya shiga siyasa tuk'uru, sannan yana son 'ya'yan sa fiyeda komai a duniyar nan... Murmushi ya sakar mata kafin yace "Toh ai ke d'ince kinsan bana jure rashinki, ina jiranki a guest house d'ina tunda kin hanani fitowa..."

Tab'e baki tayi kafin tace "Ta ina zan fito bayan 'yan d'aurin aure sun cika ko ina..."

Alh Aminu ya dara kafin yace "Haba giwar mata wai dama so nake kizo kinga sai na baki nawa gudumawar sannan idan zaki min adalci ai ya kamata kizo muyi sallama,."

Ta d'an juya idanu kafin tace "Cash ne ko check.?"

"Sai wanda kika zab'a" ya bata amsa kai tsaye...

Murmushi tayi kafin tace "Ka saurare ni." daga haka ta katse wayar...

Tana cikin waige-waige tana k'ok'arin fitowa ta ji an jawota an shige d'aki da ita, ba kowa bace Momma ce, sai faman huci take tana watsa ma Shema'u mugun kallo kana tace " Jarabebbiya babu yanda zaki je, banda shegen fitina inji gidan wani za'a kaiki yau uwar me zaki fita kiyi da wani inyi.."

Shema'u ta buga tsaki kafin tace "Momma kinafa shige gona da iri, idan banje ba cewa yayi zai fallasa ma AT halina na bin maza sannan kinsan idan wannan aure ta fasu ba AT kawai ba harta su Sajida jikokin ki sai sun tsane mu daga ni har ke, don haka a shawarce ki barni na fita kuma ki rufa min asiri sabida dolenki ne..." ta k'arashe tana juya idanu hannu rik'e a k'ugu...
Chapter 31 · 0% Book details