← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 72

Sashe 67

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

duka kaɗan na rage. Washe gari sassafe ta yi mana sallama ta kama hanya, kafin dai ta tafi ta faɗamun watannin daya rage haihuwarta sabida kintata zanyi in tawo tunda bamu da network. Haka rayuwa taita tafiya su Taiwo sukaita bani wahala in wannan ya warke ciwo sai wannan ya kama, canjin ruwa da zaman ƙauye duk saiya sa suka rame ga ƙuraje caɓa_caɓa ya fito a jikinsu babu masaka tsinke. Ranar da suka cika wata guda a ranar Bara'u ya tawo ya kwana a gidan Dada washe gari suka wuce. Na haɗama yaran goma sha tara na arziki. Taiwo Atampa biyu na bata. Na kulle atampa biyu daban na matan Gwadabe. Toye da Kahinde nasa Uwani ta sai musu kaya kala bibbiyu ƴan kanti duk da dai irin na ƴan ƙauyene amman dai na siya musu. Na siya ms Iyabo kaya itama. Dada ta haɗa musu tsarabar ƙauye, hakama Yafendo, da su Baɗɗo. Aka dai haɗa musu tsaraba rigijib harda zabi huɗu aka haɗasu dashi wai suyi kiwo. Kuɗi masu yawa Bara'u ya miƙo mun da kaya cikin babbar ƙatuwar leda yace wai inji Gwadabe yace a bani kuma yanayi mun barka. Allah sarki Gwadabe. Dan Allah Bara'u kace nagode Allah ya saka mishi da Alkhairi " "Babu komai ai tsuntsun soyayya. Naso mu tawo da Sakina ma amman tayi nauyine sosai haihuwa ko yau ko gobe. Amman wata rana kwatsam zaki gammu." Allah sarki Sakina Allah ya raba lafiya. Nima indai na shigo kano nanda wata ɗaya in sha Allah zan shigo Takai ɗin da izinin Allah." Da haka mu kai sallama ya tusa yaran a gaba suka tafi. Mu kuma rayuwa taci gaba da garawa damu. Shayarwa tasa nayi kyau na ciccika sosai. Hankalina ya kwanta sosai a tafiyar Hama gida har ga Allah ni dai saida nayi fatan inama karta dawo. Gabaki ɗaya gidan da matan gidan duk sun sake. Ƴan biyu kuwa suna ganin gata a wajen Yafendo da ƙannen Yaya Hamma. Haka dai naci gaba da shayar dasu cikin tsabta da lafiya. Abun mamki nayi ƙiba sosai baku ganni ba, sabida ƴan biyu suna da tsotso sai nima cin abincina ya ninka, dani dasu duk mukai ɓul_ɓul damu." Yau tun safe na tashi da shirin zuwa dubo Dada. Da wuri naima yara wanka nayi mana wankin kayanmu na shanya, na goya ƴan biyu na fito. Ɓarayin Yafendo na nufa nai mata sallama inaso in je dubo Dada daga can zan leƙa Cubu dan ance bata ji daɗi ba." "Sai kun dawo ƙila anjima nima in leƙo gidan in duba Adda dan jiya ciwon kai ya sata a gaba" Ni banma sani ba sai yanzu da nake ji. Ayya ai kuwa zan tafi mata da ƙwayar bature ta haɗiya. Sai mun dawo Yafendo" Fitowa nayi duk inda na wuce sai na tsaya an gaisa sun ga ƴan biyu kafin in wuce. Ga rana sosai a garin zafi akeyi sosai safiyace amman har rana tayi zafi. Sai naji idona wannan marar ganin ya soma ciwo har yana zubar da ruwa. Da sallama na shiga gidan Dada ina haki abunka da masu kitse. A tsakar gida na samu Dada a kwance Yusufu na mata fifita Kari kuma tunda ban ganta a tsakar gidanba nasan bata nan an tafi talla. "Jabu kune da safe haka? Saifa da nace da Baɗɗo ba sai sun faɗa miki ba shine saida ta faɗa" Zama nayi a kan tabarmar, na sunto ƴan biyu da suketa kukan zafi. Yusufu ya karɓi ɗaya Dada ta tashi zaune itama ta miƙo hannu in sa mata daya. A_a Dada kiyi fama da kanki Usaini nauyine dashi ga tumbuɗi" Murmushi tayi tace. "Kema lokacin da nake koyonki ai kin fishi girma da nauyi. Cika bayana dam kike yi. Duk inda na wuce sai an kalleni, har ciwon ƙirji saida ya kamani a goyonki. Miƙo shi" Murmusawa nayi. Ni dai Allah ya jarabceni da tausayin Dada. Sanyin muryarta kaɗai ka iya cika idona da ruwan ƙwalla. Usaini na miƙa mata na tashi na ɗebo ruwa a randa na ɓalla mata fanadol biyu. Na bata ta sha ta kwanta. Na samu Yusufu ya riƙe mun yaran nayi mata kwalima, na wanke mata tufafinta tas na share tsakar gidan. Bani na bar gidan ba saida na yi mata miyar tumatur na aika Yusufu ya siyo mun nama da shinkafa. Sai wajajen biyun rana na nufi gidan Cubu. Da sallamata na shiga cikin gidan abun mamaki kishiyoyinta da girmansu wasu da yaransu a gidan miji ma amman suka saka Cubu a gaba uwargidan ta zauna a ƙaton cikinta sai ihu take yi. Ragowar kishiyoyin suna ranƙwashinta. Subhanallaah me zan gani kasheta zaku yi ko me?" A firgice suka juyo suka zuba mun idanu. Hawaye suka gangaro a kumatuna. Cubu numfashinta sai kokuwa suke yi ita dashi" Mrs Bukhari
Chapter 67 · 0% Book details