← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 72

Sashe 31

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ɗauke ba. "Sannu yaya jikin naki, ashe baki da lafiya?" Nan Yafendo ta shiga yi mishi faɗa da yare, sai ruwan faɗa take yi inaji tana ambaton Hama dai. Shuru yayi baice mata komai ba. Uwani da Baɗɗo sai haƙuri suke bayarwa, ni dashi munyi shiru muna kallon juna, ina hango tausayina a cikin ƙwayar idanunshi. A cikin kallon ƙudan da muke yima juna a zuchiyata ina roƙon Allah ya karya mugun asirin da Hama tayi mana domin mu samu zaman lafiya" Ana cikin haka likita ya shigo da takaddar sallama ya miƙama Hamma. Jiki a mace ya fita. Likitan ya dawo da dubanshi gareni. "Jabu mun sallameki. Amman duk bayan kwana talatin zaki ci gaba da zuwa muna duba lafiyar idanun naki. Zamu ɗauraki akan maganin ɗigawa safe, rana, dare. Sannan ki guji gasken rana, kuma karki dinga jagwalgwala idanun. In sha Allah karku saka damuwa a zuchiyoyinku idon zai warke, ba mutuwa yayi ba, matsalace kawai amman indai muka ɗaurata bisa magani zai farfaɗo da jijiyoyin idanun da suka sandare. Wannan taruwar jinin ita kuma ba wata matsala bane da sannu zai washe" Haka dai wannan likita yaita ƙarfafani da bani shawarwari. Yaya Hamma yana dawowa daga biyan kuɗin sallama, ya miƙo ma Baɗɗo ledar magunguna, suka harhaɗa kaya muka fito. A mota ya ɗauramu ya biya kuɗin. Mu muka kama hanya, shi kuma ya koma bakin aikinshi. Ga ciwo ga rashin kyan hanya. Bamu muka isa jaɓɓi ba sai yamma sakaliya. A tsakar gidan duk muka samu matan gidan dawowarsu daga talla kenan. Hama na wanke_wanken kwanukan tuwon jiya tana ganinmu ta wani taɓe baki. Uwani na riƙe dani wallahi ban ankaraba naga kan Hama a cikin bokitin ruwan wanke_wanke Uwani ta dulmiya mata. Da ƙyar Hama ta samu ta kwaci kanta dambe ya kaure na tashin hankali tsakanin Uwani da Hama. Matan gidan sun kasa raba wannan faɗa dan Uwani ta mahaukaci tayi musu, duk wanda yazo kusanta saita gabɗa mishi kwano. Saida fa maƙota suka cika gidan wannan faɗa ya rabu da ƙyar. Duk Uwani ta fashe ma Hama Baki, har nono uwani ta riƙe ma Hama kamar zata tsige mata shi, Hama sai ihu take faman yi. Ita kuma Hama ta gama yakushe ma uwani fuska sai jini suke zubarwa. "Wallahi tun wuri kije ki tone asirin da kika ma Jabu. Shegiya muguwa mai baƙar zuchiya kawai, bagidajiya. Ku kuma munafukai ƴan iska ƙyaleku Jabu tayi wallahi dani nake aure a gidannan duk saina saisaita muku zama." Hama dai babu bakin Magana sai haki take ta famanyi. Dan iyakar dakuwa wallahi ta daku ainun. Da ƙyar matan unguwa suka tunkuɗa Uwani ɗakina. Yafendo ta dubeni tace. "Jeki Jabu ki kwanta ki huta. Ke kuma Hama ki tattara ki koma gidanku. Kuma kiyi gaggawar karya asirin da kika yi mata. Ki sani Jabu ɗiyatace ko a gidan wani take aure sai inda ƙarfina ya ƙare wajen ƙwatar mata hakkinta. Balle kuma ɗana take aure. Kece bare a cikinmu dan haka kiyi gaggawar ficewa a gidannan" Ni dai naji daɗin dukan da Hama tasha, kuma raina yayi fari da hukuncin da Yafendo ta yanke. Ɗaki na shiga na samu Uwani sai fito da kayan ɗakina take yi. "Iyabo ga kujera a tsakar gida ki zauna akai ko ki kwanta. Saina caje ɗakinnan tsab na zaƙulo abinda aka ajjiye a ɗakin." Zama nayi a kujerar ina kallonsu ita da Baɗɗo sai zaƙule zaƙule suke yi, amman fa an fitar da gabaki ɗaya kayan ɗakin babu komai. Uwani ta miƙo mun fulo, kafin in amsa sai naga ta cire fulon a riga. Hmm mutum abun tsoro saiga fulo a ɗan farke. Uwani da ƙarfi ta kama fulon ta yage saiga jar laya a ciki. Ba shiri na miƙe na shiga ɗakin bakina a buɗe" "Kingani ba Iyabo. Lallai wannan kishiyar taki tsinanniyace. Ya tabbata ita tayi asirin rabaki da Hamma harya dikeki haka. To Alhamdulillah asirinta ya tonu, kuma na rama miki dukan da tai miki itama yanzu zanje in kuma cin ubanta" Zabura uwani tayi, nayi saurin tarota da ƙyar uwani ta yarda ta haƙura ta bar Hama haka. Uwani yanzu yaya zamu yi da wannan layar to?" "Buɗewa zamu yi, mu ƙona komu jefata a masai" Baɗɗo tace. "A jefa a masai kawai basai an buɗeba, ni tsoro nake ji. Amman a nuna ma Yafendo tukunna" Nayi carab nace. A'a kar a nuna mata. Hankalinta zai tashi da yawa. Kuma ƙila hakan yasa ta tursasa Hamma ya sau matarshi" Wata uwar harara Uwani ta bini dashi tace. "Au ke kinfi so ku zauna tare, an ganota ta nan taje ta kuma ƙullo sabon asirin da bakisan ma ko rayuwar zata rabaki da'ita ba. Wai bake kika ce mun kinsha kama garukan magani a ruwan wankanku, ko banɗaki ba, bake kika faɗamun ko abincinta ran girkinta taki miyar sai an barbaɗo miki magani ba. Iyabo anya kinsan ciwon kanki kuwa?" Uwani tabalbalin kenan ƙawar faɗa da daɗi. Murmusawa nayi ina hawaye. Uwani bawa mai cikakken imana yadda yake da ƙaddara imma mummuna, imma kyakkyawa. Na daga cikin sunnar rayuwa, rayuwa bata taɓa tafiya face sunyi kafaɗa da kafaɗa da matsaloli tari daban_daban. Ni bazan so in kashe auren Hama ba in ɗauketa daga kan yaranta ba. Duk mummunan halina bazan so Hama ta fitar dani a gidana ba. Wallahi in halinta ne dama ki rubuta ki ajiye zata kuma. Watarana shi shaƙundun ɗinne zai kamata da idonshi. Anan yana da damar zama da'ita ko rabuwa da'ita." "Ahh haba dan Allah? Ai kamata yayi a mayar da layar cikin fulon kawai. Kinga watarana Hamman da kanshi zai gano layar" Dariyar dole tasani, itama duk da a cikin ɓacin rai take saida ta dara. Miƙo mun layar tayi da bismillah a bakina na karɓa na jefa a masan gidan. Alwala nayi a bakin rijiya na wuce bukkar Yafendo na yi sallar magriba da Isha. Nasha magunguna, na ɗiga na idon. Yafendo ta dure mun tuwo tace. "Maza ki daure kici tuwon Jabu. Sai kiyi kwanciyarki, in bacci ma ya ɗaukeki sai ki kwana abunki. Ina tsaka da cin tuwon Yaya Hamma, da Haruna mijin Safiya suka shigo. Gabaki ɗaya hankalin Yaya Hamma a kaina yake gaba ɗaya. Zama yayi yana fuskantata, ɗagowa nayi muka haɗa idanu. Kallon da yake yi mini mai cike da fassarorine masu dama, saƙone daga zuchiya zuwa ga zuchiyar da ake so da ƙauna. "Yaya jikin naki, ki cire hannu a tuwon bari in siyo miki nama ki ci" A jejjere yayi maganar cike da kulawa tsantsa. Idanu na lumshe a raina nace. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya kuɓutar da Annabi Yusuf daga cikin rijiya. Kuma yasa wuta ta zama ni'ima ga Babanmu Annabi Ibrahim." "Dada bari inje yanzu zan dawo zan kawo ma Jabu nama ne" Ya fice da sauri ba tare da yaji me Yafendo zata ce ba. Murmushin farin ciki naga tana yi. Niko farin cikin da nake ciki bazaima musaltuba sam, sai ajjiyar zuchiya nake saukewa. Yaran Hama ne suka shigo. Mai sunan Yafendo riƙe data goyen, ta tsakiyan na biye dasu ashe Hama bata tafi da'ita ba. Karɓarta Yafendo tayi ta goya su kuma ta zuba musu tuwo suka zauna suna ci. "Assalamu alaikum. Yafendo sannunku." Cewar Uwani kenan tana daga bakin ƙofa. "Yauwa am Uwani. Kun gama kwalimar ne?" "E mun gama shine nazo kiran Jabu ta kwanta" "Gaskiya ne. Jabu kije ki kwanta, kar ki tayarma da mijinki wata maganar ɓacin rai. Kibi dashi kamar babu abinda ya faru. Sauran ki barmun a hannuna. Tashi kije Allah ya ƙara karewa" Kaina a ƙasa nace. To Shikenan Yafendo saida safe, Haruna saida safe" Haruna dake zaune tunda ya shigo baice komai ba yace. "Allah ya ƙara sauƙi, ki yi haquri da abinda ya faru. Bamu da shaidar dukan mace a gidannan. Akwai dai wata maƙarƙashiya a ƙasa, kinsan sha'aninku na mata sai haƙuri. Na dawo tun daga hanya aka tareni ake faɗamun wai anyi dambe gagarumi a gidannan wai dake da Hama. Yaya Hamma ma an bashi labari har tafiyar Hama gida duk yaji." Murmushi nayi nace. Nagode Haruna. Sai da safe" Nai musu sallama nabi bayan Uwani har zuwa ɗakina. Sun kuma sake ma kan gadon nawa wajen zama. Kwanciyata ke da wuya muka jiyo sallamar Yaya Hamma ya shigo tare da abokinshi Baɗejo. Waje Uwani ta basu suka zauna. "Ga wannan naman Uwani kuci ke da Jabu." Uwani tasa hannu ta karɓi ledar. Mayafi na sako na fito daga cikin labulen da gadona ke ciki muka gaisa da Baɗejo. Shiru ya ɗan biyo baya can dai Baɗejo yace. "Jabu, ni bansanma ta ina zamu soma baki haƙuri ba. Amman duk da haka kiyi haƙuri abinda ya faru dan Allah ki ɗaukeshi kamar ba'aiba. Ni wallahi da badan Hamma da bakinshi ya labartamun abinda ya faru ba. Alƙur'an da duk wanda ya faɗa mun wannan maganar bazan yarda ba. Shi kanshi yace baisan sanda abun ya faru ba. Kiyi haƙuri ki mishi afuwa dan Allah. Ki dubi girman ƴan uwantaka da soyayyar da Hamma yake yi miki kiyi haƙuri. Sannan naji labarin iftila'in daya afka ma daddobinki. Allah yasa da abinda ya tare. Munji labarin faɗan daya ɓalle a tsakanin Hama da ƙawarki Uwani. Uwani ayi haƙuri dai dan Allah koma me ake tunani bazai wuce zargiba. Ita kuma Hama koma me zata yi a wannan gaɓar bazai wuce kishi ko zigazigin ƙawaye ba." Baɗejo ya daɗe yana tausata. Mai gayya mai aikin yayi tsamo_tsamo duk kunyata ta lulluɓeshi. Ni dai nayi ɗan guntun murmushi nace. Babu komai Baɗejo wallahi na yafe. Kuma wannan abun daya faru bai rage son da nake yima Hamma ba saima ƙaruwa da yayi. Tunda har yasan yayi laifi ya kuma ɗakkoka dan kawai a bani haƙuri na haƙura. Batun dabbobi kuma Allah yasa da abinda suka tare" Naja bakina na tsuke. Ajjiyar zuchiya Yaya Hamma ya sauke a sirrance. Shima haƙurin ya kuma jaddamun dai, nace komai ya wuce. "To komai ya wuce Hamma. Ina mai baka hakuri a bisa dukan da naima matarka. Dokin zuchiyane yasa har abinda zai faru ya faru. Saimu haɗu mu yafi juna" Cewar Uwani kenan. Yaya Hamma yace. "Ai babu komai daliline nasan dole yasa faruwan hakan." Nan Baɗejo yayi mana sallama, Yaya Hamma ya
Chapter 31 · 0% Book details