Sashe 43
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai Iyabo laulayi kike yi ne, ko ciwo kika yi mun yi waya har sau biyu dake baki sanar mun ba? Anya kina kallon mudubi kuwa? Kin ƙare kin lalace ko dai babu zaman lafiya tsakaninki da Hamma ne. Ga ɗakin kishiyarki na leƙa sai naga wayam. Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Uwani halin da nake ciki yafi ƙarfin duk wannan lissafin naki. A cikin dabaibayi nake, cikin rijiya mai gaɓa dubu." Wasu siraran hawayene suka gangaromun nayi sauri na share su. Labari naba Uwani na halin da nake ciki. Saida ta zubar mun da hawaye bayan ta gama saurarena. "Yanzu kina cikin irin wannan halin mawuyaci kika kasa sanar dani Iyabo? Kuma sai yanzu kuka yinƙura neman magani ma?" Uwani ina kai kukana wajen Allah shine zai mun maganin duk abinda ke damuna. Ni ko gidan magani da Yaya Hamman yace muje yau bana son yi mishi musu ne kawai shi yasa zanje. Amman da shawartata yayi da kukana zanci gaba da miƙawa wajen Allah yana sane dani bai mance dani ba. Ni garinne ya fitarmun akaina, auren ma ya fice a raina, sai inji kamar in yi ficewata in tafi ma kawai." Uwani ta dafani tace. "Komai yai tsanani sauƙi na nan zuwa. Duk abinda yai farko dole yai ƙarshe Iyabo. Amman kam kishiyarki ce tayi miki asiri ko kin ƙi, ko kinso tunda ai ta faɗa miki sai zaman gidan ya gagareki, kuma sai kin fita tsirara. Rashin bacci ai somi_ somin haukane. Amman muje wajen mai maganin muji me zaice mai kuma zai bamu. Kinga tashi kawai muje gidan matar abokin Hamman kawai mu wuce." Ko abinci Uwani bata ci ba, ta dai sha ruwa. Allah yasa abincin dana dafa tazarce nayi har dare na cika babbar kula na dare. Sallama naima Yafendo nayi mata ƙaryar zamu je gidan Cubu Uwani ta gano ɗakin. Muna fita sai gidansu Baɗejo, dama matarshi a shirye take goyo kawai tayi muka wuce wani ƙauye gaba damu sosai, munyi tafiya a mashin mai nisa kafin muka iso. Malamine sak ba boka ba, dama Yaya Hamma yayi mun bayani. Sai naga zahiri harda almajirai gasu a gabanshi. Amman layi ma ake bi ga mata da maza anata layi. Mun daɗe sosai kafin ma layin yazo kanmu. Ni kaɗai na isa wajen nai masa bayanin dalilin zuwan nawa tsab, da duk yadda nake ji, harda furucin da Hama tayi a kaina. Kai ya girgiza da lalatacciyar hausarshi yace. "A lalle haukatakin taso tayi, tunda ko runtsawa bakya yi, ƙarfin adda'ar da kike yi ne yasa burinta bai cika ba a kanki ba. Amman Allah ya fita. Yarinya ni ba boka bane, bana ba da laya. Sai dai zan rubuta miki ayoyin Alkur'ani in rubuta a allo in wanke miki. Sannan zan miki tofi da zaki dinga shafe jikinki, da habbatus sauda da zaki dinga turare ɗakin ki dashi. Ba asiri ba ko sammu akayi miki da izinin Allah saiya karye. Amman sai zuwa gobe zaki dawo, sannan ki dena kwanciya da janaba, ki dinga alwala kafin ki kwanta. Allah ya ƙara sauƙi gobe uwar haka sai ki dawo" To Malam Nagode sosai. Nawa zan bayar abun sadaka?" Murmushi yayi yace Sadaka bata kaɗan bata yawa, abinda Allah ya hore miki ajjiye ki tafi, inma baki dashi zanyi miki dolena." Nera dubu guda na ajjiye ina godiya na samu su Uwani muka kama hanya. Sai la'asar sakaliya muka shigo, a lokacin matan gidan duk sun daddawo anata aikace_aikace. A ɗakin Baɗɗo duk muka zube, muka yi Sallah. Baɗɗo suka gaggaisa da Uwani ta fita ta bamu waje "Iyabo wani tunanine ya faɗo mun. Kin tuno da wannan adda'ar ta karya sihiri wadda na baki akayi yima Gwadabe mai ganyen magarya? To yau ba sai gobe ba kiyi" Idanuna na lumshe tare da yin hamdala ga Allah. Na mance da wannan maganin karya sihirin in banda yanzu da Uwani ta faɗamun. Ai babu wata wata na aiki Baɗɗo ta ɗebo mun ganyen magarya a ɗakina guda bakwai, ta kawo mun ruwa a bokiti na tottofa duk ayoyin ban mance komai ba. Na adana bokitin anan ɗakin. Uwani wallahi na sha'afa da wannan magani na karya sihiri, daga yanzu in Allah yaso ya yarda bazan sake rabuwa dashi ba, lokaci zuwa lokaci zan dinga wanka da sha, tunda jarabawar gidannan ta kishiya mai asirice." "Wannan shi ake kira nama ya dahi romo ɗanye. Uwar miji a gidan auren fari ta hanaki saƙat. Wannan gidan kuma kishiya na neman rayuwarki. Ga kaya duk na siyo miki komai tashin hankali ya hanamu maganar kayan ma" Dariya nayi mata nace. Ke dai bari ana takai wa yake ta kaya? Bari inje in samu in watsa ruwa me gidan yana hanya. Ga kiraye_kirayen sallar magriba anayi." A ɗakin Yafendo nayi Sallah, kana na fito na raba abinci, ina kan rabawa Yusufu yazo karɓa musu na zuba musu nasu da nasu Dada. "Adda ance in faɗa muku Cubu bata da lafiya tana kwance a gida" Da sauri na ɗago na kalleshi. Meke damunta Yusufu?" Yace. "Ban sani ba dai, amman ance ciwon sosai ne" kwanukan abincin na miƙa mishi. Allah ya bata lafiya, gobe zanje in dubata. Ku kara haƙuri kunji ko Yusufu? Kaine babban kanka a yanzu kayi ƙoƙarin kulawa da kan ka. Duk abinda kuke buƙata kazo ka sanar mun kaji ko?" "To Adda, bari in tafi sai da safe" Yai mun sallama ya tafi. Ina fitowa Yaya Hamma na shigowa. Da sauri na ƙarasa na karɓi ledar hannunshi nayi mishi barka da dawowa. Daga ɗakin Yafendo kai tsaye masallaci ya wuce. Duk muna tsakar gida kowa na sha'anin gabanshi. Sai da naga wucewar Yaya Hamma ya nufi ɗakina na bishi ɗauke da tiren abinci. Saida na jima ina addu'a kafin nasa kai na shiga ɗakin. Wannan tashin tsigar jikin dai saida naji, kuma sai inji anyi tsaye a kaina. Shiru nazo na samu yaya Hamma ba dai yadda na saba ganinshi ba, kamar akwai damuwa a fuskarshi. Yaya Hamma lafiya kuwa na ganka a cikin damuwa?" Ajjiyar zuchiya ya sauke ya dubeni yana dariyar yaƙe. "Babu komai halin rayuwane, yau da gobe kinsan sai Allah. Ya jikin naki, kunje wajen maganin?" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Munje harda Uwani ma, da rana sai gata tazo" Ya yi dariya yace. "Uwani ƙawar amana kenan. Allah sarki. To yaya kuka yi da mai maganin?" Na labarta mishi yadda muka yi, yana saurare yana cin abincinshi. Abincin loma biyu yayo ya ajjiye. Furarma kurɓa biyu yayi kawai ya rufeta. Ni gabaki ɗaya na kasa gane mishi. Na tambayeshi yace babu komai. Bana son in matsa mishi dole in barshi, sai dai in naga damuwar tafi haka yawa dole in kuma tambayarshi. "Zanje wajen Baɗejo ba daɗewa zanyi ba. Kema nasan ɗalibanki suna tsakar gida suna jiranki." Tare muka fito, shi yayi waje ni kuma na ƙarasa wajen ɗalibaina mu kai karatun dai babu armashi yanayin yadda naga Yaya Hamma zahiri a cikin damuwa yake. Bamu kai lokacin tashi ba na sallamesu, na faɗa musu na kawo kayayyakin mata gobe kowacce ta kullo kudinta zan buɗe haja. Suna cikin murna Yaya Hamma yazo ya wuce mu. Da idanu na bishi jikinshi duk a sanyaye ba laka. Jikina a mace nabi bayanshi a kwance naje na sameshi yana kallon sama. Ƙur na ƙura mushi idanu ina nazarinshi. Yaya Hamma dan Allah menene matsalarka ya kamata ka sanar dani damuwarka karka sani a wata sabuwar damuwar" Tunda nake magana yake kallona, hannayenshi ya miƙo mun halamun inje. Banyi musuba nabi umarninshi. "Babu komai Jabu. Ki dena damun kanki bana jin daɗin jikin nawane yau shiyasa tun ɗazu a wajen aiki nake jina wani iri. Magani naje Baɗejo ya bani nasha." Nan na shiga aikin yi mishi sannu. Wannan dare ya bamu wuya sosai dan har ji nayi kamar ana kiran sunana. Sassafe na yi amfani da wannan tofi, na sha na shafe jikina dashi tas. Abun da yafi komai bani mamaki a madadin Yaya Hamma ya tafi wajen aiki sai kawai na ganshi ya koro shanu ina duƙe ina wanke kayan yaranshi da nashi. Tsayawa yayi suka gaisa faram_faram da Uwani ya dubeni da sandarshi a wuya yace. "Ni zan tafi kiwo ki mun addu'a Murmushi nayi nace. Ubangiji Allah ya kareka da kai da shanun a shiga jeji lafiya a fito lafiya" Kallona naga yanata yi, ni dai saina tsinci gabana da faɗuwa. Harya fice a gidan na wanke hannuna na bishi. Uwani ina zuwa" Ina fita na sameshi a ƙofar gida yayi shiru yana kallon shanun, suma duk sun tsaya suna jiran shugabansu ya kirasu su soma tafiya. Yaya Hamma yau baka da aikine zaka tafi kiwo?" Ɗagowa yayi ya kalleni. A madadin ya bani amsar tambayata sai yace dani. "Ina sonki ina ƙaunarki duk runtsi. Wannan halin lalurar da kike ciki yana tayar mun da hankali tunda a gidana kika samu wannan lalura, ga rasa idanunki da kika yi sanadiyyar dukan da ni Hamma nayi miki kaicona, ina tsoron ranar da zaki gaji da wannan auren ki nemi barin rayuwata Jabu, ina tsoro da fargabar wannan rana. Akwai wani mai magani da aka kwatanta mun in an gwada na malamin da kika je wajenshi baiyi ba, zan ɗaukeki in Kai ki can wajen wancan. Kiyi haƙuri Jabu, kinsan dai ina sonki kuma lalurar ta dameni ko?" Ga murmushi a fuskata ga hawaye inayi. Ina bala'in son Yaya Hamma ku kunsan komai, kuma duk sanadiyyar aurenshi ne nake samun wannan matsalolin, inajin auren ya fice a raina, inajin ƙauyen ma ya isheni ƙarfin sonshi da nake yi ke riƙe dani a ƙauyen da ƙarfin adda'a. Amman a kullum sai in dinga ji kamar in zunduma ihu ko in fice a guje. Da zaran naji hakan ya bijiromun sai inta karanta la'ilaha'illah anta subhanaka inni kuntu minal zalumin, hasbunallahu wa'ni'imal wakil, la haula wala ƙuuwata illabillah. Sai inji dama dama. Duk rintsi ina tare dakai Yaya Hamma. Bana fatan zuwan ranar da zan gujeka kasa a ranka zamu kasance har izuwa ƙarshen rayuwarmu. Soyayya ba ƙarya bace ina maka son so domin Allah ka yarda dani ka dena fargabar zuwan ranar da zan gaji da aurenka. Babu wannan ranar, bakasan girman matsayinka a zuchiyata bane." Murmushi yayi mun, nima na mayar