← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 72

Sashe 12

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ban gansu ba. Tare da su Baɗɗo muka ci kazarnan da tea muka kora da dafaffiyar madara. "Bari inje in harhaɗa kayan nonona sai inzo mu tafi Adda Uwani" Fita tayi, fitarta ke da wuya uwani ta soma zolayata. Da dariya na bita kawai. Baɗɗo ta gama haɗa ƙorenta na Nono ta leƙo tai kiranmu akan muje. Muna fitowa Hama na ɗaura ƙoren nononta a ka, ta fice tana tsaki. Yafendo muka je mu kaima sallama. "Jabu har da ke za'aje?" E Yafendo inaso inga kasuwarne" na bata amsa ina sauke kai ƙasa. "To Shikenan. Nima yanzu ina gamawa zan biya ta wajen Adda Daso kafin in wuto kasuwar." To Yafendo muma in muka dawo zamu biya can uwani zata maata Sallama. A wannan kasuwar naga tarin ƙauyawa iri da kala. Ga masu tuyar ƙosai da masu saida burodi, komai akwai a wannan kasuwar gasu da arhar nama, ga kayan hatsi, gasu nono, mam shanu, madara, suturu, harda shanu da tumakai, kaji, zabbi, rediyone tocila, su kayan miya ɗanye da bushasshe babu fa abinda babu. Ga maza da matan Fulani damƙam wasu sunzo siyayyane irinmu, wasu kuma kasuwanci ya kawosu irinsu Hama da Baɗɗo. Haka mu ka shawo siyayya nan muka baro Baɗɗo. Bayan mun dawo muka ya da zango a gidan Dada anan muka tarar mai nagge yazo ya tusa ƙeyar su cubu yace ba zasu zauna a hannun Dada ba. Su Baffa Musa suna zazzaune ana mayar da zancan Dada sai hawaye take yi muka shigo. Baffa ne yai mun bayanin halin da ake ciki, da korar Amaduyal da yayi a gidan nashi kan yace bazai iya dena zuboma Dada abinci in matarshi ta dafa ba. Shine ya ƙwace shanayen dake hannun Amaduyal ɗin ya fito musu da kayansu. Ajjiyar zuchiya na sauke bayan na gama jin komai nace. To babu damuwa, su Cubu su je su zauna wuya bata kisa. Amaduyal kuma ga ɗakinan ku share kai da matarka ku zauna. Shanu dama ina da burin siya ko babu yawa zan danƙama ka dinga yi mun kiwonsu, a jiki ku dinga samun madara, nono da man shanun da zaka kula da iyalanka da abincin da Dada zata ci. Dada ki dena kuka Allah zai rufa mana asiri." Baffa Musa ya sauke ajjiyar zuchiya yace. "Shikenan an samu masalaha. Jabu sannu da zumunci Allah ya baki waɗanda zasu yi miki kema. Mai Nagge kuma ina ƙara jan kunnenki kar ki kuskura wani abun ya shiga tsakaninku, ko bayan raina kar ku tayar da maganar shanun Daso daya danne ya zama mallakinshi mugun mutumne wanda zai iya kashe duk wanda zai tayar da wata magana akan shanunnan. Duk shanun da kikaga yana gadara dasu na Daso ne wanda ta samu a gado, labari aka bani rugga_rugga sai yawon bin bokaye yake yi kuma duk akan a rufe bakinmu kar mu tada zancen Shanu ne. To mun yi shiru zamu haɗu a gaban Allah" Ba komai Baffa mun bar maganar in sha Allah. A dai nema mana shanu sai mu siya manya da ƙanana sabida shi Amaduyal ya soma fita kiwo, duk da gidan babu inda za'a iya garke. To anan nake cewa daku mu tara ranar monday in Allah ya kaimu. To ina ƴan team Hamma goga dai ya ciri tuta. Ina masu ƙin Hamma me zaku iya cewa ina sauraren ra'ayinku. Mrs Bukhari
Chapter 12 · 0% Book details