← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 72

Sashe 38

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauke na kwantar da kaina akan ƙirjinshi. Hannu yasa yana shafar bayana mai cike da tsoka yana mun raɗa a kunnena. "Menene ya tsoratamun ke Jabu, mafarki mummuna kikayi?" Ni dai sai ajjiyar zuchiya nake saukewa, a hankali ya kwantar dani yana shafar kaina. Ni dai harya koma baccinshi , idanuna biyu. Dana rufe idanu sai wannan inuwar ta dawo, dana runtse idanu nayi adda'a inna buɗe sai inga babu, gashi babu tsarki a jikina ƙaƙa_sara_ƙaƙa. Babu damar yin sallah. Adda'a inna kamo wannan sai in faɗa waccan cikina ya duri ruwa sosai da sosai. Daren yayi tsayi kafin garin ya waye. Ko da na shiga bayan gida yin wankan sallah ina tsaka da yin wankan sai naji kaina na juyawa tsigar jikina na tashi. A lokacin ji nake yi kamar in fito tsirara dan tsoro da firgici. Da ƙyar da ɓarin jiki na gama wankan, na fito na tarar Yaya Hamma ya tafi masallaci. Ina ganin ɗakina amma wallahi na kasa ɗaga ƙafata in shiga. Dana gaji da tsaiwa da ɗaurin ƙirjin kamar mahaukaciya sai gani a ɗakin Baɗɗo. Ko ita data ganni saida ta tsorata. "Adda lafiya kika fito haka, ko wani abun ya sake haɗaki da Yaya Hamma ne?" Sai naji hawaye na zuba a idanuna. Babu komai ke dai jeki ɗakina maza ki ɗakkomun kayana in saka zanyi Sallah " Baɗɗo tayi maza taje ta ɗebo mun kayan nawa nasa nayi Sallah a ɗakinta. To a gaskiya a wannan lokacin nayi sallar ne, amman bana ce ga abinda na karanta ba. Inyi adda'a na kasa sai naji zuchiyata tayi wani irin mugun cunkushewa. Sai kawai na saki kuka. Baɗdo na shirin fita na kirayi sunanta. Karki kira Yafendo, ki riƙe mun sirrina Baɗɗo. Ke dai ki taya ni da adda'a dan auren ya isheni ya fice mun aka zaman ƙauyannan." Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta. Ni kuma sai kuka kawai nake rerawa a haka Yuguda ya shigo ya iskemu. Ya tambayi Baɗɗo wani abun ya sake faruwa ne. To itama ba sani tayi ba, juyawa yayi sai gashi ya dawo tare da Yaya Hamma, sai suka fita suka bamu waje, suna fita na faɗa jikinshi na ƙara fashewa da kuka. Ƙanƙameni yayi wallahi ina jiyo dukan da zuchiyarshi take yi, jikinshi har rawa yake yi. Ya kasa cemun komai bai hanani kukan ba, sai bayana yake shafawa. Da yaga bani da niyyar yin shirune ya ɗagoni muka haɗa idanu idanunshi sun zama kamar gaushi, fuskarshi ta dawo kalar tausayi, ga soyayya muraratan ina karantawa a idanunshi, fuskarshi, dama gangar jikinshi. Muryarshi a dakushe yace. "Menene ya faru, me akayi miki kike kuka haka, bakya jin tausayinane, ko dan kinga bana son kukanki ne shi yasa kikeyi dan ki horani?" Idanu ya lumshe ya buɗe su a kaina. Yaya Hamma wallahi ina sonka, Allah ya gani inason zama dakai, ina son ƙare rayuwata dakai. Amma....." Da ƙarfi ya mayar da kaina ƙirjinshi numfashinshi yana hawa da sauka. Banyi aune ba ya ɗagoni ya zura bakinshi a cikin nawa, tsabar ina sonshi haka na dinga shan wannan yawun mai ɗan bashi, dukda yana goge bakinshi kafin yaje masallaci. Ni ko goge bakin nawa banyi ba. Mun daɗe a haka kafin ya dubeni, nima shi nake kallo sonshi na sake ninka kanshi a zuchiyata. "Mu tafi ɗakinmu Kar muyi abun kunya a ɗakin ƙanne" Ba musu na bi bayanshi. A ɗakin Yafendo muka yada zango muka gaisheta. "Dada yau batai ɗumamen safe ba, jiya mun kwana bata jin daɗi. Amman zata ba Baɗɗo ta dumama kafin Amaduyal yazo ɗaukar abincin Dada" Kaina na sunne. Yafendo tace. "Ayya sannu Jabu Allah ya ƙara sauƙi" Kaina na ƙasa na amsa mata da ameen. A wajen na sulale na fito na barshi. Baɗɗo har ta shiga ɗakina ta fito da ɗumamen ma. Tana tsaye da Amaduyal suna tattaunawa na isa wajen ina ƙaƙaro fara'a. Me ake tattaunawa ne Amaduyal?" Dariya yayi yace. "Adda jiya da daddarene Yusufu yazo yake faɗama Dada wai yau za'a ɗaura auren Cubu. Ya bada aurenta ma abokinshi Baffa Modibbo" Idanu na zare. Abokin Baffan naku akaba Cubu yarinya karama da'ita. Ita za'a ba tsoho?' Baɗɗo tace ." "Hmm ai tunda Baffa ya faɗa babu makawa. Damma Baffa Modibbo dattijon arzikine. Sai dai Hajaru ƴarshi aminiyar Cubu ce, tare suke zama a wajen saida Nono." Shiru nayi lamarin duk yabi ya dameni ya addabeni. Ga matsalar data tunkaroni, ga kuma wannan matsalar. Ajjiyar zuchiya na sauke. Dada me tace da taji wannan labarin? Na tambayeshi. "Babu abinda tace face fatan alkhairi. Ai aurenta yafi zaman gidan. Dan ke bakya zuwa gidanne da in kika ga irin rayuwar da sukeyi sai kinyi musu kuka. Gidan Baffa Modibbo kuma abinci me kyau suke ci. Kuma matanshi basa tallar Nono yana da yawan shanaye, kuma sha'awar haɗa iri dasu akeyi." Shiru nayi ina hango cutarwar da hakan zai haifar. Amman yana iya, babu har sai naji ta bakin manya, duk da suma da halama babu abunda zasu iya. Ɗan daɗin da naji mata bai wuce na barin hannun matan ubaba, da kuma samun ƴanci daga gantalin zuwa tallar nononnan. Ita kanta Baɗɗo da sannu zan hanata wannan tallar nono, ta kama sana'ar yi. In kasuwancinta na man shanu ya kankama da Uwani shima zai rage wani abun. Dan Uwani tace ta dinga soyawa tana tara mata ko na nawa ne in tazo, ko inni zanje a tafi mata dashi. Amaduyal yace. "Dama Yafendo nazo faɗama. Baffa Musa yace mu je duka mu sameshi a gida har daku. Bari inje wajen Yafendo" Ya tafi ya barmu. Na dubi Baɗɗo nace. Kar ki faɗama kowa halin dana shiga Baɗɗo. Babu kuma abinda Yaya Hamma yayi mun ke dai ki tayani da adda'a kawai" Murmushin jin daɗi tayi tace. "To Shikenan Adda, Bari in ɗunduma tuwo in kawo muku naku" To Kawai nace, na wuce. Ina zuwa ƙofar ɗakina ai sai na doge, tsigar kaina taci gaba da tashi. In shiga na kasa tsoro nake ji. A wajen Yaya Hamma ya sameni. Hannuna ya riƙe muka shiga bayan nace. A'uzubillahi minal shaiɗanun rajim. Ina sauke ɗayar ƙafar a cikin ɗakin sai naji abu ya kuma shiga jikina. Take sai ɗakin ya shiga jujjuyamun. luuu nayi na tafi zan faɗi, Yaya Hamma ya taroni, amma tare dashi muka faɗa kan kujerar nayi mishi nauyi bazai iya taroni ba. A zabure ya miƙe yana jijjigani. Ni kuma na kasa buɗe idanuna dan ɗakin jujuyawa yake yi dani. Adda'a kawai nake yi ina girgiza kai ina hawaye. Nafi minti goma a wani hali wanda bazan iya fassarawa ba da ƙyar na dawo daidai. Na faɗa ƙirjinshi ina kuka. Ni Allah bazan zauna a ɗakinnan ba sai dai ka canja mun ɗaki. Ko kuma in tafi Kano" Kanshi kawai ya ɗaga sama yama rasa me zaice. Sallamar Baɗɗo ne yasa ya sakeni ya tashi. Tiran hannunta ya karɓa ya shigo dashi. "Sakko ki karya. Sai in kaiki gidan Dada ki zauna. Inna dawo aiki zan biya in ɗaukoki hakan yayi miki Jabuna kafin mu nemi mafita?" Kai na gyaɗa mishi halamar yayi mun. Hakan kuwa akayi muna gama cin abincin muka fito tare, ya bani dubu ɗaya yace in yi girki acan in naje muci Yafendo bata nan ma ta tafi kiran Baffa musa, Baɗɗo ke faɗa mana. Saina dubeshi nace. To kaje aikinka zamu je gidan Baffa Musa ni da Baɗɗo. Zan tafi da yaran sai mu wuni acan gidan Dada" murmushi yayi mun yace. "To Shikenan. Ki kula dan Allah. Saina dawo, ku gaishe da Baffa Musan. Amman me akeyi acan gidan nashi da ni ban sani ba?" Baddo sai ta bamu waje, ta haɗa kan yaran suka fita. Ni kuma na labarta mishi abinda ake ciki da ƙin auren da nakeyi sabida hakan ka iya cutar da lafiyar Cubu. Shi kuma ya nuna mun ai babu komai kuma ba'a kanta aka soma ba, kuma gidan da zata shiga gidane mai daraja gidan arziki. A haka dai mukai sallama shi ya tafi aiki, mu kuma muka nufi gidan Baffa Musa. Acan tattaunawa kawai akayi akan gudunmawar da zamu haɗa, bawai akan auren dole da tsoho da za'ayi mata ba. To kayayyakin ɗakina da sukai saura suna gidan Dada nasa an ajjiye mata harda kujera 1_1. Na ware mata dogayen riguna da zanin gado har kala uku masu kyau, ta samu kular zuba abinci mai tsada da tire harda plate da tsokali. Ni duk wata gudunmawata na ajjiyeta tuni. Nan muka gama tattaunawa mukai ma Baffa Musa sallama muka tawo gidan Dada harda su Yafendo A'i. Daga nan suka shirya dan zuwa gidansu Cubu, amman ni ban dani, ni sai zuwa gobe in an kaita ɗakinta sai inje ayi yinin biki dani. Bodi ( keken shanu) suka tafi da kayan zuwa can gidan Mai Nagge. Ni da yarana kuma mu kai zamanmu a wajen Dada. Wankinta na tattaro na fito dashi tsakar gida, na soma wankewa. Mai sunan Yafendo kuma na kirata na aiketa siyo kayan miya da garin tuwo. Ina gama wankin Dada na shiga aikin kwalime mata ɗaki, ga miyar kuka harna kaɗa na maida ruwan tuwo. "Jabu sai yaushe kayanki zasu zo ne, maƙota suna yawan shigowa neman kaya sai dai Kari tace musu kayan suna hanya" Ninkin kayan na ɗan dakatar nace. Dada suna hanya. Da zaran sun iso zaki ga Uwani zata kawo mun. Gobe ma inaso zan shiga gari gidan matar ogan Yaya Hamma in dubosu. Zan kira Uwanin a waya muji." Kai kawai Dada ta gyaɗa mun. Na ci gaba da aikina sai da mukayi sallar muka zuba tuwo da zafinshi muka ci muka ƙoshi dam. Dama har dare nayi tuwon dan inna koma gida bazan yi girki ba. Tsiren da ya zamema Yaya Hamma jiki wajen siyo mun, shi zanci in sha tea abuna. Ƴan biki sai magriba suka dawo niƙi_niƙi da tuwon biki an kawo ma Dada nata. Yafendo A'i tace. "Jabu har yanzu baki tafi gidanki ba?" Murmushi nayi mata nace. Yace in ya dawo zai biyo mu tafi. Sannunku da dawowa" Suka shiga ciki. Baɗɗo ta tsaya a wajena tace. "Adda dama a wajen bikine adda Daso take faɗan wai Hama ta kusa dawowa. Kuma kullum sai Yaya Hamma yaje wajenta. Yanzu haka ma tace
Chapter 38 · 0% Book details