← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 72

Sashe 18

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa Musa yace. "Wajen kiwo ba damuwa bane. Ko nan gidanku zai dinga zuwa yana garkesu. Ko gidana, ko gidan me sunanki Jabu. Zamu bari ranar Talata ranar kasuwa sai muje akwai shanu na siyarwa da ake kawowa. In ma ba haka ba akwai inda zamu je da Amaduyal din mu samo miki. In yaso ko tunkiya da rago sai ke ki siya ki watsar a tsakar gida, suna cin ƙanzo da ciyayi sai kiga kin ta da garke, in wata matsuwa ta kamaki sai ki ɗaga abinki ki siyar. To Shikenan Baffa zuwa gobe Amaduyal zai kawo maka kuɗin in sha Allah. Duk yadda kudin suka yi sai ayi abinda ya dace dashi kuma zuwa jibi zan buɗe kayana in soma siyarwa, abinda na kuma gagganɗawa sai a sake siyowa, har kaji da zabbi inaso in saka, naga su Baɗɗo duk suna kiwonsu" Baffa Musa yayi mun dariya yace. "Jabu mutanen birni, ta dawo matar ƙauye" Nima dariyar nayi. Nan dai muka gama abinda zamu yi, zuwa bayan la'asar Uwani taima su Dada sallama akan gobe zata wuce, daga haka sai muka koma gida. Babu kowa a gidan, sai awaki da kaji da suketa shaƙatawarsu. Tsakar gidan duk datti da tarkacen bokatai da tukwanansu na dafa nono ƙudaje sai fareti suke yi. Mayafina na rataya a saman bishiyar gidan na ɗauki tsintsiya tun daga kitchen na zakulo shara, a iyakar kitchen kawai saida na fitar da tarkacen ledoji da toka ƙaramin buhu. Duk girman tsakar gidannan na share tas, na haɗe musu kayan kazantarsu a bakin rijiya inda suke wanke'wanke da wanki. Lokaci guda gidan yayi fes ras dashi. Karar girki dana gani a jibge a kusa da ɗakin Baɗɗo na ɗebo Uwani ta tayani muka hura wuta abu kamar wasa wuta ta kama na tsayar da sanwar miyata. Uwani tayi mun jajjage a babban turmin gidan, su citta, tafarnuwa, diyar miya duk muka daka na wanke naman rago na sashi a ɗayan gefen na murhun na sanar muku baki bibbiyu suke gina murhun, saina ɗaura tafashen nama a ɗaya, ɗayan kuma na tsayar da sanwar miyar karkashi. Awa uku cir muka yi a kitchen kafin na kammala tuwona na shinkafa miyar karkashi yaji nama. Soyayye Tuwon na ƙuƙƙula a leda na cika babban flaks, na bare sabon filas tuwo da miya na zuba na kai ɗakin Yafendo da dawowarta kenan. "Sannu Jabu gida yayi kyau sosai. Allah yayi albarka ya baku zaman lafiya" Ameen Yafendo nagode. Ina fitowa daga ɗakin Yafendo sai ga matan gidan sun dawo zuga guda da goyo da ƙananun yara raɓe_raɓe ga siyayya iri_iri sunyo. Suna ganin yadda gidansu ya sake sunsan aikinane. Sannu da zuwa nayi musu na shiga binsu da tuwon girma ɗaki_ɗaki. Da nazo kan Hama bari kuji abinda samodarar tace dani bayan taƙi amsar tuwon fur. "Au a rabe zamu dinga yin girkin? Aina ɗauka duk wacce miji yake ɗakinta ita zata girka abincin ?" Murmushi nayi mata. A'a ko wacce girkinta zata dinga yi, in ranar girkinki tazo kina wajen tallar Nono ni ina gida bazanci abinci ba kenan?" Ai saita zabura tace. "Ai kema zakiyi tallar nononne, wallahi ban yarda a raba girki ba" Dariya nayi mata na wuce da tunowa na ƙarama Baɗɗo. Bayan na fito wanka na zuba tuwon na aiki yaro ya kaima Dada dan nayi alƙawarin ko ƙasa na dafa tare zamu ci da Dada, kuma nasa Baɗɗo ma ta roƙi mijinta ta dinga aikama da Dada abinci duk a haɗu a rufa ma kai asiri. Yaya Hamma basu suka shigo ba shi da abokanshi sai bayan isha sai gasu. Naci dariya, sunyi santin tuwo sosai ɗaya daga cikinsu ma cewa yayi abincin ƴan aljannah ne. Sai tara da rabi suka yi mun sallama suka tafi suna faɗin zasu turo matansu koyon girki. Ni kuma sai nayi amfani da damar wajen tallata musu kayana tare da sanar dasu jibi zan buɗe dilar. Duk sunce zasu ba matansu kuɗi su zo su sai zanin gadon makka, kunsan dai kayan makka da farin jini. Bayan Yaya Hamma ya shigo mun kaɗaita komai ya lafa sai nake labarta mishi duk yadda muka yi da Baffa. Shima ya goyi bayan ayi hakan babu damuwa. Sai naji nasamu nutsuwa sosai. Washe gari sassafe Uwani tai mana sallama ta kama hanyar kano harda ƙaton zakaranta da Baɗɗo ta bata. Muna dawowa daga rakata ni da Yaya Hamma, yana shirin fita sai muka jiyo sallamar Amaduyal. Kuɗaɗen dake hannuna na tattare dubu ɗari ukku na bashi su a baƙar leda, ragowar kuɗaɗen dama nayi musu mugun ɓuya ƴan kuɗin hannuna bai wuce dubu saba'in ba haka wanda suke fili ɗan na zara a kashe wutar data taso. "To ni zan tafi aiki. Akwai abinda kike buƙatar in siyo miki a birni ne?" Ya tambayeni na girgiza mishi kaina. A'a babu sai dai in maka fatan dawowa lafiya. Amman kafin ka fita ya kamata ace akwai kayanka ko kala biyune anan ɗakin bawai kullum in kayi wanka zaka fita sai dai kaje ɗakin Hama ka saka ba" Dariya yayi ya shafa fuskata. "Hakane Jabuna. Zan ɗebo inna dawo. Kar ki manta kafin Hama ta fita ki je ki karɓo garin tuwo da man shanu. Inna dawo zan nuna miki naggenki da zaki dinga tatsar nono a jikinta, kinga sai Baɗɗo ta koya miki yadda ake fitar da man kya dinga fitarwa da kanki kin samu na girkin ki ko, madarar da Nono sai ki ta sha tunda kinƙi tallar nono " Dariyar soyayya mu ka yi ma junanmu. Na dinga ragargazo mishi adda'a yana ameen_ameen harya fice daga lungunmu. Sai da naga tafiyarshi ina rakuɓe a bakin lungun harya fita Hama ta bishi da gudu raɓe_raɓe da nononta guda ɗaya ta ciroshi ta wuyan riga. Ga Yuguda mijin Baɗɗo a wajen Hama ko a jikinta. Da ganin yadda take magana faɗa take yi ilai kuwa sai naga tana share hawayenta. Kaina na girgiza nayi komawata ɗaki nayi ɗaiɗai a ƙasa ina tura wainar ƙwai ina danne maiƙon da ruwan tea na me madara. Saida na gama karyawa na fita tsakar gidan, tun sassafe na kaima Yafendo nata abun karin. A zaune a ƙasa durshan na samu Hama tana jijjiga madara kwananniya dan fitar da man shanu. Kanta babu ɗankwali ya ilahi zo kuga gashi wallahi kamar a india amman annakiya zata kashe shi, wani irin dattine a daddanƙare akan da ciyayin katifa. Ina kwana Hama ya kwanan yaran?" Baki ta taɓe tace. "Lafiya" Dama Yaya Hamma ne yace ki bani garin tuwo da ɗanyan mai" Dariya tayi harda shewa tace. "Ai Hamma ya gama kwanaki ukkun da zaiyi a ɗakin ki, kinga harya faɗamun kalar miyar da zan kaɗa ta dare. Saiki bari in kwana ya zagayo kanki sai kizo in baki" Ta ƙarashe da Dariyar ƙeta harda sakin waƙa da fulatanci. Turus nayi a tsaye ina jujjuya kalaman nata. Taya akayi kwanan suka zama uku. Kenan harda darena na farko da tazo ta jaye shi harda daren a lissafi kenan? Wata bazawarar dariya nayi dan wallahi yau sai Hama taga bariki zan nuna mata nayi zaman gidan karuwai a saudiyya. Kaina kaɗa nayi tafiyata, matan gida sai kallona suke yi, Baɗɗo har ɗaki ta biyoni tana bani haƙuri ta kawo mun man shanu ƙwarya guda da garin jar masara nata. A'a ki koma da masarar, man shanun dai na karɓa." "Adda sabida ke fa ko gaisuwata Hama bata amsawa, ta hana yaranta wasa da nawa yaran. Ko a mota muka haɗu ta dinga tsaki kenan. Kuma ƙawayenta ke zugata wallahi baranma Daso. Jiya a kasuwa sun haɗu da Daso naga ta bata ƙunshin wani magani naji ana cewa da tayi amfani dashi Shikenan. Ni dai iyakar abinda naji kenan. Adda kiyi a hankali Hama hatsabibiyace" Dariya nayi ina mamakin Daso, ita da take ƴar uwata amman da ita aka haɗe kai ana son sai anga bayana. Ni zancan asiri_asirinnan na Hama zancan gaskiya yana tsoratani duk da na dogara da Allah, amman bansan wacce iriyar illa zatai mun ba a kwana a tashi. Numfashi naja nace ma Baɗɗo. Da izinin Allah asirinsu bazai yi tasiri a kaina ba. Bari in baki tea da ƙwai ki kaima Dada, kullum kafin ki fita ki leƙo ki tafi mata dashi. Itama saida taci nata ta fita dana Dada da garin tuwonnan. Suna fita na nufi ɗakin Yafendo na tsiri yi mata kwalima na gyare mata ɗaki tas na fito da wankinta na haɗe da nawa na wankesu tas. Na wanke ƙazamin bayan gidan tas da toka, na tusa sharar tsakar gidan. Sai gidan ya dawo abun sha'awa har wani fili ya sake yi gidan yana da yalwa sosai da sosai. Da rana na dafa mana farar shinkafa ina da miyata a ɗakin Yafendo naci nawa, yaran gidan duk da iyayensu suna ajjiye musu abinci a ɗaki na harhaɗa kansu na zuba musu a tire suka daka wawar abincin. Can sai gasu Yusufu da Kari sun shigo, a ɗakin Yafendo suma suka yada zango aka gaggaisa na zubo musu abincin. Kari na cin abincinne take sanar dani. "Dama Dada ce tace mu zo mu sanar miki an siyo shanun, harda tumakai biyu da akuya. Zuwa anjima Amaduyal zai kawo su nan gidan shanu sunyi kyau" Murna ta kamani sosai, Yafendo ta sanya mana albarka ta riga tasan komai a wajen yayyenta. Na tambayi Yusufu ya suke suna dai samun abinci ko? "Wallahi a'a Adda ana bamu dai na safe. Amman na dare wata rana sai dai Cubu ta siyo rogo a ɓoye ta kawo mana muci, ko ƙosai, ko ƙarago. Dama Kari ce ke sa mana abinci kafin Baffa ya koresu. Shiru nayi idona ya cika da hawaye Yafendo tace. "Yanzu su Hassana sai su hanaku abinci dan basu da imani bayan taƙamar tasu dukiyar ta Daso ce akai mata fin ƙarfi?. Babu komai ke Jabu aiki ya sameki sai ki ƙara sanwa su dinga zuwa suna ɗaukar abincin a wajenki. In yau kin basu, gobe sai Baɗɗo ta basu. Mu ba ma bari su tagayyara ba, watarana sai labari.' Godiya nayi ma Yafendo sosai, Yusufu shima yayi farin ciki sosai da wannan bayanin. Hakan kuwa akayi dan su Yusufu basu tafi ba har saida na gama abincin dare, shi ya tafi musu da nasu,
Chapter 18 · 0% Book details