Sashe 52
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
awa ɗaya ina abu ɗaya. Ni kaɗaice a gidan Yafendo ta tafi raka Yafendo A'i zuwa gidan Baffa Musa, daga can zasu je gidan Yafendona. Ni dai inata aiki jikina sukuku. Masu tallar nono an dawo sun sameni na gama suyar kaza na zuba a jar miya ina soya miyar. Ga shinkafa ina zaune inata tsinta da akwai ƙasa sosai. "Kun dawo sannunku" Safiya da Baɗɗo ne dama kaɗai suke amsa sannu da zuwa in nayi musu. Ni dai inata aikina bayana da wuyana duk yabi ya riƙe gam. Sai magriba na wanke shinkafar na zuba. Naje nayo wanka nayi Sallah. Ina idar da Sallah na fito na raba abinci. Ɗaki_ɗaki saida na zuba ma kowa dake shinkafa abun ɗaukanice barinma mai miya da nama. Ina ɗaki shiru ina sauraren motsin da cikina yake yi, idanuna a lumshe ina mamakin yama za'ace anyi awo bani da ciki. To in hakanne meye a cikina yake motsi? Shigowar Yaya Hamma ne yasa na buɗe idona na yi saurin karɓar ledar hannunshi. Kayan miyane a ciki da maggi. Sannu da zuwa Yaya Hamma ya aikin. Wanka zaka soma ko cin abinci?" Zama yayi a ƙasa ya jingina da kujera yace. "Yaya jiki_jikin. Kin ga likita da kuka je asibitin?" Sai gabana ya faɗi. Amman saina jure nace. Naga likita yaronka yana cikin ƙoshin lafiya" murmushi yayi yace. "Allahu ya rabaku lafiya. Allah ya baki lafiya. Bari in soma wankan inzo in baki labari" Ruwan wankan naje na juyo mishi na dawo. Saina ga jini digo uku a ƙofar ɗakina. Gabana ya yanke ya faɗi wata fitinar ce kuma ake so in taka kenan? Cikin gida na shiga na ɗakko tsintsiyar sharar tsakar gida da ragowar ruwan Baɗɗo dana gani a bokiti nazo da bismillah a bakina na wanke jinin tas, nayi adda'a na shige ɗaki ina mamaki. Ina zuba mana abinci Yaya Hamma ya shigo ganin shinkafa da miya harda kaji yasa ya zauna yana kallona. "A ina kika samu kuɗi haka Jabu?" Murmushi nayi mishi kawai nace. Kai dai kaci zan maka bayani " "A'a aimun bayanin tukunna dai. Kaddai zuwa kika yi kika ari kuɗi Jabu. Nasanki dai akwai ɓoye sirri bana jinki" Da dai naga ya fara zargi saina sanar mishi abinda ake ciki. Na ɗaura da cewa. Kuɗin yana jakata na adanasu. Amman dan Allah inaso sati mai zuwa ka yarje mun in je Kano. Inaso zan kaima su Iyaa Debisi ziyara, da Uwani" Shiru yayi kawai yana kallona irin kallon tausayi. Murmushi kawai nake yi dan murmushin yana kwarara mun zuchiyata. "Allah yayi miki albarka. In sha Allah Jabu zan riƙeki da amana ni dai nayi miki alƙawarin ba zaki yi kuka dani ba. Batun zuwa Kano bazan hanaki ba. In lokacin yayi ki shirya kije. Amman meye tunaninki akan kuɗin me kike ganin zaki yi wanda kuɗin bazai rushe ba?" To ka soma cin abincin tukunna muna hirar." Yana cin abinci yana santi, ina mishi dariya. In ina tare dashi yaye mun dukkannun damuwata yake yi. In ina farin ciki mancewa nake yi ina da damuww ma a rayuwa. Gida nake so in siya ko me ɗaki biyu ne a zuba mun haya. Kasan ina da gidan dana siya a kusa da gidan Uwani, da ƴan haya ma a ciki. To ko ta kusa dasu na kuma samu sai in siya, ko kuma in sai fili" Saida ya cika tsokar nama a bakinshi yace. "Allah sarki bansan kina da gida a Kano ba yaushe kika siya?" Bayan aurenmu. Lokacin dana shiga kano A wannan lokacin Uwani taimun tayin wajen saina siya" Kai ya girgiza yace. "To ki sake siyan gidan ko filin kadarace babba musamman dake a birni ne, ba kamar ƙauye ba. Ga kayan miya na siyo miki. Na fita yau da ƙafar dama. Na samu gadi a gidan wani Alhaji a Girei. Daga takwas na safe zuwa shidan yamma zan dinga tafiya. Akwai wanda yake yin na kwana. Duk da nima yace inta kama zan dinga kwanan. Nera dubu huɗu a wata" Nan na shiga murna tare da yi mishi adda'a. Da ƙyar naci naman kazannan ya zauna a cikina. Da safe da nayi dumame kuma sai naji inaso naci da yawa. Da Yaya Hamma zai fita na zari dubu Hamsin na miƙa mishi a hannunshi. Ya kalli kuɗin ya dubeni yace. "Me za'ayi miki dashi?" Nakane na baka kayi noma dashi. Dan girman Allah kar kace mun ba zaka karɓa ba. Dan girman Allah Yaya Hamma" Murmushi yayi yace. "Nagode Allah yayi miki albarka" Ameen ko kai fa. Gobe ance in koma asibiti akwai gwaji da zasu sake yi mun. Nasan inka koma ɗakin uwargidanka bazan ganka ta daɗi ba." Dariya yayi tare da girgiza kanshi yace. "Allah ya nuna mana goben lafiya. Sai mu fita tare ai, ni in wuce aiki ke ki wuce asibiti." Hakan kuwa akayi Bakwai ma mun fice a gidan, har bakin asibiti ya rakani, ya wuce wajen aikinshi. Da naga ya ƙule na fito nayo babban titi na hau mota zuwa gari. Allahu Akbar a babban asibitin ma magana ɗaya ce anyi duk gwaje_gwaje, da hoto, da sikainin amman basu ga komai ba. A zahiri ga ciki sun shaida kuma yana motsi, amman a awo babu ciki babu dalilinshi. Tunda uwata tai sanadin zuwana duniya ban taɓa ji ko ganin abun almara irin wannan ba. Halin dana shiga ya wuce gaban misalin da za'a musalta har ƙwaƙwalwar mai karatu ta ɗauka. Ku kwatanta da kanku, in kece wanne irin ruɗu zaki shiga? To irinshi na shiga nima. Gaga_gaga na dawo gida. Na ja bakina nayi gum babu wanda yasan halin da nake ciki. Ai saina dena bacci, nice sallar dare, nice sadaka. Ko aikin girki nake bana rabo da ambaton Allah. Salatin annabi kuwa sai inyi a rana fin dubu biyu. Da sati ya cika na shirya kayana a akwati na fito naima matan gida sallamar zanje ganin gida. Da ƴar tsarabata a buhu harda nono a jarka, da man shanu duka dai wata tsaraba data dace. Yaya Hamma bai bar tasha ba har saida motarmu ta bar tashar. Ko dana juya baya ina hangoshi ta tangaran ɗin motar yana ma motarmu odabo. Wasu siraran hawayene suka sulalo a kumatuna, a hankali na lumshe idanuna, inata tunano abubbuwan da sukaita faruwa, lallai in haka kishiya take irin hama kishiya bala'ice, masifa ce. Hama ta wargaza mun dukkannin farin cikina, ta hanani sakewa da masoyina sam. Bata ƙaunar a zauna lafiya, in bata zageni, ko taci mun zarafi ba bata samun kwanciyar hankali. Amman ina tausayin ranar da zata soma girbe abinda ta shuka, ranar da zata zama abun tausayi. Dan ƙarshen mai biye_biyen bokaye ba ƙarshe bane me kyau. Macen data mutu akan wannan Gwadaben bata ba shiga aljanna, ba faɗata bace faɗar Allah subhanahu wata'ala ne. ( Jan kunne. Yake ƴar uwata ki sani bin bokaye shirkace. Allah baya gafartama wanda ya mutu yana shirka, kuma babu shi babu jin ƙamshin aljanna. Shin akan ɗa namiji kike son kai kanki ga halaka, kina mace kina zaluntar ƴar uwarki mace? Mace ta haukata kishiya, ta kashe kishiya, ta kashe yaran kishiya, ko ta kassara rayuwarsu. Sai kace munzo duniyane domun mu tabbata. Da muna tuna Allah, da azabobubshi, da muna tuna juma'ar da bata da ƙarshe, da muna tuna wuta, mu tuna aljanna wallahil azeem wasu abun ba zamu yi ba. Ke kina nan kina tabkama kishiya asiri, wata ƙila rayuwarki ma ba mai tsayi bace kije ki faɗi ki mutu Shikenan kin gama yawo. A duniya ba riba, a lahira ba riba, kizo a banza ki koma a wofi. Allah ya ƙara tsare imaninmu ameen) Bayan la'asar muka shiga kano Shigata kano ya famamun ciwukan da har abada ba zasu warke a rayuwata ba. Allah sarki Gwadabe alkhairin Allah ya kai muku tare da yarana a duk inda kuke. Allah ya wadataka ya horema samun macen data kere Iyabo ta kuma" Ni dai kai tsaye gidan Tabalbalin na wuce, nafiso saina gama da harkar asibiti kafin inje gida, kwana biyu rak zanyi a gida in koma. A shago na tadda Uwani tanata cinikayya da mata, ta buɗe dilar kayan jirarirai. Ga Hafizu a cikin shagon yanata rataye wasu kayayyaki a hanga. Shagon an sake gyarashi yayi kyau har doguwar kujera aka saka an sake yawan kantocin, an yi sabon fenti. Acaɓana na ajjiyeni a bakin shagon Hafizu ya iso ya sauke mun buhun kayana, da fantimoti na. "Alaja kece a tafe, maraba" Cewar Hafizu. Murmushi na kakaro nace. Wallahi nice Hafizu nace mutuniyar kwana biyu shiru ni bari in leko. An wuni lafiya ya Amarya da yarinyarta ko yarone?" Baki ya washe. "Duk kowa yana lafiya, ai tama haihu jiya Wallahi an samu Uwani" Baki na kuma washewa. Saida na sallami mai acaɓa nace. Ah ka kyauta. Uwani muka samu, wannan yarinya kace mafaɗaciyace" Tare muka shiga shagon na Uwani, ta ko haɗe rai tamau. Ni nasan bazai wuce akan sunanta da akasa bane, ga cikinta ya fito sosai itama. "Iyabo maraba. Jiya fa nayi mafarkinki kuma wallahi marar daɗi harma nayi sadakar ƙosai mai zafi. Ga waje ki zauna a karɓo miki lemo" Waje ta nuna mun na zauna. Ta ba Hafizu kuɗi ya siyo mun lemo da sakwara. Hmmm Uwani damuwoyi sun yi mun yawa a kannan nawa. Ina tsoron kar in faɗi in mutu mutuwar farar ɗaya. A baya matsalata uwar mijice, sai facaloli. A yanzu matsalata Hama ce, haɗa miji da mace mai asiri bala,ine. Ni wallahi har gara in haɗa miji da makira. Ita duka biyu ta haɗa Uwani. Jibi ga ciki a jikina ga motsi, kuma yana girma. Amman gwajin duniya Uwani likitoci basu ga wannan ciki ba wai babu komai fa a cikin. Kaina ya ɗaure, bacci wannan bana iyawa. Banda bala'e_ bala'en daketa sauka akan dukiyata. To ta faru ma ta ƙare tunda yanzu komai nawa ya ƙare tas" Hawaye na sharce bayan na ƙarashe maganata. Uwani kuwa kasaƙe tayi tana kallona kawai. "Iyabo na shiga uku. Wannan tashin hankali har ina. Babu ciki likitoci basu ga cikin ba kikace. To mijin naki wanne mataki ya ɗauka akan hakan? Kinga jikina rawa yake yi Iyabo" Hamma baisan abinda ake ciki ba sam. Na ɓoye mishi Uwani kar kiso ganin