← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 72

Sashe 41

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 9 min read

MARAÆŠI
Tare suka faÉ—i rakwatsam a cikin bokatai. Sabitu yana kan burgujejen tumbin Yaya Tasi'u.
Hadiza kuma duk zafin dukan da Sabitu yayi mata bai hanata yima Gwadabe dariyar mugunta ba. Data kalleshi a tsakiyar kwallaye tsamo sai ta kuma tuntsurewa da dariya. Shi kuma kunya duk ta lulluɓeshi ji yake inama ƙasa ta tsage ya faɗa ko ya huta. Haka ya yunƙura ya bi bayan su Auwala ya bar Hadiza a ƙasa tana dariyarshi.
Da sauri Sabitu ya É—aga Yaya Tasi'u. Sai da Mammada ya taimaka ma Yaya Tasi'u kafin ya iya tashi abinka da mai jiki.
"Meke faruwa, duk me ya kawo wannan rikicin?"
Yaya Tasi'u ya tambaya yana zazzare idanu. Hadiza ce ta fito ta bashi labarin sale_salin rikicin, da zuwa zaneta ta yayi har É—aki"
"Bazan lamunci wannan iskancinba. Rashin darajar matarka yayi yawa da kowa faÉ—a take yi. Ka sani duk ranar da matarka ta sake takalo rigima irin wannan a gidannan to daga kai har ita ba zaku ji daÉ—i ba. Akanme kuma zaka bi Hadiza har É—akinta ka daketa sabida matarka, kuma shima Gwadabe har ka tureshi. Mace na nema ta mayar dakai sususu shashan banza."
Nan Yaya Tasi'u yaita ruwan faÉ—a yana hargagi.
"Duk kuje ku kwanta. Banason jin wannan maganar a cikin gida a kiyaye lafiyar malam. Zan saɓama duk wanda ya shigar da labarin gida har yaje kunnen malam. Gwadabe kayi haƙuri. Kema Hadiza kiyi haƙuri, kuma ki kiyaye kinsan Sabitu dashi da matarshi duk ƴan hau ne tuburarrune"
Nan Yaya Tasi'u ya kashe kes É—in, kowa ya shige É—akinshi.
Ko washe gari Gwadabe bai leƙa ɗakin Hadiza ba balle yaga yata kwana, kuma ya gani ko Sabitu yayi mata rauni.
Itama da damuwar abu biyu ta kwana. Damuwar rashin haɗin kan gidansu, da damuwar maganganun matar Sabitu. Waɗannan abu biyu su taita tubka a kansu tana warwara. Ta wayi gari da baƙin cikin fishin da Gwadabe yake yi da'ita wanda a yanzu tayi imani Shafa tasan fishi yake yi da'ita.
Yau monday dukkansu ficewa wajen aiki suka yi
Hadiza na dawowa ta ɗaura farfesun naman kan rago data siyo. Ta jiƙa shinkafar tuwonta dan lafiyayyar masa take so tayi musu suci da romon ganda. Da ɗan dama ta jiƙa shinkafar dan tana son ta miƙa ma Malam shima tasan yana son waina.
Sai ta shiga aikin ƙalƙale ɗakinta
A zahiri Hadiza irin matannanne da zaku ga komai na ɗakinsu ƙal filin tsakar ɗakinsu sai kaga kamar ba'a takawa. Badai kaga datti, ko ƙura ko ƙasaba. Komai kuma yana zaune a muhallinshi. Shafa na da nata irin tsabtar amman ba irin na Hadiza bane, dan irin su Hadiza har cewa dasu akeyi masu aljanun tsabta, in tsabta tana yawa to tasu tayi yawa ma. Data gama ƙalƙale dakinta ta fito ta shiga gyaran kitchen. Shafa na barandar ɗakinta a zaune tana wasa da Abba sai dariya yake yi. Daga haka sai Hadiza ta jiyo kakarin aman Shafa a bayan gida.
Da sauri ta iso ƙofar bayan gidan tana tambayarta me taci, ko dama bata da lafiyane?
A galabaice ta fito ta zauna.
"Lafiyata ƙalau Yaya, kuma ni banci wani abu da zai tayar mun da zuchiya ba. Tun safe nake jin jikina wani iri haka dai. Sai jiri da nai ta ɗan ji a wajen aiki. Amman inaga gajiyar hanya ce.
Shiru Hadiza tayi tana karantar yanayinta. A cikin zuchiyarta tace
"Shafa dai ƙarfi da yaji itace uwargidan Gwadabe. Ni dai nawa uwargidan sunane. To mi ya rage, ta haifi ɗa namiji gashi babba. Yanzu daga dawowarmu har Gwadabe ya ɗirka mata wani cikin zata kuma rigani haihuwa, ni shikenan na zama ƴar kallo. A zahiri kuma Hadiza tace.
"Bazai wuce gajiyar ba. To Allah ya ƙara sauki. Bara inje gida zan aika almajiran malam sui mun markaɗe inna gama gyaran gidana" Shafa tace.
"To sai kin dawo. Ni kam banji duriyar ummi ba tunda kuka dawo ko kukanta ban jiyo ba?"
"Ummi iyayen rigima tanata bacci. Yanzu sai dare yayi mu ta hanamu baccin " murmushi kawai Shafa tayi. Hadiza ta ƙarashe gyaran kitchen ta kwanke banɗakinta, ta ɗauro alwala. Sai da tayi salla kana ta fice ta bar ganda akan gawayi a hankali gawayin yake ci babu yawa tasan ƙila ma mutuwa zaiyi nanda ɗan wani lokacin. Hadiza dai harta gama tuyar masarnan tana ta aikin tunani duk ta shiga damuwa. A sanyaye ta miƙa ma matan yayunta masa, tasa mayafi ta kai ma Baba Fhatsima tace ta ba Malam.
Zuwa taran dare saiga Gwadabe ya shigo. A lokacin tana tsaye taci kwalliya da riga da wando, ga kanta yasha kitso. Ummi na bayanta tana jijjigata sai ƙananan kuka take yi.
"Sannu da zuwa" Ta faɗa tare da karɓar ledojin hannunshi ta ajjiye a gefe.
Akan daddumar data jera kulolin abinci da duk abun buƙata ya zauna.
"Yauwa. Meya sameta ta hanaki zama" dukkansu babu yabo babu fallasa a fuskokinsu.
"Rigimace kawai" Murmushi yayi yace
"Kuntota, kije ki kirawo Shafa muci abinci yau a mugun gajiye nake sosai" Umarninshi tabi ta kunto Æ´ar ta bashi, taje ta kirawo Shafa suka tawo tare.
"Sannu da dawowa" Sai ya washe bakinshi yace.
"Yauwa Shafa ya gidan, ina Abba?" Hadiza tana zuba abinci tana kallon yadda Gwadabe yake mata fara'a tana jin ciwo.
"Bacci yake yi, yana kan kujera a falo"
Tana faɗar haka zuruf ya miƙe ya ajjiye ummu akan kujera ya fice. Hadiza ta kalli ummi data canyara kuka, ta dubi Shafa taji wani abu ya riƙe mata maƙonlatonta. Sai ga gwadabe da Abba a kafaɗarshi. Hadiza ta ɗauki ƴarta ta goya ranta ya bala'in ɓaci sai taji abincin ya fitar mata ma aka.
Allah ya taimaketa tana goya yarinyar sai tayi bacci. Suna tsaka da cin abinci sai Shafa ta fita a guje amai yazo mata. Da sauri gwadawa ya bita da Abba a hannunshi. Hawaye suka zubo ma Hadiza a kumatunta ta yi maza ta share hawayen ta rurrufe kwanukan abincin ta wanke hannunta ta shigewarta ɗaki tayi kwanciyar rub da ciki ummi na bayanta. Tuƙuƙin kishi zai murɗa mata yake yi. Gwadabe yafi awa guda kafin ya shigo.
"Hadiza daure ki É—an dafa ma Shafa tea sai ki haÉ—a da balango a cikin ledar dana shigo da'ita in kai mata"
Namiji tuwon ƙaya miyar allura
Tean ta haÉ—a ta kawo mishi da naman ita bata rabo da ruwan zafi a filas, nanma saida yafi minti talatin kafin ya dawo.
Ya tarar Hadiza ta kunce ummi ta mata shinfiÉ—a itama tana kwance tayi shiru tana zubar da hawaye. Kwanciya Gwadabe yayi a kusa da'ita ya jawota jikinshi ya haÉ—a bakinsu waje guda. Daga nan labarin ya canja salo. Tsakanin mata da miji sai Allah. A daren Gwadabe ya wanke laifukanshi. Sukai baccinsu mai daÉ—i, da asuba ma bayan ya dawo masallaci ya jawota jikinshi suka koma ruwa.
Shikenan fa maganar ta ƙare.
Hadiza sai ta dena ƙorafi sam, duk abinda ta gani saidai ta cinye damuwar abun na cin ƙasan ruhinta.
Laulayin dai ciki ya tabbata bil haƙƙi akan Shafa cikinne dai da'ita. Cikin irin mai shegen laulayinnanne Anty Badi'a sun dawo daga tafiya suka tarar da Shafa babu yadda take. Ko me taci amai take yi farfesun kifi ne kaɗai take ci ya zauna mata. Tama dena girki kwata_kwata farfesun kifinma indai ita tayi bata iya ci, sai Hadiza ta ɗauke mata.
Shi kuma goga gwadabe fa ganin canjin da aka samu a wajen Hadiza sai ya zamana ya ƙara sonta, ya ƙara zagewa wajen kulawa da'ita. Kuma ya mata godiya sosai akan canjawar da tayi dan yaji daɗi gaya.
Ita kuma matar Mammada Allah bai bata haihuwarba ita kaɗaice a cikin matan gidan bata haihu ba, duk matan gidan goyo suke yi, sai ita kaɗai da ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Ga Shafa ta samu ciki tana jin yayi wuri dama bata samu ba. Ga matar Mammada tana dama itace Shafa. Haka Allah dama yake yin ikonshi.
A cikin gidan malam ta ɓangaren matanshi yawan faɗa da yawan rikici yayi sanyi sosai. Sai dai fa ko wacce ta ciki na ciki. Sunyi haƙurine sabida yanayin jikin Malam, da kuma sakin Baba Suwaiba da yayi. Wannan yasa Baba Asshi ta sassauta faɗanta dama itake haddasa yawanci fitintinun gidan. Tayi zuchiyar dena zuwa turakar Malam ma a tunaninta zaita binta yana rawar ƙafa akanta. Irin yadda yaima Baba Fhatsima data dena zuwa turaka, sai taga saɓanin haka. Ba shiri ta watsar ta koma akaci gaba da rabon kwana da'ita. Matar Malam kuma ciki gareta tana fama da laulayi, yau an bata gado a asibiti, gobe tana gida, yau amai, gobe yawu dai. Yaran matan da akaima aure, Malam ya kafa musu dokar dena zuwa mishi gida barkatai, sai matsalolin cikin gidan ya ragu. Sai matsalolin can gidan wanda wannan Yaya Tasi'u da Yaya Jamilu ne akai. Malam yama dena sanin meke faruwa.
Ta ɓangaren Baba Fhatsima kuma ta roƙi Yaya Tasi'u ne akan ya auri Balaraba tunda ta lura har gobe suna son junansu. Ta bashi kwana biyu yayi tunani. Ya dawo bayan kwana biyun yace mata ya amince.
To a halin yanzu hidimar haɗa kayan akwati akeyi. Harma an fitar da lifaran (ankon biki) Anty Badi'a ko da Yaya Tasi'u ya tareta da maganar ƙarin auren. Sai tayi mishi fatan alkhairi tare da yi musu adda'ar zaman lafiya. Jin daɗin hakanne yasa ya biya mata Umara. Ta tafi da kwana ɗaya aka ɗaura auren. Bikin daya tara ƴan uwa da abokan arziki. Amarya Balaraba ta tare a ɗakinta, akaita amarci. Saida suka cinye amarcinsu kafin Anti Badi'a ta dawo. Kafin ta dawo tazo ta tarar Yaya Tasi'u ya sake mata komai na ɗakinta, tayi mishi godiya, ta kuma rungumi Balaraba suke zaune lafiya, sai ɗan abinda ba'a rasawa. Wannan dalilin ya ƙara ɗaga daraja, girma, da kimar Anti Badi'a a wajen iyayen Yaya Tasi'u dama ƙannenshi ƴan ɗakinsu.
Ta bangaren matan Gwadabe kuma rayuwar tana ta buɗe musu, Gwadabe yana ta samun ciniki. Kwatsam ranar wata Juma'a sai ga kiran Zulƙi yana sanar da Gwadabe akwai taron manya da za'ayi a garin Abuja ranar monday. Yana so gobe yaje Takai ya sameshi sai su wuce taron tare ya tafi da maganinshi.
Ai kuwa hakan akayi shadda kala biyu Gwadabe ya ɗinka, ya sai takalmi mai tsada da hula. Ya ɗauki akwatin magungunan shi yaima matanshi sallama sai Takai. Kwananshi ɗaya a wajen Bara'u ranar Lahadi suka shiga Abuja. Washe gari Gwadabe yabi Zulƙi zuwa wajen taron. Kamar wata ƴar liyaface aka haɗa na Gwamnoni, da ƴan majalisu, da Chiyamomi, harda sarakuna.
Alkhairi da Gwadabe ya samu a wajen wannan taron bana wasa bane. Saida ya saida maganinshi tas ya dafe kuɗaɗenshi. Suka sake kwana a Abuja. Washe gari Gwadabe ya dawo Nijar, Zulƙi ya wuce Takai.
Cikin dare Gwadabe ya shiga gida, a É—akin Hadiza yake harta yi bacci sai gashi. Yayo musu tsarabar sutura, da kayan kwalliya da turare. Kuma yai musu ihisani da kuÉ—i mai É—an tsoka. Sukaita shi mishi albarka. Shafa kuma ya bata kuÉ—in siyan kayan jariri ta soma ajjiyewa duk da cikin watanshi ukune kawai, ganin ya samu kuÉ—ine yake ganin bari a soma ragewar dai, tunda shi É—inne dai zai siya.
Chapter 41 · 0% Book details