← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 72

Sashe 35

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ɗanta shikenan ni da Ummi ya juya mana baya. Sai fishi yake yi, kuma fa har gidan tsohuwar Matarshi a Kano saida abokinshi ya rakashi suka je. Ni fifikon da yake nuna mun ya isheni" Baba Fhatsima tayi shiru cikin karantar yanayinta tace. "Hmm Hadiza ho. Wallahi in kika yi saken da Gwadabe yaga wallanki to wallahi kin shiga uku zaman bazai miki daɗi ba. Hala kin isheshi da ƙorafine, ko kuma wata damuwar ke damun ranshi har kika ga ya canja. Ko kin tambayeshi dalilin canjin nashi?" Hadiza ta girgiza kai halamar a'a" "Kinji irin shashancin naku ai yaran yanzu. Yanke hukunci ba naku bane, zaunar da miji zakiyi cikin kulawa da nuna damuwa da sannu saiya warware miki cikinshi. Da haka mace take zama sirrin mijinta abokiyar shawararshi. In kikayi sake Shafa ta samu wannan kambun bake ba. To abubbuwa da dama zasuita faruwa da mijinki, ƙalilan daga cikine zaki iya ji. Masu yawan yaci ya birne da abokiyar zamanki. Hadiza namiji wawane, kuma sauƙin sarrafawa garesu Wallahi. Abinda yasa na kira namiji da wawa shine. Shifa kulawa da tarairaya, sai ladabi da biyayya,iya girki, iya kwalliya, tsabta iya ɗauke lalurarsa. Shine fa namijin kuma shine zaman auren. Ana mallakar miji da kissoshi sunfu kala saba'in bari in jero miki kaɗan a cikinsu. Akwai kirsar magana Akwai kirsar tafiya a gaban miji, ko kishiya Akwai kirsar rauni, yawan kuka Akwai ta shagwaba Akwai kirsar nuna ma miji ke kullum bai isarki a shinfiɗa Akwai kirsar shimfiɗa Akwai kirsar sa sutura Akwai kirsar iya girki Akwai kirsar ciyar da miji abinci a baki Akwai kirsar yima miji wanka Kirsoshin suna da yawa, ko wanne guda ɗaya kika ɗauka zaki zama ta daban. Kuma zaki zauna daram a zuchiyar mijinki. Shine zakiji yana faɗin alkhairin Allah ya kaima wance. A gaban matarshi zai iya yabon matar data mallakeshi da Tata kirsar namiji ba kunya gareshi ba. Ko kiji yana da wancece da yanzu tayi mun kaza, ko tace kaza. Namiji ya barki da sakakken baki. Su basa raina sauyi, ko jin daɗi duk ƙanƙantarshi. Abubuwa da dama mun ɗauke kanmu akai bamu ɗaukeshi da mahimmanci ba, shigowar boko duk ya wanke muku kanku kun dena biyayya. Mu a zamaninmu a wani gari da Malam ya taɓa kaini muka zauna lokacin sana'ar Malam sai da gishiri da manda ne. To gidan da muke haya akwai wata Fatu bafulatanar Gombe ce. Akan rashin sa ruwa a buta mijinta ya saketa sai garinsu ta koma. To wani akan shara zai iya rabuwa da mace. Wani duk waɗannan ƙanunun abubbuwan harma da manyan bai dameshi ba babu ruwanshi. Amman kinsan babban abinda maza suka wasa shine tsananin kishi, zargi, ƙorafi, bin diddiginsu dan ganin laifinsu, ƙazanta. Waɗannan abubuwan dana jero duk halinki ne banda ƙazantar shi yai silar mutuwar aurenki na fari. Ke ba zaki zama mai kawaiciba, ki gani ƙiri_ƙiri ki nuna baki gani ba. Kiji ki toshe kunnenki. Dole sai anayi ana haɗawa da halin ko in kula, koda hakan zai dameki. Hadiza ki kiyaye abinda zai maisheki bora, Gwadabe fa yana haƙuri dake" Hadiza taci kukanta mai isarta. Baba Fhatsima batai yunƙurin hanata ba har saida tai shiru dan kanta kana tace. "Sai ki kiyaye. In ranar kwananki ya zago saiki bashi haƙuri a bisa kusakuranki da kinfi kowa saninsu. Kuma cikin lallami ki doki cikinshi ya baki labarin matsalarshi. Ke kuma saiki magance mishi damuwar. Inta adda'ace kice zaki taya shi da adda'a. In kuma na shawarane ki bashi shawara, inma na nasihane ki mishi. To zaki ga ko farin cikin ya shiga kece ta farko. Ke namiji sauƙin kai gareshi in baki kwaɓeshi ba sai kiga har asirin kishiyarki ya fasa miki shi babu ruwanshi. Tashi ki koma ɓarayinku" Sallamar Shafa ce ta katse musu hirarsu. Baba Fhatsima ma ce ta amsa mata ta shigo suka gaggaisa. "Malam baya nanne Baba? Shafa ta tambaya" "Bayanan sun tafi taron biki cikin Zinder sai da yamma zai dawo. Ya kika baro mutun Takai dana Habuja?" Murmushi Shafa tayi tace. "Duk suna lafiya Baba. Ga wannan turmin zanine wana yace in kawo miki" Ta miƙa ma Baba wannan turmin zani holan. Baba Fhatsima taita godiya. Anan dai ta tafi ta bar Hadiza dan saida taci ragowar zogalen da Yaya Tasi'u yaci ya rage, ta kora da fura kana ta tafi. Tana komawa gidan ta samu suna abinda suka saba. Wannan karon da matar Mammada da matar Sabitu ne. Dan kaf gidan bada wanda matar Sabitu batai faɗaba shima ɗaure mata baya yake yi inya dawo ta faɗa mishi ƙarya da gaskiya saiya fito tsakar gida da gajeren wando bako riga yaita fitsara. Har Hadiza ta wuce ganin da matar wanta ake rikicin saita tanka. "Haba matar Mammada wannan ai ba halinki bane kiyi haƙuri ki rabu da'ita sharrinta zai koma kanta" Tsautsayi da ba'a saka mishi rana. Buɗar bakin matar Sabitu sai tace. "Ai sharri a jininku yake yawo. Tunda mahaifiyarki ta kakame komai gani take ku kaɗaine ƴaƴa. Kamar yadda Mammada ke da gado, haka Sabitu yake dashi shima. Ina ruwanki da wannan faɗan?" Hadiza tayi kasaƙe tana jin ikon Allah ga Shafa tana tsaye tana jin duk abinda ke faruwa. Hadiza tana juyowa ta cukume rigar Matar Sabitu dambe saiya kaure. To Hadiza ƙaƙƙarface sosai, nan ta guggurje bakin matar Sabitu. Duk da itama ta taɓuka tunda ta gwara kan Hadiza da bango har saida wajen ya fashe. "Shegiya mai haƙoran mayu" A guje Hadiza ta bita Shafa tayi carab ita da matar Auwala suka riƙeta To dama Hadiza kunga a cikin yanayin da dama take wuni tayi tana zage_zage da mita a tsakar gida, tana faɗin. "Daidai nake da ko wacce shegiya a cikin gidannan " matar Sabitu ta leƙo tace. "Harma kina da bakin magana ke da saida aka roƙi Gwadabe ya taimaka ya aureki. Shi yasa aka haɗa auren da Shafa dan itace zaɓin ranshi. Wooo anji kunya anyi bandaro an kasa auruwa" Hadiza sai da tayi ɗan daka ce bata kula matar Sabitu ba, dan ta ɓarar mata da gari a gaban kishiya. Tunda ta shige ɗaki shikenan tayi ƙus. Shafa kuma tayi dariya ta shige ɗakinta itama. To ko da daddare da Gwadabe ya dawo bai fa leƙo Hadiza ba. Tsarabar lemu da ayaba da balangu ya aiko Shafa ta kawo mata. Tana zaune sai jujjuya maganar matar Sabitu take. Gani take kamar gaskiya ne abinda ta faɗa akan aurenta da Gwadabe Fitar Shafa ba daɗewa sai ga Sabitu ya buɗe labulen Hadiza rai a ɓace harda bulala fa. Batai tsammaniba ya shigo ya soma carbaɗa mata. Gwadabe yana cin abinci ya jiyo karan tabka da ihun Hadiza ba shiri ya fito a fusace. Ganin yadda bil haƙƙi Sabitu ke dukan Hadiza Gwadabe yayi kukan kura ya dira a wuyanshi. To gaskiya Gwadabe ba ma'abocin faɗa bane, kuma ko a sifa Sabitu ya fishi jikin ƙarfi zuga Gwadabe yayi da ƙasa yaje ya shure jeren kwallayen Hadiza duk murafen suka rikito mishi. Wannan ƙaran ɓarin kwanukanne ya fito da su Mammada. Auwala ya tari Sabitu ya dinga aika mishi naushi Babu shiri Sabitu ya fito a ɗakin Hadiza da gudu. Ya bangaji Yaya Tasi'u da shima hayaniyar ce ta fito dashi suka faɗi tim a ƙasa tare. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Chapter 35 · 0% Book details