Sashe 19
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kari kuma ta tafi dana Dada bayan taci nata. Yafendo ma na miƙa mata nata. Nan na shiga hidimar tarbar miji, ina jiyo hayaniyar dawowar su Baɗɗo masu tuwon dare, sai su kai goman dare basu gama tuwo ba. Takwas dai-dai Yaya Hamma ya shigo dan naji muryarshi abun mamaki sai naga har minti talatin bashi ba dalilinshi, ni gashi naci kwalliya kuma naci alwashin saina nuna ma Hama shiru_shiru ba tsoro bane. Ai saina ɗauki mayafina na yafa na fice. Hama na kitchen nayi shigewata ɗakinta ga zahiri yana ciki ga takalmin robanshi nan a ƙofar ɗakin. Cusa kai nayi da sallamar da buɗe labulen a tare. Yana zaune babu riga daga shi sai dogon wando, ba laifi yau ɗakin ba a hargitse yake ba anyi mai gyara buja_buja. Yana riƙe da yarinya yana mata waƙa da fullanci. "Jabu irin wannan ƙyalli da kikeyi kamar wata ɗan dare sha biyu?" Wata basarakiyar murmushi nayi mishi na nemi daf dashi na zauna jikina da nashi na gugar juna, na wani narke mishi duk na sukurkutashi da kallo masu fassararo. Da shawaba nace. Naji shigowarka tun ɗazu sai naji ka shiru. Nazo na ganka a tuɓe ka manta kwananane?" Idanunshi har sun ƙanƙance, hannuna ya kama ya ɗan matse a nashi ni dashi du muka lumshe idanu na sake shigewa jikinshi. Yayi daidai da shigowar Hama da tiranta na silba. Ba shiri ta saki tiran komai ya watse ji kukeyi rakwacam. Tasha kwalliyarta harda janbaki. Atampar jikinta ta amsheta ban ɓoye muku ba Hama a fulaninma ita kyakkyawace wallahi saida gabana ya faɗi data shigo dan koni tayi mun kyau, damma dinkin yayi mugun yi mata yawa rigace a mugun ɗangale har cikinta ana gani wuyan rigar kuwa baya ko zama. Amman dake atampar ja ce sai ta haska. "Me zan gani wannan Hamma. Baka sanar mata yau kwanana bane da zata ci kwalliya ta shigo mun ɗaki sabida neman fitina. Da nice nayi haka ace ban kyauta ba. Jibi yadda ta matseka har kana riƙe hannunta sabida rashin kunya" Da fullanci take du wannan maganar, tanayi tana hawa tana sauka, dan masifa har hunhuna hancinta yake yi. "Shigowarta kenan kema kika shigo. Meye laifi danta shigo ɗakinki, da kike maganar ta zauna kusana na riƙe hannunta. Matatace halaliyata ai kin sani" ya faɗa mata haka, ai saita sake hawa tace. "Sai ku bari kuje ku karata ranar girkinta bawai ranar girkina tazo har ɗakina ta nuna mun ta fini iya kwanciyar Aure ba. In banda Hamma kana da kamata kyakkyawa wanke hannu ka taɓa me yasa ka auro Jabu oho.." "Kiyi mun shiru baki da hankaline" Ya daka mata tsawa, ni kuma nayi murmushi na miƙe. Hama gadararta kyaune, ni kuma ina gadara da ƙirar da Allah yaimun musamman mazaunaina wanda nasan yana rikita kan maza, kuma shi kanshi Hamman mazaunan suna daga cikin abinda suka fi fisgarshi game dani. Ba yabon kaiba ina hamdala da irin dirin da Allah ya bani, ko a fuskar ni ba mummuna bace, na yarda a fuska Hama ta kereni ovar, amman baya ga haka na fita kayan alatun more rayuwa sau dubun dubata. Saida na yi taku na kaɗa mazaunaina sosai kana na juyo. Yaya Hamma ina jiranka karka daɗe. Bazawara kwana uku take dashi, a iyakar sanina kwananka biyu a ɗakina. Bazan iya sarayar da kwanana ba, dan na fita buƙatar kwanan" Ina dasa aya nasa kai na fice. Wane tudu wane gangare sai ga Yaya Hamma ya biyoni. A wannan daren na wanke mishi kai tas, abubbuwa da yawa sun faru masu tsaiwa daram a zuchiyoyi, muka wayi gari cikin farin ciki da shaƙuwa a tsakankaninmu, na jefa Yaya Hamma a duniyar da nayi imanin bai santa ba kafin ni. Wannan saiya zama matattakalar ƙara buɗe sabon faifayin sona a zuchiyar Yaya Hamma, yana ji dani sosai, wallahi baya son ganina a damuwa ko ɓacin rai. Tun asuba Hama ta wayi gari da dukan yara da zaginsu a nufinta na hucewa a kansu. Ina jiyota Yafendo na mata faɗa, shima uban gayyar bayan ya gama shan soyayyarshi daya fita ina jiyoshi yana mata faɗa. Ni ko a safiyar ranarma bata ganni ba har ta gama dafa madara suka kama hanyar tallah. Bayan na gama aikin shara da wanke bayi dana ɗaurama kaina , na dafa abinci mai yawa, na kaima Yafendo nata. Yafendo zanje gida, yau nake son buɗe kayana na siyarwa. Daga nan duk zan leƙa maƙota in sanar musu" Murmushi tayi tace. "Ƴar albarka. Yi tafiyarki zan shiga da kaina duk in sanar musu zaki kuwa kwanɗa ciniki mu nan mata suna da kuɗaɗensu babu laifi. Bari mu fita tare" Abun sha'awa a tare muka fita, ni na tafi gida ita kuma ta dinga zagaye gidajen wannan gunduma tanai mun tallah. Ina isa gida na tarar da Dada da Kari a tsakar gida, Dada na kwance Kari na wanke_wanke. Ganin Dada na hutawa shine farin cikina ko iya haka burina ya gama cika sanadiyyata Ƙaddararren aurenta ya mutu, sannan sanadiyyata ta dena yawon wahalar talla itama ta soma morar haihuwa ai bata ga komai ba in sha Allah saina biya mata makka taje kafin rai yai halinshi. Muna haɗa idanu tayi mun murmushi mai kyau. Danma bata sakewa dani kundai san halin fulanin daji. Amman murmushinta shi ya nuna taji daɗin ganina. Gaga_gaga na shiga buɗe kaya na soma da buɗe zannuwan gado. Wasu ƙananan zannuwan gadone masu ɗawisu suna da santsi, na kwasosu da yawa gaskiya sabida suna da sauƙin kuɗi. Masu tsadar ɗan jejjefosu nayi. Dogayen riguna kuwa gaskiya masu kyaune giredi wan baƙaƙe sunfi yawa. Ina kam ciccira rigunan na soma jin sallamar mata Yafendo na ta tawo mun su. Allah cikin ikonshi wannan zannuwan gado sai suka tafi dasu, a ƙauyan kab su basu taɓa ganin irin wannan zannuwan gadon ba. Du mata gomannan da suka zo ganin kaya saida ko wacce ta sai ganin gado nera ɗari dubu ɗaya kuɗinsu. Dogayen rigunan kuma ɗari biyar biyar ko wacce ƙulle da gyalenta. Hayaniyar matannan ita ta jawo mun hankulan matan maƙota gida fa sai ya ɗinke da mata. Alhamdulillah zannuwan gadonnan an kwashesu duk da dogayen rigunanma an jidesu na kama ƴan ƙudaɗena na ɗaure. Wajajen azahar gidan ba kowa, bayan nayi Sallah saina zuba ma Dada abincinta na zuba nawa, wanda yayi ragowa na miƙama Kari da yaranta. Yafendo dama ko zama batai ba rako wannan mata kawai tayi ta koma ta bar yara ƙanana a gida. Zuwa bayan la'asar saina ɗau haramar komawa gida. Na bar riguna ashirin, da zannuwan gado ashirin na danƙa a hannun Kari akan in wasu matan sun shigo siyan kaya saita nuna musu. Na bata doguwar ruga biyu nata da zanin gado. Na ɗan tsinci digayen rigunan da zanin gadon na sa a leda. Naima su Dada sallama na koma gida. Abinci na ɗaura na shiga aikin shara duk da ɗakin a share yake amman so nake in ganshi ƙal_ƙal. Ina gama sharar saiga ƴan tallah sun shigo. Bayan sun nutsa na fitar musu da kaya suka kwashe, har Hama saida ta sai doguwar riga baƙa da zanin gado. Rai a turɓune ta kunce gefen zani ta ƙirgomun kuɗina na dafe. Banyi tunanin zata ko kalli kayan ba, dan dana je wajen nai musu sannu tana wanke_wanke bata ko ɗago kai ta kalleni ba. Jin yadda ake kururuta zannuwan gadonne yasa ta wanke hannunta tazo kashe ƙwarƙwatar idanunta. Da magriba Yusufu yazo ya ɗaukar musu abinci, na haɗa mishi dana Dada. Amaduyal ma da yazo ɗaure shanu saida ya shigo na cika mishi kwano da abinci ya cinye. Ni dai ina yin sallar isha nayi kwanciyata dan nasan yau Hama ba zata barshi yazo ko gaisawa mu yi ba. Ai kuwa wajajen sha ɗayan dare ina bacci naji ya faɗo ɗakin. Da sauri na farka dan tsoro ya bani ma. "Gimbiya har kinyi bacci ba tare da kin sani a idanunki ba? Ni inacan gangar jikinace acan ruhina yana tare dake" Yayi maganar yana shafa fuskata. Lumshe idanu nayi nace Nasan ƴar rigimar matarka ba barinka zata yi kazo ba, kaga shi yasa nayi baccina amman kana ƙasan zuchiyata can ciki" "To da fatan kina lafiya?" Sai alkhairi ya aikin, da fatan ka dawo Lafiya?" Murmushi yayi yace. "Lafiya lau wuni nayi ina tunaninki. Nayi kewarki sosai. Yanzu dai da safe ki shirya zan kaiku gidan ogana matarshi ta haihu gobe suna zaku je mata dan ta dameni da gori" Nan mukai sallama ya fita. Lumshe idanuna nayi bacci mai cike da mafarkai yayi sama dani. Washe gari kamar kullum na gama duk abinda ya dace da sauri dan Yaya Hamma ya turo Hama yace inna gama in samesu a ɗakinta. Kwalliyar leshi nayi fari sol mai kyau da tsada, takalmina da jakata masu ruwan zuma na ɗauko ɗankunne da sarkar gwal na saka, da awarwarona da zobunan zinare, turare mara ƙarfi na fesa a hammatata dan gudun yin warin zufa kunsan mu masu ƙiba gaskiya ba wuya munyi zufa, daga zufa sai warin hammata yanzu saimu gume waje. Shi yasa ko wankana yana ɗaukar lokaci ba laifi dan sai nayi cuɗa da ɗauraya sosai. Zanin gado ɗaya na ɗauka na sa a jakar leda ta ƴan gayu zan kaima mai jego. Tun sasssafe na aiki Amaduyal da yazo kaɗa shanu gida ya kwaso mun kaya na loda a wata babbar jaka. Fitowa nayi tsakar gidan ba kowa, sallama nayi ƙofar ɗakin Hama suka fito muka kama hanya. Babu laifi Hama tayi kyau kunsan farar mace akwai haskawa atampa koddibuwa ce mai ruwan kore da ruwan madara. Sai dai fa mayafi mai ruwan bula ta saka sai takalminta baƙi, da wata cinyayyar jakarta ja abunta. Kuma ita da gaske ta kece raini haka take ji dan taƙu ɗaiɗai take yi. Haka dai muka shiga cikin gari Yaya Hamma ya kaimu gidan oganshi anguwar masu kudi tabkeken gidan sama. Har falon gidan ya shiga damu, yasa masu aiki sukai ma Hajiyar gidan magana. Mace mai karamci da faram_faram sai gata ta fito tana walƙiya. "Ah Hamma masha Allah wannan mata zuƙa zuƙa haka ga siririya ga duma_duma. Bayin Allah sannunku da zuwa kuzo mu shiga ciki" Nan Yaya Hamma yai mana sallama akan da yamma zai zo ya ɗaukemu.