Sashe 3
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ni ko da uwar harara ma ta bini. Ni kuma nayi mata murmushi kawai nasan kishin rashin Hamma ke damun Daso, ba taya Hama kishi ba. Tunda data samu dama itace zata zama kishiyar Haman. "Ga abinci kuci Jabu. Baƙon ya tafi ko?" E Dada ya tafi" Matashin kanta ta ɗan ɗaga ta gefe ta zaro kuɗin da Saleem ya bata ta miƙo mun." "Ki riƙe a hannunki, ni bansan ma nawa bane. Jabu su Yusufu har yanzu basu zo sun dubani ba" Murmushi nayi mata nasa hannu na amshi kuɗin Dada nice na hanasu zuwa, kiyi haƙuri an kusa sallamarmu mu koma gida" Maimakon naga tayi farin ciki. Sai naga saɓanin hakan damuwa ta bayyana a fuskarta. Babu shiri na ƙarasa wajen gadon na zauna a gefe guda. Dadana na siya miki gidan da zaki zauna ki huta ki mori haihuwa kema. Kuma in sha Allah zan zuba miki kayan alatu da zaki more tsufanki. Kulawarki ta dawo hannuna Dada. Su Cubu zasu zauna tare dake, na ɗauke miki nauyin komai Dada. Nasan ƙila tunanin inda zaki zauna kike yi" Hawayene ya gangaro ta gefen kuncinta, sai ta runtse idanunta tace. Ubangiji Allah ya kai haske kabarinka Akintoye. Haƙiƙa kabar baya me kyau. Jabu kamar yadda sanadiyyarki matsalolin rayuwata suka gutsire. Ina roƙa miki Allah Hamma ya zama silar goge miki damuwar rayuwarki. Sannan inaso in faɗa miki kibi Hama a sannu, sannan kibi Daso a sannu. Ɗazu ba bacci nake yi ba duk abinda suka tattauna duk a kunnena. Dansu a kuɗirinsu shine aurenma bazai yiwu ba. Bokaye sosai Hama take bi duk dan a raba soyayyarku. Ke kuma saiki dage da roƙon Allah yai miki tsari da sharrinsu. Nayi imani da Jabu uwar Daso zata san abinnan da Daso tayi zata iya yi mata baki. Dan haka kija bakinki kiyi shiru komai ma yazo ƙarshe daga gobe za'a yita ta ƙare" Hannun Dada na damƙe na lumshe idanuna. Na lura a wannan tafiyar kamar da jarabawar kishiya kuma zan jarabtu na tsallake rijiya da baya akan uwar miji, ga kishiya kuma jama'a tana neman rayuwata. Babu komai Dada, Allah shi ke da iko akan komai. Ki tayani da adda'a nima zan zage damtse. Ki kuma dena kuka Dada, Allah ya jiƙan Baami" Dawowa nayi kusa da Uwani a tabarma. Na zuba ma Dada jallof ɗin shinkafa dasu Daso suka kawo, har zan miƙa mata sai naga kamar yayi kaɗan sai na saƙa cokali zan ƙara mata. Wallahi saiga dunƙulen magani a cure a waje ɗaya bai idasa cakuɗuwaba. Subhanallaah Uwani duba" Na nuna ma Uwani. Haɓa ta kama tare da zaro idanu. "Iyabo wannan ai dunƙulen maganine, hala kishiyarkice ta kawo abincin?" Da kai na amsa mata. Juye abincin nayi na rufe, na jawo kular Karima matar Amaduyal na zuba ma Dada abincin ciki. Shinkafa da miya da kifine. Na miƙa mata na bata ruwa. Na saka mana cokula biyu a cikin kular zamuci dan sabida ƙauyanci a kan shinkafar ta kyaɓo miyar. "Iyabo jikina yayi sanyi tsoron Allah kuma ya kamani. Tofa wata sabuwa inji ɗan caca. Shi kuma wannan auren na lura da kishiya za'a fafata. Nifa duk harkar asiri bana ciki. Ko kishinne nafi son muyi na kirsa duk wacce ta biya allonta saita wanke. Amman tun kafin ki shigo ciki an soma binki da bita da ƙulli?" Ni dai ko magana wannan na kasa yi. Sai cin abincin nake yi. Abincinma sharkab da mai dan masifa sai tea na haɗa mana muke danne man dashi. Wajajen bayan isha Yaya Hamma ya dawo. Leda ya miƙo mun ɗaya cike da tsire, ɗayar kuma lemun kwalba ne montin dew. Dada ta ɗan jima da bacci sabida magungunanta kamar akwai masu saka bacci. "Ni kam me ya haɗaku da Hama da Daso Jabu" Kallonshi nayi, sai na fahimci ranshi a ɗan ɓaceyake sai nace. Babu komai wani abun suka ce maka anyi?" "E Hama tace mun wai kince kinfi ƙarfin kiyi kishi da'ita dakin shigo zaki kaɗata. Maganganu dai marasa daɗi Daso tace har mahaifiyar Hama kika zage tas. Dan Allah meye gaskiyar wannan lamarin?" Kallon kallone ya shiga wanzuwa tsakanina da Uwani. Tab wata sabuwa inji ɗan caca, ni Iyabo gidan da zan faɗa kuma kenan? Ga asiri ga makirci anya kuwa? Uwani ce naji tayi mishi bayanin abinda ya faru. Sai yayi dariya kawai yace. "Kishi ne yake damunta sosai shi yasa ita da Dason suka ƙirƙiri wannan maganar. Amman zan ɗauki mataki akan ita Haman ni na isa da gidana. Jabu ina jiranki a waje domin ki bani amsar tambayoyina" Yana idasa maganarshi ya fice hannunshi riƙe da sandar da ba'a fiye raba bafulatani da'ita musamman ma masu fita kiwo. Idanuna na lumshe kaina sarawa yake yi sosai. Uwani ci namannan bari inje in kashe wutar da kika kunnamun. Inna dawo zamu tattauna matsaloli Uwani" Nan na bar Uwani tana cusa tsire da albass a bakinta. A inda yake kwanciya na sameshi kanshi a ƙasa yana bubbuga sandarshi a ƙasa. Harna zauna bai ɗagoba, ko salllamata yaƙi amsawa lallai ran maza ya ɓaci. Angona masoyina wanda ya zama zaɓina abun begena. Lafiya ka kasa amsa sallamata, ko dai maganganun da Hama tace na faɗa mata ne suke damunka?" Shirune ya biyo baya na daƙiƙu kana ya ɗago idanunshi ya saukesu a kaina. Na kasa karanta haƙiƙatan ɗin abinda ke cikin idanun nashi, na hango kishi, da so mai wuyar fassarawa. Ajjiyar zuchiya na sauke tare da yin ƙasa da idanuna, ina jiyo yadda idanunshi ke yawo a fuskata. "Wallahi Allah ina da mugun kishi akan duk abinda nake so. Wannan dalilin yasa na kusan kashe ɗan uwan Hama a filin shaɗi a lokacin da ya zama daga cikin gwarazan da suka fito neman aurenta. Jabu kafin ki tafi saida na damƙa miki amanar rayuwata nasa kikai mun alƙawarin babu wani ɗa namiji da zaki bashi damar shiga rayuwarki. Kaico ashe ke soyayya kiketa ta yi. Ni kin barni da dakon sanki, kewarki duk ta hanani sukuni, hatta bacci me kyau ina samune duk ranar da nayi mafarkin na aureki jibi yadda na fita hayyacina Matata da abokaina kullum a cikin surutun lalacewata suke. Amman ke ashe mu biyu kika ajjiye a gurbin zuchiyarki, kin ban mamaki sosai Jabu. Meye matsayin Saleem a wajenki, kuma me yazo yi wajenki, Allah yasa ba kukan sonshi kika yi ba?" Shiru nayi kamar ruwa ya cinyeni tunda ya soma maganarshi harya dure. Akwai taushi da zafi cakuɗe da muryar tashi. Yaya Hamma ka yarda dani kai ɗaya tal ne a zuchiyata ban haɗa soyayyarka data kowa ba. Ko uban Ƴaƴana ban soshi irin son da nake yi maka ba. Gaskiya dai ɗaya ce Saleem ya taimakemu a zamanmu na saudiyya. Dan shi yai mana hanya muka dawo Najeriya. Bamu yi soyayya ba, amman ya soni sosai. Dalilin zuwanshi kuma neman aurena yazo yi, kuma na faɗa mishi gaskiyar lamari. Batun kuka kuma ka gafarceni tausayi ya bani ne" Ƙur idanunshi a kaina yana kallona irin kallo mai fassarar ban yarda dake ba. Idanu na lumshe na buɗe a kanshi. Yaya Hamma" Yayi saurin ɗaga mun hannunshi. Yayi magana da wata murya a ciki. "Ya'isa haka dan Allah. Kar kiyi sanadiyyata inje in rataya a wuyanki. Ki koma ciki (🤣🤣) Uwani na jiranki saida safe" Nayi yinƙurin fahimtar dashi tare da rarrashinshi. Amman bai bani wannan damar ba sam. Haka na miƙe jiki da zuchiya babu kuzari na shiga na samu Uwani tana waya. Jagwab na zauna a gefenta ina ambaton Allah. "Lafiya na ganki haka Jabu, an samu tsabanin fahimta da Hamma kenan ko?" Ke dai bari yaƙi fahimtata akan zuwan Saleem Uwani. Amman zan bashi lokaci inya huce zai fahimceni. Ni wallahi komai ya fice mun arai, Hama lamarinta ya kashe mun jiki. Tsorona Allah tsorona hulɗa da mai mu'amala da bokaye Uwani. Wannan wanne irin zama zamuyi kenan, da wanne irin bita da ƙullin zata bini in mijin ya zama namu mu mu biyu?" Uwani ta muskuta kana tace. "Adda'a takobin mumuni, bacci da barin bakinki shiru ba naki bane. Ni a tunanina da ai miki kisan mummuƙe aita gabza miki asirinma baki sani ba. Ai gara kin sani zaki san irin zaman da zaki yi da'ita. Ke dai ki zama me lura sosai. Kar ki sake kici duk abinda zai fito daga hannunta shine kawai tunda kin nace. Abinne Allah cuta Allah magani, tunda ko kai akazo aka tarar bakasan irin wacce za'a kwaso maka ba. In kinga irin yadda amaryar Hafizu take tata ɗiban albarka irin nasu na ƴan ƙauye Iyabo zaki riƙe baki. Kinsan akace shege na ƙauye." Dariyar dole Uwani ta bani, duk da labarin da take bani mai ciwone a gareta itama saida ta dara. Bani labarin yadda ta kaya a tsakaninki da Hafizu ranar da kika koma" "Hahahahhh baki da kyau Iyabo. A daren ranar ni ban barshi ya shigo mun ɗaki ba. Kafin ya dawo na garƙame ɗakina. Bugun duniya banbi ta kanshi ba, sai matarshi ce tazo ta jayeshi tana cewa wai ya barni ƙila bacci nake yi. Sai da safe dana buɗe ɗakina ya shigo muka gaisa sama_sama, ni dai naƙi sakin fuskata sai jana da hira yake yi nayi biris dashi. Ke saiga wani dumamen tuwo da wani ƙazamin ruwan kokko harda dogon gashi a ciki matarshi ta shigo ta dure mun. Ke dai kinsan banda daɗi Iyabo, a taƙaice dai na sai gida a can saman layin ta titi, ɗakuna ukune sai banɗaki da kitchen harda shago a ƙofar gidan, nayi komawata. So nake inna nutsu a gyare mun shagon in soma kasuwanci a ciki, in Allah ya dafa mun shikenan fa Iyabo. In Hafizu yazo miji, in baizo ba shi da banza basu da maraba. Bazan kashe kaina ba wallahi sabida rijalu. Ko yanzu ya tafa mun takaddar sakina cafewa zanyi in cashi zawarci" Kai na jinjina ina dariyar furucinta na kusa da ƙarshe da tace in yazo miji, in baizo ba shi da banza duk ɗaya. Uwani ta balbalin duniya. A irin zafinki kam zama gida ɗaya da kishiya ba naki bane, raba gidan yafi. Koni da ace Hamma zai amince mun da saina sai waje na gina inyi zamana a gidana da saina fi samun nutsuwa. Amman kinsan ƴan ƙauye su