Sashe 56
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ran haifa mishi namiji. Shine tace, in dai tana doron ƙasa ban isa na haife cikinnan ba. Shekaru uku kenan har mijin ma ya gaji ya sakeni, ina gida da ciki" Take zufa ta wankeni, jikina ya shiga ɓari. Malaminne ya soma magana da cewa. "Kwantar da cikin akayi bazai yi gaba ba bazaiyi baya ba. Amman kin kawo kukanki gidan mutuwa Akwai aljanin da zamu sa ya tayar miki da cikin. Zaki kawo baƙin raƙumi, da baƙin bunsuru, da ɓakar tunkiya, da baƙar mage. Wannan shine ladan aikin" Zumbur na miƙe ina haƙi, tari ya kamani na nufi hanyar waje. Uwani ta biyoni tana riƙeni muka fita. Uwani dama kina ta'amali da bokaye ban sani ba muke ta abota?" Na tambayeta raina a ɓace hankalina a tashe. Ita kanta a cikin rudu tace. "Wallahi Allah bansan boka bane. Kinsan Allah da girma yake Iyabo wajannan wata maƙociyatace ta taɓa zuwa, tana neman maganin haihuwa, ita ta kwatanta mun. Barni da Balbalin kema kin sani harkar shirka bana ciki. Mu maza mu bar wajannan danni gabana ma faɗuwa yake yi" Ba shiri mka bar wajen, a ciki na baro takalmina warin ƙafar hagu. Bamu muka koma gida ba sai wajajen sha ɗayan dare wallahi, gajiya, yinwa duk mun kwaso. Ni babbar damuwata bansan ko Allah zai amshi sallolinmu ba. Duk da shine masanin gaibu, munje wajenne ba tare da ilimin boka bane. Ni dai a zarge na rama sallolina. Uwani Allah yana gani zan koma gida muita adda,a da izinin Allah zai mun mafita. Bazan sake zuwa asibiti ko wani maganin gargajiya ba. Lokaci zaiyi halinsa, Allah zai nuna ma Hama ikonshi nayi wannan imanin Allah zai dubeni." Kwanana goma cib a garin Kano. Kwana huɗu a gidan Uwani, kwana shidda a gidanmu. A kwanaki gomannan na siyar da zinaraina, Uwani ta sai gidana dake jikin nata muka gagganɗa kuɗin aka siya mun gidan sama mai ɗakuna goma sha biyar, da shaguna huɗu. Burodami Kokodeen da Burodami Debisi, da Uwani sune suka zama shaiduna, muka biya aka gyara takaddu da cike_ciken abinda ya dace, na kamo hanya na dawo, gida na hannun Uwani da Burodami Debisi su zasu saka haya su amshi kuɗin hayar. Ƴan canjinan da suka ragemun, na siyo kayan aune, aune, da busassun kayan miya, da maggi dunƙule da fari, da dai abinda duk nasan ina buƙata. Iyaa Debisi ma tayi mun tsarabar doya, garin alba, garin amala, bushasshiyar gandane. Burodami Debisi shi kuma shinkafa da wake ya aunarmun mai yawa, ya kawo nama akaimun miyar stew soyayya mara ruwa ƙaramar robar fenti. Uwani kuma kayan miya ta siya da yawa aka niƙo ta tafasamun ta duramun a jarka aka zuba mai a saman, yana daɗewa sosai bai lalace ba. Banda tarkacen su yajin daddawane, jan yaji ne. Tsaraba dai rigi_rigi na koma da'ita. A tasha na samu Yaya Hamma a tsaye kamar yadda ya saba yana jiran dawowata. Da magriba matan gidan duk suna tsakar gida anata aikace_aikace sai gamu mun shigo da sallamata. Ga yara na bina da kaya rigi_rigi. Yaya Hamma shima yana riƙe da wasu kayan. Hmm kunsan me? Da muka gaisa da matan gida saina nufi ɓarayin Yafendo na yada zango acan. Yaya Hamma kuma ya wuce masallaci, dan anata kiraye,kirayen Sallah. Bayan na rama sallolina Baɗɗo ta kawo mun tuwo naci. Sai Yafendo take faɗamun mummunan abinda ya afku bayan kwana uku da tafiyata. "Jabu ai bayan tafiyarki da kwana uku gobara ta tashi a lungunku. Da ɗakin Safiya, da Ɗakin Fatu ƙarama da naki. Ƙurmus suka yi babu abinda aka ɗauka. Gobarar daga ɗakin Fatu ƙarama ta tashi, anyi ruwa mamako saita shiga da gaushi ɗakin. Ashe ya kama zanin gadonta ita bata sani ba, cikin dare sai wuta ta tashi. Murmusawa nayi idona na hawayen da suke shirin makanta ganina nace. Allah yasa sa da abinda ya tare" Yafendo ta girgiza kai tace. "Ameen. Bayin Allah duk sun kakkawo taimako anata kan karɓa kinsan mutanen ƙauye da haɗin kai. Zamu kwana tare dake anan har zuwa a gyara miki ɗakin naki. Su Safiya duk suna gidansu." To Shikenan Yafendo mun gode. Shigowar Yaya Hamma yasa Yafendo ta fice ta bamu waje. Zama yayi yana fuskantata, ni kuma inata share hawayen da nayi yin duniya yaƙi tsaiwa, da kanshi yake hankaɗo kanshi. Kallon tausayi yake yi mun, mai cike da tsantsar so. "Kiyi haƙuri Jabu. Haka Allah ya ƙadarto mana. Daga wannan sai mu faɗa wannan. Aikin gadin dana samu ma ya kuɓuce mun. Matar gidan tasa an ɗakko ɗan uwan mijin a ƙauye an bashi aikin. Shanun da nake gadara dasu duk sun soma ciwo, yanzu haka Yuguda ya tafi dasu asibitin dabbobi. Annobar bace ta samu shanun. Waɗanda shanayensu basu kama ciwo ba, duk sun tafi ciranin dole, dan gujema annobar. To mu kam kusan rabin shanunmu ciwon ya kamasu, jikinsu duk kuraje. Kaɗan daga ciki da basu fi ashirin ba Jumare ya tafi cirani dasu. Kiyi haƙuri zan sai miki kayan ɗaki gwargwadon halina." A'a Yaya Hamma. A halin yanzu bata kayan ɗaki ake ba. Mu yi adda'ar Allah ya kawo sauƙin wannan annoba data samu shanun kawai. Babu komai zamuita lallaɓawa" Jigum_jigum muka yi. Kunsan dai bafulatani da Shanu. Baffa Musa ma ance yana kwance babu yadda yake a dalilin shanayenshi wajen bakwai sun mutu. An siyar da kusan goma. Jikin nashi yayi tsananin tsananta. Haka a daren muka je dubashi baya gane ma wanda yake kanshi. Mu dai gamu jigum_jigum su Dada sai sharar hawaye suke yi. Domin shi suke gani a makwafin uba a garesu. Wannan kenan. Su Yafendo ne suka yanke shawarar data tashi hankalina cewar asubar fari Yaya Hamma ya kora shanun Baffa Musa ya tafi wannan cirani dasu. Ai kuwa hakan akayi, a gidan Baffa Musa dukka muka kwana. Washe gari sassafe gun_gun matasa da magidanta suka haɗe kawunansu suka ɗau hanyar dokar daji, su kansu basusan a ina zasu samu garin da zasu yada zango su kafa tantinsu ba. Har waje nabi Hamma ina kuka. Ku dubi kunya irinta bafulatanin mutum amman gam Yaya Hamma ya riƙe hannayena yace. Har abada soyayyarki ta dabance a zuchiyata bazan mance da halaccinki a gareni ba. Jabu ki tayani da adda'a ba zan fi shekara ɗaya ba ko dan inzo inga abinda kika haifa zan dawo. Bazan mutu ba har sai Allah ya sake ara mana lokacin da zamu sake shinfiɗa sabuwar rayuwa. Yara goma sha biyu zaki haifamun dukka maza in sha Allah." Ina kuka ina murmushi mu kai sallama yabi ayarin gungun fulani da gungun shanaye, suna tafe suna waƙar fullanci ta nuna jarumtarsu. A ranar nayi kuka sosai. Sun tafi babu jimawa dan ko awa uku ba'aiba da tafiyarsu Allah ya ɗauki ram Baffa Musa sanadiyyar mutuwar shanunshi fulani da shanu ba dama ne. A wannan shekarar anyi asarar dukiya anyi asarar rayuka sosai. Dan wasu da kansu suka kashe kansu, wasu kuma zuchiya suka haɗiye suka mutu. Haka akaita zubar da gawawwakin dabbobi abin tausayi. Wasu wannan ne yai silar karayar arzikinsu ciki harda Mijin Cubu, da mai Nagge mahaifinsu Baɗɗo, danshi kab shanunshi wayar gari akayi asa tarar sun mutu. Sai ya zama kamar wani zautacce_zautacce haka.