← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 72

Sashe 53

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read

yadda ya ɗauki rai ya ƙallafa akan wannan ciki. Shi burinshi ya haɗa jini dani Uwani. Wallahi tsoro da fargabar me kaje kazo ne ya hanani ce mishi komai. Ina cikin tsaka mai wahalar fita." Kuka na fashe dashi, nayi shi ƙaƙas sai naji zuchiyata ta ɗan rage naunyi ni da kaina nayi shiru. Uwani bata hanani kuka ba. A ko da yaushe Uwani takance kuka shima wata hanyace ta rage nauyin zuchiya da cunkushewarta. "Hmmmm ki kwantar da hankalinki Iyabo. Zamu zagaye asibitocin Kano. Kuma in sha Allah za'a dace. Akwai wani malami zan ɗaukeki muje zai taimaka miki." Dawowar Hafizu ne ya katse mana hirarmu. Lemon montin dew ya ajjiye a gabana. Da kular sakwara. "Hajiya tunda kinyi baƙuwa zan tafi. Sannan ki daure kije ki duba me jego da takwararki" Uwani ta dubeshi sai naga tayi dariya, ta zuge lalita ta ciro kuɗi ta bashi. "Ga albashinka nan" Yayi saurin cewa.." "A'a ki riƙe a wajenki. A tsintamun kayan jaririya a cikin kwashe irin na ɗari_ɗari ko tsinke ban siya ba" Kuɗin Uwani ta mayar tace. "Gasu can ƴan ɗari_ɗarin ka ɗebi na iya kuɗinka" Ni dai ina jinsu, Sakwara nake ci hannu baka hannu ƙwarya ga ganda sutu_sutu a miyar. Sai da Hafizu ya fita nace. Uwani ki ƙyale Hafizu haka dan Allah " "A'a fa Iyabo. Barni da Hafizu inda kika gammu. Nifa a haka nayi matuƙar ƙoƙari da kai zuchiyata nesa tunda har na iya ɗaukarshi aiki nake biyanshi duk sati yake samun naci da iyalinshi. Banyi ƙoƙari bane nifa nake ci da kaina da nawa yaran. A shago ina siya mai abincin rana. To me kike so, in goyashi in yi yawo dashi kome? Kinfa san komai duk ba akan Hafizu naje na afka bala'in da Allah ne yayi ina da tsayin rayuwa ba. A ƙarshe me yayi mun?" Anan zan dakata sai ranar monday kuma MRS BUKHARI
Chapter 53 · 0% Book details