← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 72

Sashe 6

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni da uwani kuma muna madafa na hura kara ina kiciniyar ɗaura girki ta dubeni tace. "Iyabo yanzu kema da karar zaki dinga girki in kunyi auren ko? Ni wallahi Iyabo ba wai ƙin Hamma nake yi ba, ba kuma ƙyamatar rayuwarsu nake yi ba. Ke nake jiye ma, kece baki saba da irin wannan rayuwarba, su fes suke jin kansu ba wata matsala, ta ina ke zaki soma Iyabo?" Murmushi nayi mata ko a jikina nace. Nifa babbar nasara shine in zama mallakin Hamma kawai, kuma inason in zauna da Dada, aurenta fa ya mutu faɗa miki ne banyi ba uwani. Uwani zuchiyata tayi nisa da sonshi, idanuna ya rufe bana hango komai. Bini da adda'a ƙawata kawai, ki dena damun kanki. Da birni da ƙauye duk rayuwar ɗayace, ita mace kwanciyar hankali take buƙata a gidan aure ba birni ko ƙauyeba, sannan inason in koya ma ƙannena yadda zasu bautama Allah. Hatta Dada daga iya alwalarta akwai gyara ina ga karatun Sallah kuma." Dariya tayi kafin tayi Magana kawai sai muka jiyo guɗar su Boɗɗo da su Cubu, harda Yafendo Jabu. Kuma wajenmu suke nufowa. Suna shigowa Baɗɗo tace. "Adda yau dai kin zama matar Yaya Hamma an ɗaura aurenku babu jimawa" Farin cikine, a'a ruɗewace sai kawai naji gudawa ta kamani. Kafin in miƙe sai Yafendona tace. "Munyi farin ciki da wannan Aure. Muna fatan mutuwace zata rabaku. Adda Daso sai kukan farin ciki take yi" Ni dai da jin wannan labarin saida nayi gudawa sau biyar cikin awa guda. Ina cikin wannan zuruftu saiga Hamma da abokanshi biyu sun kutso kai gidan. Nayi maza na shige kitchen dan yafi kusa dani. Idanu na lumshe inajin wani farin ciki na cikar buri na lulluɓeni. Amman sun sammaceni, babu shakka wannan shine dalilin zuwansu Baffa Musa da safe asibiti, kuma shine dalilin Dada na cewa za'ayita ta ƙare, ashe tana nufin auren za'a ɗaura kowa ya huta. Uwani ce ta dafani nayi saurin buɗe idanuna. Sun tafine uwani?" Na tambayeta ina dariya. Itama dariyar take yi tace dani. "Sun tafi, dake da Hamma bansan wanda yafi wani farin ciki ba. Bakiga bakinshi ba yaƙi rufuwa sam. Ina miki fatan alkhairi Allah yasa ki samu farin ciki ɗorarre na zubar da makaman yaƙina iyabo, Allah ya ƙadarto miki rayuwa a rugga" Ameen Uwani ko ke fa. Yanzu dai me ake ciki dangane da kayan ɗaki? Ni a kano naso sayen gado da kayan kujeruna gaskiya, to yanzu ba lallai lokaci ya bamu damar hakan ba" Baɗɗo ce ta shigo tace. "Adda kizo Baffa na son magana dake" Uwani ki dinga duba girkinnan kafin inzo' Nasa kai na shiga ɗakin Dada da sallama. Dukka ƴan uwan Dada suna ciki. Yafendo Kaɓoji tace. "Tawo ki zauna a kusa dani ƴata" Cike da kunya na ƙarasa na zauna a gefen ƙafarta. Baffa yace dani. "Ungo nan Jabu sadakinkine nera dubu biyar. Ɗazu aka ɗaura aurenki a ƙofar gidan mai gari ke da Hamma. Amman kasancewar auren yazo babu wani shiri, inda zai saki ma bai gina ba tukunna zaki zauna a gida kamar na sati biyu kafinnan ya gama ginin ya kuma gama haɗa lefe sai ki tare" Hannu nasa na amshi sadakin. Na kuma ji daɗi sosai da akace mun sai nanda sati biyu zan tare. Har zan shiga Kano inje inyi gyaran jiki in kuma siyi kayan ɗaki irin wanda raina yake so" Yafendo Kaɓoji tace. "A'a Yaya sati biyu yayi yawa. Ginin yau zasu soma da abokanshi zasu iya gamawa yau. A bar dai tariyar rana ita yau zaifi" Dada tace. "Allah ya nuna mana rana ita yau ɗin. Amman ita Jabu gobe zata koma kano kamar yadda na sanar daku, acan za'aje a ɗakko Amarya a wajen dangin mahaifinta suna da hakki. Da ace lafiya nake da ni da kaina zan kaita inyi ma Toyosi ɗin bayani a nitse dan gudun kar suga kamar anyi musu fin ƙarfine." Baffa Musa yace. "Hakanma yayi, babu damuwa ku zaku tsara yadda tafiya ɗakko Amaryar zai kaya. Allah ya sanya alkhairi. Jabu zaki iya tafiya sai ki kwana da shirin tafiya kanon gobe. Duk abinda zaki kintsa saiki kintsa rana itayau za'a zo ɗaukar taki, ki sanar musu suma acan. To Baffa " Iyakar abinda na iya cewa kenan. Na fita na samu Uwani na labarta mata duk yadda mukayi. Haka dai muka wuni tarbar baƙi masu zuwa dubiya. Su Yusufu duk suna gidan sun shige ɗakinsu da abokansu. Sai da daddare Hamma ya samu zuwa muna tsakar gida mun gama cin abinci munyi sallar isha anata hira ina jin daɗin kasancewata tare da ƙannena, sai gashi ya shigo da sallamarshi. "Ango kasha ƙamshi lale da zuwa" Cewar Uwani kenan tana tsokanarshi. Hannunshi riƙe da ledoji biyu. Sai ya miƙa ma Cubu leda ɗaya yace ta kaima Dada. Ɗayar kuma yace ta Uwani ce, na karɓa na miƙa mata. Watsewa sukayi suka barmu mu mu biyu a tsakar gidan. Ni ina kan tabarma shi kuma yana kan jarkar ruwa yana fuskantata. Ina wuni Yaya Hamma? Na faɗa a sanyaye da sabuwar muryar da baisan na mallaketaba. Wata iriyar muryace mai kama da busar sarewa." Sai da ya sauke ajjiyar zuchiya nannauya kana ya dubeni muka haɗa idanu sai yace. "Faɗa ya ƙare Hamma yayi nasarar samun Jabu na kayar da mutan birni." Dariya ya bani sosai. Yaya Hamma kenan. To Allah ya bamu zaman lafiya. Allah ya baka ikon yi mana adalci a tsakaninmu" "Ameen nagode da wannan adda'ar taki. Sai batun tarewa Dada tace an tsayar da maganar tarewa sati me zuwa. Kuma a Kano za'aje a dakkoki ko?" Kai na gyaɗa mishi. Sai yace. "Maganar kayan lefe zan baki kuɗinne ki siyo abinda kikeso a Kano harda fantimoti ko yaya kike ganin za'ayi?" Duk yadda kayi daidaine na baka wuƙa da nama" Kai ya girgiza yace. "Ni kinga bansan kalaba. Sannan Hama ma ba sanin kala tayi ba bare in bata ta haɗo komai" To ka tuntuɓi su Dada ko su zasu haɗa ni basai na haɗa lefe ba" "To Shikenan Amarya yadda kikace haka za'ayi. Zan tuntuɓi matar ogana na birni naga kamar kayayyaki take siyarwa in yaso sai in bata ta haɗamun duk abinda ya dace. Yanzu nawa kike buƙata na gyare_gyarenku na Amaren birni?" Dariya nayi mishi. Shima dariyar yayi. To kuɗin gyaran jiki, sai kuɗin ƙunshi, da kuɗin kayan fitar biki Shikenan abinda nake buƙata" Hannu yasa a ajjihu ya zaro nera dubu goma sha biyar Murtala _murtala ya miƙo mun, nasa hannu na karɓa nasa musu albarka." "Gobe zanzo in kai ku tasha, dama inason zan sai fenti a birni mun gama gina miki ɗakinki. Duk da dai ban samu yadda nake so ba lamarin yazo mun babu shiri" Zamu rabu kamar ba zamu rabu ba a wannan dare mai cike da ni'ima iska sai kaɗawa take yi hadari na rugugi a sararin samaniya. Ganin an soma yayyafi yif_yif yasa ba dan rai ya so ba muka rabu da juna cike da shauƙin junanmu. Washe gari sassafe muka shirya tsab Yaya Hamma yazo ya kaimu tasha har sai da motarmu ta bar tasha suka tafi shi da aminanshi. Bayan la'asar sakaliya muka shiga gida. Su Iya duk suna tsakar gida suna murnar haihuwar Bose muka tarar dasu. Nan murna ta zama bibbiyu. Sai da muka nutsa muka rama sallolin da aka boyomu, Uwani tai ma Iyaa bayanin duk abinda ke a kwai. Da jin wannan bayani sai Iyaa ta miƙe tsaye tana buga cinyoyinta tana faɗin. "Mo ti pari mo ti pari ah ah ahh.. ( na gama yawo, na gama yawo) Iyabo aure a ƙauye a wannan garin zaki zauna kiyi zaman aure? Kin kashe rayuwarki, kin kashe kanki" Kafin kwabo Sai gasu Iyaa Beji da su Iyaa Kokodeen sun shigo. Bata sauya zane ba. Ita dasu duk kanwar ja ce, sukaita kwakwazo har sai da Alfa ya shigo shine ya tsawatar musu. Iyaa kuwa du hannuwanta aka ta ɗorasu tana jijjiga harda hawaye shaɓe_shaɓe tana ta ambaton Ah ah ah...." Wanda indai kaji beyerabiya nata maimaita wannan kalma to fa abu yayi abu. Alfa ya tambayi Iyaa Kokodeen meke faruwa. Kafin tayi magana Iyaa Debisi ta soma magana da yare ta bashi labarin abinda Uwani tace mata. Jimm yayi sai halamun tsoro suka bayyana a fuskarshi muraratan. "Je otito Iyabo?" ( Da gaske ne Iyabo) Ya tambayeni idanunshi kakkafe a kaina. Beeni ( Eh)" Itace kalmar dana furta a sanyaye. Shima jikinshine ya kuma mutuwa mus. Gwauron numfashi ya sauke yace. "To Allah ya sanya alkhairi. Tunda rayuwar da kika zaɓama kanki kenan mu bamu da abinda zamu ce dake. Toyosi kiyi haƙuri ki bita da adda'a a wannan karon kar ku juya mata baya." Da ƙyar ya rarrashi Iyaa ta haƙura. Ni da Uwani dai duk mun takure, Uwani taso tafiya ma, amman ganin irin faɗan da Iyaa ta dinga yi mun yasa dole muka kwana tare. Washe gari ragowar samari da magidanta gidanmu duk labarin aurena ya ruskesu. Kowa sai jimantamun yake yi. Burodami Debisi kuwa kamar zai yi hauka da yazo gidan yaji labarin abinda ake ciki. Ƙasa zaman gidan yayi ya fice. Nan Iyaa ta sake saka ɗambar faɗa tana faɗin. "Ai duk Debisi ne ya ja wannan abun. Tunda tun farko dashi ya auri yarinyarnan da sai dai mutuwace zata rabasu. Gashi yanzu ta kashe rayuwarta a banza, wawuyar yarinya wadda batasan meke mata ciwo ba. Ko da yake Daso ce ta zuga ta shi yasa ta jayeta su je su sha wahalar tare" Iyaa ta dinga jero zance babu arziki muka shirya tsab muka bar gidan. Da gidan Bose muka soma, sai muka nufi gidan Uwani data siya. Hafizu yana zaune a kan benci a ƙofar gidan sai gamu. "A'ah Alaja Iyabo rakiyarce kuma har Kano? Lallai wannan ƙawance naku da girma yake" Ya ƙarashe yana dariya sai kace wanda yaga wawan zama. Uwani kuwa girar sama ta haɗe data ƙasa, ta buɗe gidanta tayi shigewarta ta barmu muna gaisawa dashi. A tsakar gida na sameta tana kiciniyar buɗe ƙofar ɗaki. "Taho ki soma ganin dilolin kayan. Da mun gama hidimar biki zan buɗe dila amman nafi son in gyare shagona tsab." Ta buɗe ɗakin muka shiga, ga dilolinan masha Allah, wani kan wani dukiya akwai
Chapter 6 · 0% Book details