Sashe 4
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read
gidan gandunnan shi suke yi, kowa dai da ɓarayinshi." "Amman dai zaki gyare ɓangaren naki yadda zaki ji daɗin zaman wajen ko? Ina tausayinki Iyabo baki san sharrin rijalu bane hmm" Murmushi nayi nace. Sai dai in gyara cikin ɗakin nawa, wallahi Uwani bana son inyi wani abun da zai haskoma Hamma kamar na raina arzikinshi. To iyakar gyara zan yishine a cikin ɗakina" Harara ta watso mun taja dogon tsaki ta jiya baya ta kwanta. Uwani meye haka?" Cikin masifa tace. "Da Allah Iyabo mu bar zancannan ni bacci nake ji naga kamar kin zama majuniniyane akan Hamma" Dole haka zancan ya tsaya. Ni kuwa na jima cikin tubka da warwara da ƙyar bacci ya ɗaukeni cike da mafarkai marasa daɗi masu tada hankali. Gabaki ɗaya saina wayi garin cikin damuwa da fargabar data haifarmun da zazzaɓi. Da sassafe saiga Yafendo Kaɓoji, da Baffa Musa sunzo. Dada tace mu basu waje, me suka tauna oho basu jima ba suka kama hanyarsu. Muna komawa ciki saiga takaddar sallama da ragowar kuɗaɗen da ake binmu. Gashi yau tun sassafe Yaya Hamma ya bar asibitin. Uwani ta zauna da Dada ni kuma naje na biya kuɗin da ake binmu. Ina dawowa na tarar da Amaduyal shi da Kari matarshi. Kari ce ta tayani tattare kayayyakinmu tsab, Amaduyal kuma nace ya fita ya nemo mana ƙaramar mota zuwa Girai. Ai kuwa hakan akayi motarnan ta saukemu a Girai muka hau akori kura zuwa Banyo, daga Banyo muka ƙarasa jaɓɓi. A sabon gidan Dada muka sauka. Ta kalli gidan ta kalleni saita saki kukan farin ciki ta dubeni tace. ", Jabu Allah yayi miki albarka. In sha Allah Kamar yadda kika sani zubar da hawayen farin ciki. Rayuwarki zata yi albarka. Allah ya jiƙan Adetoye da rahama." Ameen Dada nagode sosai mu shiga ga ɗakinki nan. Wancan nasu Cubu ne, sai na su Yusufu gashi can." Ɗakin muka shiga daga gado sai wata kujera doguwa guda ɗaya, sai kafet malale a ƙasan ɗakin da labule, sai akwatin kayanta guda ɗaya. Kayan ciki sababbi nasa aka ɗinko mata da hijabinta biyu da takalma biyu sai dadduma. Kan kace me labarin sallamomu ya kareɗe ƙauyen nan mata suka cika gidan ana ma Dada Yaya jiki ana mata barka da arziki. To nima anan nake cewa mu tara gobe in Allah ya kaimu.... MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI