← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 72

Sashe 26

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya yayi ma Hadiza ya kalleta yace. "Hadiza duniya, fitinarki yawa, kin iya tada zaune tsaye. Ayi magana kice anci miki fuska." Haɗe rai tayi tace. "Wai ni kam tsohuwar matarnan taka dame tafi sauran matane, da har yanzu ka kasa daidaita sonta da namu? Ƙila ma ta mance dakai ita sam a rayuwarta tana tare da mijinta ya kankare ka a zuchiyarta da ƙwaƙwalwarta" Haɗe rai yayi ƴar fara'ar da yake take ta tsaya. Dama tayi ne dan ta kunna mishi wutar kishi, ko babu komai ranta sai yayi fes. Washe gari Gwadabe ya bata kudi ta shiga kasuwa tayo ma ƴan takai tsaraba, har turamen atampa ya bata ta siyo mishi, da kayan yara na yaran Bara'u, da yaran Tamu. Baba Fhatsima itama ta haɗa musu nata tsarabar, ɗan kayan kwance Anti Badi'a ta tarkata tace a kaima Sakina. Malam da daddare yasa akai mishi kiran Gwadabe ya sameshi a turakarshi dashi da matanshi duka anata shari'a Sabitu ya daki matarshi har tayi yaji. Shigowarshi yasa Malam sallamar kowa sai Baba Fhatsima da take dashi ranar. "Gwadabe naji a bakin Gyatumarku kunason zuwa Takai ko?" "E Malam gobe in Allah ya kaimu zamu tafi harna yankar mana tikiti." Malam yayi jim. "Toh Gwadabe bazan hanaka shiga Takai ba ko dan Bara'u da matarshi su kaɗai sun isa ayi tattaki akai musu ziyara. Amman akwai abinda na ɓoye maka. Ga Fhatsima ita tasan komai Jamilu da yayi mun rakiya shima yasan komai. Babala tace Allah ya isanta nononta daka sha in har ka shigo Takai ka shiga gidannan. Sannan ta yanke halaƙarka da ƴan uwanka Allah ya isanta in ka je musu gida. Babu abinda bata faɗa ba. Dan haka sai ka guje ma Allah ya isanta kar ka kuskura ka shiga cikin gidanku. Hadiza da Shafa zasu iya shiga su nuna mata yara in Allah ya bata ikon ganinsu to, in suma ta korosu sai a haɗu duk ayi haƙuri. Iyatu da Hambali ke zuga uwarku akanka nayi iya tunani da hangen nesa namu na manya mahaifiyarku tana da son abin duniya, shi yasa take ɗaukar duk maganganun da Hambali ya ɗaurata akai. Da ace Allah zai ɗaga darajarka a duniya ka samu arziki zaka sha mamakin yadda komai zai wuce kamar bai faru ba. Gwadabe ka daɗa haƙuri kaji ko?" Kan Gwadabe ya ɗaure, amman baiyi mamaki ba. Murmushi yayi ma Malam kawai yace babu komai ya gode, kuma zai kiyaye in sha Allah zaiyi yadda take so ɗin. Washe gari asubar fari motarsu ta ɗaga sai Kano. Tafiya mabudin ilimi sun fito shiddan asuba basu suka shiga Kano ba sai shidda na yamma. Gwadabe na sauke ƙafarki a garin Kano yanayinshi gabaki ɗaya saiya canja, tunaninshi ya sauya, yana hasko irin rayuwar da suka gudanar shi da IYABO a garin Kano. Har Hadiza ta soma zargi kunsan bakinta baya haila cewa dashi tayi. "Hala tunanin tsohuwar matarnan taka kake yi. Naga duk ka sauya?" Baiko kalleta ba ya soma nema musu motar da zata shiga Takai. Sun ko taki sa'a motar akwai wajen mutum ɗaya daga ita kuma mota ba zata sake barin tashar ba sai gobe. A haka suka shiga Gwadabe ya zauna a injin shi. Wajajen tara da ɗoriya sai gasu a Takai abuka da ƙauye garin a cike yake dam da matasa gungu_gungu, da magidanta a ƙofar gida wasu na hira wasu rediyo suke saurare, ga yara ratata a waje sunata wasansu cikin kwanciyar hankali. Suna tafe zuwa gidan Bara'u da kici_kicin kayansu suka zo wucewa daidai ƙofar gidansu. Gabanshi ya yanke ya faɗi ras. Yau shine zai wuce gidan da aka haifeshi yayi rarrafe da wasan kasa a cikinshi, gidan da a ciki aka birne mahaifarsa. Wasu siraran hawayene suka gangaro mishi ya wuce gidan da sauri. Hadiza dai sai jejjefa kafarta take yi, babu wuta garin yayi duɗum dashi. Gaba da gidansu kaɗan anan majalisar abokan gwadabe take abokai irin na wasan kasa. Ai kuwa ilai Bara'u na wajen anata fafata musun da suka saba. "Sannunku sarakan musun tsiya" Cewar Gwadabe, da fara'arshi dan ganin tsoffin abokanshi. Nan suka soma sowa da hargowar murna. Bara'u yace. "Hadiza barka da shigowa Takai ta kawo ta saba da saukar baƙi." Murmushi tayi aka gaggaisa. Gwadabe ya gabatar da'ita ga abokanshi. Suka sake gaisawa da'ita. "To bari mu karasa inna ajjiyeta zan fito muyi hirar yaushe gamo." Ila yace. "Akwai babban labarin abokinku kai da Bara'u Zilƙifulu." Baki Gwadabe ya buɗe yace. "Zilƙi fa kace, ya dawo daga yawon duniyar kenan? Shegen kaya bari in fito gaskiya a darennan ma ni sai naga Zilƙi" Bara'u ya tayashi ɗaukar kayan shi da Ila, Ila iyakarshi dai zaure. Sakina da yara suna tsakar gida zafi kamar zai kashesu suka jiyo sallamar baƙi. Suna shigowa Sakina ta riƙe baki. "Ah_a_a_a manyan baƙi mutanen nijar. Hadiza maraba lale. Gaskiya Bara'u muna da manyan baƙi yau" Sakina tayi maza ta kunto Ummi daga bayan Hadiza. "Ga tabarma Hadiza zauna dan ɗakin baya shuguwa, kun shigo lokacin zafi sai sanƙarau aketa yi da kwalara." Zazzaunawa suka yi, nan aka shiga gaisuwa yaran kuma duk suka ruƙunƙume Gwadabe suna ga Baba ga Baba. "Shafa anan gidan ta wuni yau cur. Abba yayi wayau sosai, danma ƙurajen zafi duk sun fesuo musu har uwar wallahi" Cewar Bara'u. Ita kuwa Sakina tana kitchen taje hado abinci, Ummi tana hannun Bara'u" "Sakina ki bar tuwonki. Bari inje wajen Nalanjin in karɓo musu gashasshiyar zabuwa suci su more" Da dariya Sakina ta fito "Kaga Shinkaface da miya yau muka dafa ba tuwo ba sabida Shafa." Bara'u yayi Dariya yace. "Kice yau Toye ya cika cikinshi har ya gaji?" Itama dariya tayi tace. "Ɗan jakar uba ba. Gwadabe Toye baya son tuwon masara sam yaronnan. Dana zubo tuwo sai ya kama kuka harda birgima fa" Dariya suka fashe dashi. Gwadabe yayi ma Toye yarbanci, kafin yace da Sakina. "Dake bamu fiye yin tuwon masaraba sai Amala, ko sakwara, ko tuwon farin albo shiyasa bai saba da tuwon masarar ba" . Bara'u yace. "Allah sarki tsuntsun soyayya. Ni ko Gwadabe kana jin labarin Iyabo kuwa? Ya kamata ko ba komai ayi zumunci bai kamata muyi fatali da Iyabo ba baiwar Allah guda da bari." A_ido_a_ido Gwadabe ya kalli Hadiza, saida ta kasa jurewa ta sauya fuska. Sakina tace. "Ko da suka shigo cikin gidannan sai da Iyabon ta fado mun. Ban dakko zancan bane sabida kar Hadiza taji babu daɗi" "Hakane kuma uwargida a gafarcemu, ai yanzu kambun sarautar a hannunki yake. Gwadabe tawo muje mu siyo mata gashasshiyar zabuwa" Ficewa suka yi nan suka bar Hadiza da dariyar yake ta ciki na ciki. GWADABE "Gwadabe Yaya Hambali ya zama babban mai kuɗi, yana ɗaya daga cikin manyan masu kuɗinmu na Takai. Da azuminnan daya wuce, yayi rabon abinci na ban mamaki. Sunje sun sauke farali har su Fodiyo ya biyama. Kai kaga inya shigo Takai yadda ƙofar gidanku yake cika kuwa? Hmm abun ba'a cewa komai. Babala kuwa tana dai shigowa Takai duk wata tayi sati guda ta koma Kano. Hambali ya ɗauketa kacokan daga Takai, kuma kasan Hambali ya auri Laila kuwa?" Gwadabe da bakinshi yake buɗe dan mamaki, ai saiya sake buɗe bakinshi. "Ya auri Laila fa kace, ita auren nata kuma mutuwa yayi ne?" "Mutuwa kai. Laila ai a kotu ma alƙali ya raba auren. Gagarumar sata taima mijin na akwatin kuɗi guda. Taita facaka da dukiyarshi shi bai sani ba, lokacin fa Laila ta shigo gari. To su Yaya Hambali ne suka tsaya mata lokacin ana kes ɗin, duk zaman kotun bai wuce ni ba. To bayan Yaya Hambali ya biya shi mijin kuɗin da Lailan ta sace, sai suka nemi a raba auren kawai. To kai kasan Baba Iyatu idonta idon kuɗi nan taita naci da kuke kuken dole a cikin yaran Babala a samu ɗaya ya auri Laila ko dan a rufa mata asiri. Shine Hambali ya daki ƙirji ya aureta. Kai kaga bikin da muka sha a ƙauyannan? Ba'a taɓa yin biki irin nasu ba ni dai a iya tasowata" Kai Gwadabe yaita jijjigawa har suka siyo zabuwa suka juyo, Gwadabe ya kasa cewa komai dan mamakin abubbuwan, da mamakin yadda ya zam bare a cikin ƴan uwanshi cikin ummanshi. "Kaji labarin Zilƙi a wajen Ila ko?" Ajjiyar zuchiya ya sauke, Bara'u ya lura Gwadabe ya lula duniyar tunanin yadda dangi sukai watsin ruwan tsarki dashi, shi yasa ya kawar mai da tunani da zancan Zilƙi. "Wai ashe Zilƙi zai dawo ƙauyannan? Nifa na ɗauka ya manta da kowa" Dariya Bara'u yayi yace. "Sai gashi ya dawo abinshi. Kuma kasan abin mamakin? Shine charman na nan Takai. siyasa ya faɗa ka'in da na'in kasan Charman ɗinmu daya sauka na nan Takai abokinshi ne, shima dake saida shima ya je ya gama yawon duniyarshi ya dawo ya faɗa siyasa. To wallahi shi ya tsaya ma Zilƙi akaita shige da fice, dani akaita yawon kanfen waje_ waje har dai Allah ya karɓa mishi ya zama Charman" Dariya da mamaki Gwadabe yayi ya buɗe baki yana murna. "Charman Zulƙin? Iko sai Allah, Allah mai yin yadda yaso da bawa. Gobe zaka kaini gidanshi an daɗe ba'a haɗuba." "Ai kuwa shima sai tambayarka yake yi tun ma ana kan gangar siyasar. Kaci sa'a jiya ya dawo daga Abuja yaje taron wani semina. Gobe da sassafe zamu dirar mishi mu karya a tabkeken falonshi. Dariya du su biyun suka yi. "Ya batun nomar bana Bara'u?" "Asara kawai Gwadabe, Takai wannan karon anyi asarar dukiya noman bana babu yabanya me kyau sai dai godiyar Allah musamman mu masu noman gyaɗa har ɗan dama dama masu noman maiwa. Ya taka sana'ar maganin ka ce mun dai ka soma zuwa cin kasuwar ƙauyuka ya yanayin kasuwar to?" Sai da Gwadabe ya jajanta ma Bara'u kafin yace. "Kasuwa Bara'u babu abinda zance sai hamdala wallahi. Duk kasuwar ƙauyan dana ziyarta dana baza magani na soma yehuwa zaka ga an lulluɓeni. Bara'u fatana shine Allah ya bar abokarmu har yaranmu su gajeta. Ɗazu kayi maganar Iyabo, tunda muka rabu ban sake sa Iyabo a idanuna ba gaskiya. Amman in sha Allah inna shiga Kano ko a tasha ne zan ajjiyesu in nemi gidan Uwani. Ko kuma in barsu a nan Takai ka rakani mu nemi Uwani inji labarin Iyabo.
Chapter 26 · 0% Book details