Sashe 16
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 1 min read
shi a cikin yin ba daidai yake ba kenan?" Tsaki yaja kawai. Gaga_gaga haka rayuwar taita turawa kwanaki cikin kwanaki. Har Shafa tayi arba'in. Ana gobe Hadiza zatayi arba'in Gwadabe ya dawo daga cin kasuwa can garin Tawa yace. "Ki shirya jibi zamu je Najeriya. Zamu je mu gaishe da su Babala da abokaina. Shafa ma jiya suka shiga Takai ɗin." "To Shikenan Allah ya nuna mana. Dan Allah kayi haƙuri a bisa laifin da nayi maka jiya. Wallahi zuchiyata ce ta kasa jura naga daka dawo a madadin ka mayar da hankalinka a kanmu ni da Ummi. Sai inga damuwarka Shafa dai da Abba." Ƙur ya zuba mata idanu kamar bazaice komai ba dai sai yace kawai. "Bakomai Hadiza. Gobe ma da ƙorafin da zaki kawo. Kinga ita ko Shafa bata taɓa mun ƙorafin komai a kanki ba. Hadiza baki gane bane kinci babban kaso a zuchiyata mai girma. Ya kamata ki kwantar da hankalinki" Murmushi tayi taji daɗi har a cikin ranta. Kuma ta gamsu da hakan. Tana girmama yadda Gwadabe yake ɗaga mata ƙafa. Har cikin ranta tasan kishi da ƙorafi shine matsalarta, tayi imani Shafa ma nada nata matsalar. "Na haɗa harda kason tsohuwar matarka na kwakwushe Iyabo?" MRS BUKHARI