Sashe 55
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba aure yayo da kuɗinshi ba, abinda yayi ragowa ya cinye shi da amaryarshi ba? Wai ko so kike in danƙa mishi ragamar dukiyata ne, sai yadda yayi da'ita?" Tabalbalin ta dinga faɗa ta inda take shiga ba tanan take ɓullowaba. Ni dai dana gama cin sakwara saina miƙe. Bari in shiga ciki in ɗauro alwala inzo in yi sallah" Ciki na shiga na kama ruwa nai alwala. Sai kawai ma nayi sallata tunda yaran suna ciki sai murnar ganina suke yi. Fitowa nayi shago na tarar da wata mata suna maganar filaye da Uwani. "Kinga filin yayi sauƙi manyane dubu ɗari_ɗari aketa yankawa wallahi nan da shekara biyar wajannan cika zaiyi sosai. Shi yasa nace bari in sanar miki ko kina da buƙata ƙanina ne suke yanka wajan" Cewar wannan Mata kenan. Uwani tace. "To zan duba kuɗaɗen wajena, ko kuma zuwa karshen mako akwai dashi da zan ɗauka kuma da kauri ko guda biyu ne sai in siya in haɗe ai" Ai sai nayi carab nace. In babu matsala Uwani nima ai sai in siya tunda na siyar da shanuna kiwon yaƙi sai ciwo suke yi" Baki Uwani ta riƙe cike da mamaki. Numfashi ta sauke tace. "To babu damuwa Halima da daddare zamu zo in Bellon ya dawo sai muyi magana ƙawata zata siya. Wannan ƙawatace tun muna yara tare muka je saudiyya da'ita. Zan siya sai a bamu kusa da juna" Da wannan matar tai mana sallama akan sai ta ganmu zuwa daren. "Wai kiwon ma Hama ta hanaki kiyi sabida bata son kiyi arziki? Hmmm kingani ko Iyabo kinsan muguntar mutumin ƙauye kuwa? Yanzu da ba dan kina da wannan gidan ba da haka kuɗin zasu haɗu su galgance jibi asarori da kika tabka. Ni da ace iyakar karayar jarine da yanzu na ɗoraki da yardar Allah. To ba'a siyan komai ne a hannunki baƙin asiri mitsiyaciyar tayi miki na baƙin jini. To ince dai bata da labarin gidan da kike dashi ko?" Bata da labari, ko shi Hamma bai jima da sani ba. Hatta su Dada babu wanda yasan ina da gidannan. Wannan kuɗin dabbobinne ma Dada tace in samu in mallaki kadara. To Uwani kina ganin ko in siyar da ɗan kunne da sarkar da Saleem ya bani da wanda na siya a siya mun gida a sake zuba ƴan haya. Amman ke me kika gani. Inata ajjiye dasu su ba kawo mun kuɗi suke yi ba, ko babu komai hayar zatai mun amfani zan dinga karɓar kuɗina ina magance ƴan matsalolina. Amman meye shawararki?" Uwani tayi jim tace. "Magana ta domin Allah in kin tawo dasu ai gara a haɗa a siyar dukka, mu haɗa da ƴan kuɗaɗen dake jikinki, shima wannan gidan a siyar sai a sai babba ko da gidan samane, me ɗakuna da yawa. Kinga duk shekara zaki samu kuɗaɗe masu kauri a hannunki, zakita jalautawa. A ƙauye in kinsa zinare ma waya sani babu. Ai gara ace ƙasa gareki itace babbar kadarar da babu asara a cikinta, yaranki ma sai su gada duk da dai fulanin gadon shanayen wahala ake bar musu" Mun jima muna tattsunawa. Dab magriba Uwani ta kulle shagonta muka shiga ciki. Tuwo ta tuƙa mana dama tayi miyarta ta ɗanyen karkashi yaji ɗanyan kifi tun safe, ga yajin daddawa mai daɗi da take siyarwa, ga man shanu shima soyayye da take siyarwa. Uwani fa ƙaƙas ta zama ƴar kasuwa. Bayan munyi Sallah muka ci tuwonmu munata hira, sai naji rabi da kwatan matsalata kamar ta kau. Sai da mu kai Isha Uwani ta ɗebi kayan jajirai muka tafi gidan kishiyarta barka. Gidan duk ya fice a hayyacinshi yayi biji, biji. Da Sallama muka shiga ɗakin. Jaririyar sai kuka take canyarawa. Ashe ba kowa ne a ɗakin, ko ina uwar oho sai wan jaririyar yana zaune da ƙaton ciki sai gyangyaɗi yake yi. Uwani tayi haka zata ɗauko jaririyar a gado mai rumfa. Uwar jaririyar ta shigo da gudu ta riga Uwani ɗaukarta. Har tana sauke ajjiyar zuchiya. Wai ashe haka kishi, da kishiya yake?. "Tunda naji kukan yayi yawa nace ko wani abunne mugu ya sameta ashe kune. Sannunku da zuwa" Ta ƙarashe zancan tana dariya. Uwani ta dubeni, ta dubi kishiyar tata tace. "Mune mugayen da muka kusanceta kenan shi yasa take irin wannan kukan? Yayi kyau baki da laifi" "Lahh wallahi Innar Zainab ni ba haka nake nufi ba kar ki juya mun maganata dan Allah" Uwani zata kuma magana na taɓata ta baya. Wannan karon nako ci sa'a sai tayi shiru muka zauna. Ta bamu jaririya taƙi ta ƙanƙameta, daga ƙarshe saita cusama yarinyar mama. Wani shafaffen yanƙwanannen mama. Hafizu ne yayo sallama ya shigo. Ganinmu ne yasa ya washe bakinshi. "Iyabo ashe kun shigo. Ke basu jaririyar ki kawo musu abinci." "Tayi bacci ma" Ta faɗa. Uwani tayi dariya tace. "Kinga kwantar da'ita in tayi bacci. Abinci kuma ki bar abinki. Iyabo Jeka lo ( muje)" Miƙewa nayi, ledar dake hannun Uwani saita miƙa ma Hafizu tace. "Ga gumama asa ma takwarata" Ya amsa yanata godiya. Mu dai nan muka fito muka barsu, ya suka ƙare oho musu. Wai Uwani yadda kishiyarki ta ɗaukeki kenan baƙar muguwa? Kinji furucinta wai me yasa kishiyoyin kusan halayyarsu gudane, sai ɗaiɗaiku da suka rabauta?" "Rabu da matsiyaciya. Baƙin ciki nan take Hafizu na aiki a ƙarƙashina, da kuɗina ake ciyar da'ita. Da bini_bini zata biyoshi har shago wai tazo ganinshi. Tasa na sallameshi da ƙyar na dawo dashi, da sharaɗin matarshi karta kuma zuwa nemanshi. Ko gidan biki ko suna haka na maƙota dana shiga sai ta sha jinin jikinta. Ni nafi ƙarfinta da ba dan haka ba wannan ƴar ƙauyan juyanu zata yi kamar waina. Shakkarta fa shi kanshi Hafizun yake yi, damma yasan ba kyau ba daɗi ni ɗin, shima da tsiyar zai tatamun ta su rijalu." Washe gari Sassafe muka wuce asibitin murtala, bayan bin dogon layin awo. Bata fa sauya zani ba, magana guda ɗayace. Bani da ciki su basu ga komai ba. Hankali saiya tashi fiye dana ko yaushe. Danni abinda nasa a raina shine a Adamawa akasi aka samu, bana jin asibitocin Kano indai dan ƙwarewa ne. Munbi asibitin kudi huɗu a ranar wallahi zancan ɗayane. Kafin yamma idanuna ya faɗa na yi wata rama ta fatat ɗaya. "Iyabo gobe zamu buga sammako zuwa lahadin makoli wajen mai maganin dana faɗa miki. Muje da izinin Allah zamu dace, kuma a dage da adda'a " Kayya Uwani, ni ina ganin mu haƙura da zuwa wani gidan magani. A asibiti ba'a gani ba sai a wajen mai maganin hausa ne za'a gani? Allah yana ji yana gani shi zai bani mafita." Uwani ta dafani tace. "Bazan hanaki kuka ba. Wallahi nima dauriyace tasa ban zubar da hawaye ba. Amman fa Iyabo kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa. Ni dake a asibiti muka ga dunƙule magani a cikin abinci. Amman idanki ya rufe Hamma kawai. Alhalin ya kamata ace ki duba waye abokiyar zamanki shima yana da mahimmanci. Matan katsina, Sokoto, zamfara, Maiduguri me yasa zaki ga in akaji dasu za'a haɗa kishi sai kiga an tashi hankali? Sabida waɗannan garuruwa dana lissafa sunyi ƙaurin suna wajen kassara kishiya, da mugun dumi suke ɗaukar sha'anin kishi. ( Kuyi haƙuri ba duka ake nufi ba, mafi yawancin ƴan garuruwan da aka ambata haka suke. Amman akwai da dama waɗanda ba haka suke ba. Kar a mance labarin na gaske ne ba ƙirƙirarshi akayi ba) Iyabo mun kama laya a cikin fulonki, muka so ni da Baɗɗo a nuna ma uwar mijinku. Amman kika ƙi waike kaza ke kaza kar aurenta ya mutu. Ba gara aurenta ya mutu ba akan ta tarwatsa rayuwarki. Zuchiyar bafulatani fa tauri gareta basa jin kira. Yanzu jibi a cikin dare dubu ɗari da ɗayan data saki, baki mutu ba alƙiyamarki ta tsaya. Ga ciki yana motsi, yana girma amman ba ciki bane" Kukana ne ya sake tsananta, ina ganin meye laifi danna zaɓi in rayu da sanyin idaniyata. Soyayyar da nake ma yaya Hamma ta wuce gaban kwatance, dan ko mayyace Hama bazai sa in janye aurenshi ba. Ganin kukana yayi yawa ga dare ya raba Uwani taita rarrashina. A daren ranar bacci banba, ni innaji cikina yayi motsi sai tsoro, dan bansan dame nake rayuwa a ciki ba. Washe gari ni ko wanka banyi ba muka wuce, da ƙyar da suɗin goshi Uwani tasa nasha kokko da ƙosai biyu muka wuce. Motar Karamar hukumar warawa muka shiga, daga warawa muka hau akori kura zuwa Ƙauyan Lahadin makoli. Daga lahadin makolinma saida mu ka yi tafiyar ɗari bibbiyu a Acaɓa. Tafiyar ɗari biyu a ƙauye bafa ƙaramar tafiya bace. Sai gamu a wata bukka da mata masu ciki zuzzube a ƙasa. Wasu cikinsu ya kusan haihuwa, wasu kuma cikin kamar dai nawa, wasu ma cikin bai kai nawa ba. Layi Uwani ta kama mana, muka samu mu kai azahar, ta siya mana ɗanwake da mai da yaji. Ni bakina ma ɗaci yake yi da ƙyar dana sa ɗanwaken a bakina na haɗiye. Uwani dan Allah ki rabu dani da abinci. Ki barni inji da damuwata" Murmushi tayi tace. "Ki yarda da Ubangijin daya kuɓutar dake daga hannun larabawannan da suka nemi ranmu. Ki kuma yarda da ubangijin daya taimakeki kika auri Gwadabe a lokacin da duk wanda ya kalli alaƙar cewa yake bazai yiwu ba. Ki yarda da ubangijin daya ƙadarta miki auren Hamma har kika shiga wannan halin. Ki yarda zaki samu taimako daga gareshi. Iyabo nasanki da tawakkali da ɗaukar komai ba komai ba. Amman naga wannan lamarin kin ɗaukeshi da matuƙar zafi. Kici abinci kar ki kashe kanki" Wallahi maganganun Uwani sai suka wanke mun kai. Wani tawakkali ya sakko mun. Murmushi nayi nasa hannu na karɓi ɗanwaken na cinye tas na sha ruwa. Na dubeta nayi murmushi. Itama murmusawa tayi. A haka har layi yazo kanmu. Mu huɗu muka shiga masu ciki, sai Uwani ta biyar. Ta farkon itace ta soma bayaninta, wanda ya gigita tunanina. "Malam shekarata uku ɗauke da wannan cikin. Ni ban haihu ba, ni ban huta ba Malam. Naje wajen masu magani iri daban_daban amman ba'a dace ba Malam. Kishiyata ce ta biyun taimun baki a lokacin da mijinmu yake rawar ƙafar na samu ciki yana saka