Sashe 27
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko gidan naje mutuncina zasu ci har gaban abada ƴan uwanta ba zasu ƙaunaceni ba" Bara'u yayi murmushi yace. "Baiwar Allah mai wuyar wucewa. Muma muka kasa mance halacci da Alkhairan Iyabo balle kai da dominka muka santa. Abinda za'ayi shine in ka huta zamu shiga mu nemo duk inda Uwani Tabalbalin take muji labarin Iyabo, mu ajjiye mata saƙon gaisuwa. Zancan abota Gwadabe tunda zamu haɗa yaranmu aure ai zumunci zai ɗore, fatana Allah yasa kar silar auren zumuncin namu ya samu tangarɗa." Haka dai hirar wannan abokai ko Aminai yaƙi ƙarewa, gida suka shiga suka kai musu naman da suka siyo Hadiza da Sakina sai hirarsu suke gwanin sha'awa. Su kuma suka ɗauki abincinsu suka fita dashi waje yara suka kawo musu tabarma da fululluka dan a ƙwar gidan zasu kwana. Washe gari. Da safe Gwadabe yasa Hadiza ta cicciro tsarabobin da yayi ya cire na Sakina da yara, ya cire na Bara'u. Na gidansu Shafa ma ya cire ya ajjiye a gefe. "Wannan in Sakina zata kaiki gidansu Shafa sai ki tafi musu dashi ko, wannan kuma na gidanmu ne" "Dama nice zanje ni da nazo garinsu? Aina ɗauka itace zata zo ko?" Ƙur yayi mata da'idanu su biyu ne a ɗakin ta gamama Ummi wanka kenan tana mata nabkin. "Kiyi abinda nace miki a matsayina na mijinki. In kuma ban isaba to sai ki zauna. Kar Sakina ta kaiki gidanmu tukunna dan su Babala basa nan." Baki ta zunɓuro tace. "Amman ai ita....." "Ya'isa haka Hadiza. In baki bi umarnina ba zan saɓa miki mai taurin kan tsiya marar jin magana baki da aiki sai ƙorafi mtwssa Yaja tsaki ya miƙe ya fice. "Gwadabe munga tsaraba fa Allah yasa a mizani, Allah ya bar zumunci" "Sakina kenan baki da dama. Bara'u muje ko?" Bara'u yace. "To muje. Sakina gidan Zulƙi zan kai Gwadabe yaushe rabon da'a gana" "Allah sarki, sai kun dawo kwa gaishesu. Muma da mun kammala zan zazzagaya da Hadiza duk gidan daya dace dai. Gida kuma Babala bata nan inta dawo wannan aikin naka ne banma isa na kai Hadiza wajen Babala ba" Da haka sukai sallama zuwa gidan Zulƙi. A harabar tabkeken gidan nashi suka zauna a wasu fararen kujeru me gadi ya shiga sanar mishi da zuwan na Bara'u. Bara'u ba baƙon gidan bane an saba ganinshi hatta ƴan sandan dake tsare lafiyar Zulƙi sun sanshi. "Rigiji gabji lallai Zulƙi yafa samu duniya ji gida ma malam, ji ma'aikata da masu tsaro, ga motoci har uku." "Bafa kaga komai ba Gwadabe bari dai mu shiga cikin falon ka gani" Me gadine ya ƙaraso inda suke yace. "Hajiyar gidan tace a muku iso zuwa falonshi. Bacci ya tashi yanzu wanka yake yi zai zo ya sameku inya fito" Tiryan_tiryan suka bishi har zuwa masauƙin baƙinshi inda anan yake zantawa da baƙinshi irin masu unguwa, mai gari, da hakimai, da dakatai" Masu aikin girki suka kawo kulolin abinci da filas na shan shayi da kofuna. Gwadabe sai karema falon kallo yake yi. Yana mamakin wai wannan gidan na Zulƙi ne" zamansu baifi da minti talatinba sai gashi ya shigo yana saye da shadda wagambari ɗinkin tazarce. Baki ya buɗe ya nuna Gwadabe da yatsanshi yace. "Gwadabe yau kaine a gidana, to yaushe ma ka shigo garin?" Da sauri Gwadabe ya miƙe suka tafa da Zulƙi suna dariya gami da farin cikin ganin juna yaushe gamo. "Ranka shi daɗe ashe rai kanga rai?" Zulƙi yayi dariya suka zazzauna yace. "Bara'u kaji ɗan iska waini yake kira da ranka shidaɗe. Ni Gwadabe kaida kake tare mun faɗa nine ranka ya daɗen?" Dariya suka saka Bara'u yace. "Ai Zulƙi ba zaka canja ba. Wai kai baka mantuwane dan Allah?" "Ba komai ake mancewa ba Bara'u. Gwadabe ai mutumne harda ɓari kai ka sani da sauran abokanmu da muka taso tare. Gwadabe wanne aiki kake yi? Bara'u dai ya tsokatamun matanka biyu kuna zaune a nijar gidan Baba Magaji wan Babala" Gwadabe yace. "Hakane matana biyu. Sana'a anata buga_buga inayin haƙon zinare. Ina tallar magungunan karfin maza na gargajiya dana bature. Kaga irinsu" Gwadabe yasa hannu a ajjihu ya ɗauko wani ƙullin magani guda biyu, dana bature sacet ɗaya. Baki Zulƙi ya buɗe yace. "Kusun uwa tafi da gidanka kenan. Gwadabe kaine ka zama mai siyar da maganin maza?" Sunfi minti koma sunata ƙyalƙyala dariya kamar waɗanda suka ga wawan zama. Gwadabe yace. "Wannan in ka zuba a tuwo kaci yajinnan Zulƙi ko kakai shekara saba'in saika dawo ɗanyen jini a wannan ranar, da miyar yauƙi ake ci. Wannan kuma na baturene shayin maza ne. Ka juye a kofin shayinka ka shanye ranar ba'a magana. Gana dattin mara, amman shi yana sa gudawa sassafe kafin aci komai ake dafawa a shanye da tuƙarshi. Ka jarraba amfani dashi zaka samomun kostoma" Bil haƙƙi Gwadabe yake musu bayani. Su kuma sai kwashewa da dariya suke yi. "Ikon Allah kenan. Gwadabe zan jarraba in naga kyanshi niko zan haɗaka da manyan mutane" "Yauwa ni dama abinda nake son ji kenan. Ya batun iyali Zulƙi, kuma wai ina katafi yawon duniya ne?" "Iyali sunanan an tara. Na jima da yin aure yaranmu shida da matar dana aura a bariki ƴar garin bayalsa ce, tana da yare. Sai bayan na hau kujerar mulki saina auri yarinyar ƙanwar Babarmu, sun matsa ni bama sonta nake yi ba, dan Jenifa ta taimakeni sosai a rayuwa. Can Bayalsa na yada zango. Dakone kwasar shara, kwata. Gwadabe babu sana'ar da bamba har Allah yasa na auri Jenifa to mahaifinta ɗan siyasane babba. A wajenshi na koyi harkar siyasa shi ya wanke mun kai yace ai zan iya komawa ƙauyanmu in shiga takarar chiyaman tunda ina da takaddar gama sakandare. Shine ƙashin bayana, Rabo kuma chiyaman daya sauka saiya tsayar dani na zama ɗan jam'iyyarsu kaji abu kamar wasa ko?" Kai duk sukaita jijjigawa, dan shima Bara'u yaune yake jin wannan labari" Gwadabe yace. "Yaya kake fama da Jama'a amma?" Sakkowa yayi yace. "A zuba abinci muna ci ina baku labarin wahalar dake cikin kujerar mulki." Dariya su ka yi. Sunsan Zulƙi tun yana yaro da zaran rana ta take lokacin cin abinci yayi ake nemanshi a rasa. Bara'u ya bude kular abincin ya juye masar dake ciki dukka a faranti, ya kwarara miyar masar akan masar ya yaryaɗa musu man shanu isasahe. Duk yayi muku komai suka tsoma hannu, saida Zulƙi ya kai noma biyar kyawawa kana yace. "Kujerar mulki bata da daɗi Gwadabe sam. Hakkin al'ummar yankunku akanka kai shugaba ya rataya. Kowa jira yake kahau ya kawo maka buƙatarshi, kuma fa dole yake nufin wannan buƙatar ka biya mishi. Yanzu tafiyar da nayi akan yadda za'a samun hannu a takaddar tallafama manoma da taki ne. Satina fin nawa ina sunturi, masu ruwa da tsakin sunƙi sa hannun." Ya dinga basu labaran yadda abubbuwan suke tafiya, da yadda haƙiƙanin siyasa take. Sunfa jima suna hira a wannan gida basu ankara ba suka soma jiyo kiran sallar azahar. A banɗakin falon su kai Alwala sun fito harabar gidan Zulƙi ya shiga ya kira yaranshi maza uku suka wuce masallacin dake manne a jikin gidan ta waje. A cike masallacin yake sosai kundai san jama'armu basai an karashe ba. A cikin masallacin Sai ga ƙafa da kafaɗun Gwadabe manne dana Yaya Hambali. Duk su biyun basu lura da hakan ba har saida gwadabe ya kalli ƙafar ya gane wannan ai kafar Yaya Hambali ce. Da sauri ya ɗago ya kalleshi a lokacin har an yi kabbara. Idanu suka haɗa wani irin kallon tsana Hambali yake jefo ma Gwadabe idanunnan nashi cike dam da farin kwalli kamar yadda ya saba, a yanzu ma yafi rambaɗawa sabida ya samu wadata. hannu yasa ya jawo wani saurayi daga sahun gaba ya sashi a gurbinshi, shi ɗin ya koma sahun gaba. A sanyaye Gwadabe ya ɗaga hannu yace. "Allahu Akbar" Jikinshi sai rawa yake yi dai, haka gabanshi yake ta faɗuwa har aka idar da sallar. Kallon saurayin dake kusa dashi yayi sai yaga Ashe Nazifi ne babban yaron yaya Hambalin. Sauke kai kawai Gwadabe yayi baya ma so ya kallesu zuchiyarshi ta idasa karyewa. Shi dai yana gefe a zaune Zulƙi yanata gaggaisawa da jama'a. Ya jima sosai kafin ya samu kanshi ya ƙaraso inda su Bara'u suke jiranshi. Gwadabe yana ganin yadda Yaya Hambali yake ta girmama Zulƙi. Yayi ƙiba ya sake kyau na musamman, fatarshi ta murje shi da Zulƙi suka saje. A gaban idonshi suka fita shi da Nazifi. "Kuyi haƙuri na barku. Haka muke fama da jama'a, kuma dole kabi dasu inba haka ba sai zagi da cin mutunci. Kuzo muje can gidansu Baba mu gaishesu* Dunguma suka yi gidansu Zulƙi aka gaggaisa akai zumunci. To su dai a gidan suka rabu dashi akan sai Gwadabe ya kawo matanshi sun gaisa. Suna tafe suna tattauna abinda ya faru a masallaci sai gasu a ƙofar gidansu. Babala na daga ta cikin ƙofar gidan, Yaya Halima da Yaya Hambali suna daga ta waje. Gabaki ɗaya sai guiwowinshi suka sake ya tsaya cak shi bai jeba shi bai wuce ba. Kallon kallone ya shiga tsakaninshi da Babala na wasu sakanni. Ganin Babala ta ƙurama waje ɗaya idone yaja hankalinsu Hambali suka juya. Daidai lokacin da Bara'u yake jayeshi. "Ka daure kayi ƙoƙarin cinye jarabawarka Gwadabe" "Daya daure da kar ya daure duk ɗaya. Tsiniwace a kanshi ai inya tako mana gida. Tuni muka tsame matsiyaci a cikin zuriyarmu. Karka sake matanka ko wata banzar tsarabarka ta shigo gidannan. Dan naga Sakina na zagaye da iyalanka" Cewar Yaya Hambali kenan, cikin ihu da ɗaga murya yake maganar tashi. Kuka Gwadabe ya fashe dashi Bara'u ya jashi suka koma gida babu ma kowa a gidan a tsakar gida suka zauna jigum_jiugm sunata jimantawa juna. Har akayi kiran sallar la'asar babu wanda yace da wani uffan har suka fito daga masallaci. A gindin bishiyar mangwaro suka zauna akan kututture. "Gwadabe kayi haƙuri ka ƙara. Uwa ba abun wasa bace, ka kiyayi Babala karka cuci kanka taima baki. Tunda bata son ganinka ni kam in dan ta mune karka sake kawo mana ziyararma wallahi mu mun yafe Gwadabe ka zauna zamu dinga zuwa duk ƙarshen shekara " Gaga_gaga haka wunin ya kasance musu. Sai yamma suka samu shiga gidansu Shafa a tsakar gida