← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 72

Sashe 66

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

IYABO:. Harda lemun kwalba kiret biyar suka tawo dashi da gararsu riƙi_riƙi. Buhun shinkfa, garin Amala, wake, doya, manja, harda soyayyar jar miya aka tawo mun da'ita. Ga suturu ɗinkakku da aka kawomun Burodami Debisi ne yasa duk aka ɗinkamun kayan tas, ga takalmi ƙafa biyu ga su ɗankunne da sarƙa, ƴan biyu ma sun sha kaya, ni dai dana gansu naga kayan da suka kawo sai kuka kawai Anty mulka tace. "Ki dena kuka Iyabo wannan shine zumuncin ai. Kinganmu har anko muka yi wanda zamu saka ranar suna. Sai dai kin rame kin mugun lalace sai kace ba ke ba, wani abun akeyi miki a gidan. Ko kuma matsalar miji, ko kishiyane?" A jejjere tai mun tambayoyin duk sun kafeni da idanu suna son jin amsar bakina. Sai Bose tace. "Dole fa kiga ta lalace a ruga fa take aure. Jibi a irin gida da ɗakin da take rayuwa, kuma ita ta zaɓarma kanta zaman" Hararar dana doka mata ne yasa tayi shiru. Babu komai Anty Mulka nayi ciwo a cikinnan. Laulayin da ban taɓa yin irinshi ba nayi. Amman lafiya lau nake zaune da mijina, kishiya ita kuma zaman haƙuri akeyi da juna" Su Taiwo da Kahinde ne suka shigo da gudu da yaran Kari. Iyaa Baji tace. "Waɗanda ba yaranki na wajen tsuntsun soyayya bane? Harma yasan a inda kike aure kenan? Ahhh Ahhh Iyabo" Uwani ce ta ƙwaceni ta hanyar mu su bayanin yadda akayi, shine suka barni na sarara. Babu laifi sun samu tarba mai kyau daga wajen Yafendo, Dada ma ta ƙuƙuta tayo musu farfesun kaza an aiko musu dashi. Maƙota sai zuwa gaishe da baƙi suke yi, anata zuwa gulmar irin kayan da suka tawo dashi. Hama ma ta shigo tako daɗe sosai a ɗakin tafi awa saida ta gama ƙarema kayan da suka tawo dashi kallo tas kafin tai musu sallama ta nufi madafi kuma. Washegari ranar suna yara suka ci sunansu da suke zuwa dashi Hassan da Usaini. Tun asussubar fari su Anty Mulka suka shiga hura murhu aka ɗaura tukwanen girkin suna. Maƙota suka cika gidan dam jama'ar su Baɗɗo da Dada, da jama'ar shi Yaya Hamma. Dan kab matan abokanshi saida suka shigo taya aiki. Ta ɓangaren mazan gidan suna daga gefe anata aikin fiɗar ragunan suna, Uwani tana bakin rijiya ita da Bose suna gyaran kayan ciki. Ni kuma ina daga ɗaki ina saka kaya. Farin lace ɗin da Iyaa Debisi tayi mun shi na saka ɗinkin buba da zani na fito shar dani gashi nayi muguwar rama ta mamaki hatta mazaunaina da nake gadara dasu sun sace kaɗan ya ragemun. Sai nayi haske fuskata tayi fayau da'ita ga kitso nasha ga lalle na salateb an rangaɗamun. Ina sanya ma su Hassan kayan da Burodami Debisi ya siya musu yace a sanya musu suci suna. Sai ga Yafendo ta leƙo ɗakin Safiya na riƙe da ƙaton bahun shaƙe da kayan dangin maza, saida sukaimun turamen zani ashirin cib, ƴan biyu kuma sunsha rigina masu hangar roba da masu hangar ƙarfe, omo da mandula da nabkin Kam mun samu da wasu wando me kala kala na yaran fulani. Da wata riga mai ruwan hoda, bulu, yallo. Nasan kun ganeta duk uwar da tayi renon ɗa shekaru ashirin baya ta san wannan riga da wannan wandon. "Jabu ga namu kayannan babu yawa ayi haƙuri, yanayin garinne kinga anyi annobar Dabbobi an samu karayar arziki sosai" Murmushi nayi . A raina ina tuno haihuwa biyu da nayi a gidan Gwadabe, a leda ake kawomun kayan dangin miji shima a wulaƙance. Nagode sosai Yafendo mai yawan kenan ai. Dama yanzu nake son in gama a fitar da kayan da su Bose suka tawo dasu ma. "Ki barshi in Adda Daso ta kawo na wajenta sai a saka a bawo biyu a fito dashi a shimfiɗa tabarma haka muke yi. Tubarkalla kunyi kyau ke da yaran. Naga yayyensu ma suna tsakar gida duk anci kwalliya" Murmusawa kawai nayi ta saki labule ta koma ɓarayinta. Ina gyara ɗaurin ɗankwalina saiga Kari da Cubu da kaya niƙi_niƙi a buhu sun shigo dashi, daga ɓarayin Yafendona suke saida aka kai mata sannan tace a kawo mini. Uwani ce ta shigo. "Iyabo wannan man kamar bazai isa ai suyan kayan cikinnan ba gaskiya. Ahh cancaɗi kaga Amarya a gidan Hamma. Kai inama angon ƙarnin yananan zanso ganinshi a wannan rana" Dariya nayi dan ta sosa mun inda yake yi mini ƙaiƙayi. Tun a daren jiya nake kewar rashin mijina a tare dani a lokacin da nafi buƙatarshi. To kafinnan Uwani zo kiga abubuwan arziki da aketa samu. Sannan a sakasu a bawo a fitar tsakar gida kamar yadda suke yi a al'adance" Nan Uwani sukaita jejjera kaya, ta ɓangaren Dada ma masha Allah ƴan biyu sun samu kaya sosai. Bawo uku aka fitar shaƙe da kaya. Nan maƙwabta akaita tururuwar zuwa ganin kaya. Da bakinsu suke labarin tunda ake haihuwa a rugar babu mai jegon data kaini goshi. Hama kuwa kamar zata haɗiye zuchiya ta mutu ta huta da baƙin ciki. Jallof ɗin shikaface sai zoɓo da Amala da miyar ewedu da miyar tumatur da taji ganda. Dan tafi da gidanka su Iyaa Beji suka yi na bushasshiyar ganda, tun jiya da dadare aka jiƙata cikin bokiti da ruwan zafi. Maƙwabta akaita bi da abincin suna, gidan sunan cike da yara da manya, kowa ka gani abinci da lemun kwalba yake ci. Ina cikin matan abokan Yaya Hamma suna bani tasu gudunmawar, mai atampa, mai omo, mai kayan yara, masu miƙo kuɗi nayi sai ga Hama ta shigo babu ko sallama. Ganin na canja kaya nasa atampa me kyau dinkin ya zauna sosai a jikina saita sake ɓata ranta. "Danginane abincin da aka bani bai ishesu ba. Ga kula a zubo musu. Mutum biyu basu samu lemun kwalba ba sai zoɓo" Kular hannunta na karɓa na miƙa ma Uwani dake zuzzubama jama'a abinci. Babu musu ta cika mata kular tab da jalob ta ɗaura mata kayan ciki. "Gashi lemun kwalba ne ba zasu iya samu ba. Kinga waɗannan lemun kwalbar da masu shi, suyi haƙuri da zoɓon da suka samu ma" Cewar Uwani kenan. Hama dai ganin idanun abokan Hamma sai tace. "Ai babu komai Uwani. Hakanma mun gode" Ta karɓi kularta ta fita ɗaya daga cikin matan abokan Yaya Hamma sai kurantata take yi tana cewa tayi kyau wannan kwalliya haka. Haka dai wannan suna ya gabata sai yamma lis kowa ya watse, akabar ƴan gida da wanke_wanke. Tare duk aka haɗu akayi wanke_wanken ragowar abinci daya rage kuma matan gida duk suka ɗebe ko wacce tana faɗin ta huta da ɗaura tuwon dare. Sai bayan isha su Uwani suka kammala aikinsu tsab. Uwani ta shigo da banƙararrun ragunan da aka rataye a tsakar gida. Waɗannan ragunan fa Uwani" "So kike a bari a waje a sace? Uwargidanki tun magriba take sunturi a lungunnan kuma duk wucewa sai ta kalli ragunan taja ƙwafa na jima ina lura da'ita. Yanayinta kaɗai ya nuna ba mutuniyar arziki bace. Cewar Anty Mulka. Dariya nayi nace. Yanzu saita ɗauki rago to ta kaishi ina? Uwar harara Uwani ta doka mun, nayi mata dariya kawai. Washe gari duku_duku su Iyaa Beji suka tashi da suyar rago. Su Baɗɗo kuma sunata kiciniyar haɗa musu karim kumallo. Yafendona ce ta juyo ruwan wankan yara, nima ta kai mun nawa. "Maza Jabu je kiyi wankan kar ruwan ya huce" Mayafi na ɗauka na fito. A ƙofar bukkata na tarda Taiwo da Kahinde suna zaune suna kuka. Kallonsu nayi tausayinsu ya kamani, tsugunnawa nayi a kusa dasu. Na shiga rarrashinsu na samu su kai shiru nace su shiga ɗaki su kwanta a kan gado. Ai kuwa babu musu suka tashi suka shige. Murmusawa nayi nabi bayansu da idanu. Hawaye suka taru a idanuna. Wallahi barin yara a wani gidan babu daɗi. Kuma duk yadda mace takai sai yarannan sun mance da'ita kuma zasu kasance babu wannan shaƙuwar ta ƴaƴa ga mahaifiyarsu. A hakama Gwadabe yayi namijin ƙoƙari sosai da har ya aiko a kawo mun yaran. Da ƙyar naja ƙafata na shiga wankan, ban jima ba na fito, na samu Yafendona tana yima ƴan biyu rawa sunsha fararen ovaroll sunyi kyau yara kamar yaran Turawa. Kan gadona na kalla Taiwo da Kahinde sunyi baccinsu sai ajjiyar zuchiya suke saukewa. Haka aka soya namannan guda ɗaya surutum Yafendo tace a ciremun ɗayan ragon suka kasa kashi huɗu. Ɗaya nasu Yafendo da mutan gidan. ɗaya na Dada da ƙannena. Ɗaya na maƙota, sai ɗayan na dangin Babana. Yafendo tace in dibarma Hama a nawa, an kuma bata kai da ƙafan rago ɗaya, ɗayan da safe shi aka dafe mun naci. A leda na ƙulla mata na tura yara suka kai mata. Nayi tunanin ba zata karɓama ma sai kuma ta karɓa. Na ƙarama su Iyaa Beji a nawa da Uwani. Washegari su Iyaa Beji suka kama hanyar Kano. Uwani dama tace saita yi sati guda kafin ta koma. Wata ranar alhamis muna zaune a tsakar gida ni ina wanki, Uwani na yi mun kwalimar ɗakina saiga Hama ta fito da jaka niƙi_niƙi da yara wai gidansu zata koma ita acan zata haihu taci gaba da zama har sai Yaya Hamma ya dawo. Kai kawai Yafendo ta girgiza tace. "A sauka lafiya. Ni bazan hanaki zuwa gidaba tunda wanda kike zamanshi bayanan. Amman ki ajjiye yara a gidansu suci gaba da zama a cikin ƴan uwansu. Jabu ki karɓi yaranki kici gaba ds da riƙesu har zuwa sanda zata dawo." Bafa haka Hama taso ba. Cikin fishi ta ajjiye jakar yaran tayi ficewarta tana maganganu marasa daɗi. "Allah ya shirya. Jabu kici gaba da haƙuri nima kaina haƙurin nake yi da Hama. Tunda dai aka auroki gabaki ɗaya kafatanin halayenta suka sauya. Babu komai Yafendo. Ku kuma kuzo mu shiga ciki ko?" Na tattare yaran muka shiga cikin ɗakina dasu. Ana gobe Uwani zata tafi da daddare na tattaro mata kayana atampopi kusan kala goma cib nace duk ta ɗinka mun inna tawo sunanta sai in tawo dasu. "Ki haɗo da waɗannan rigunan masu zubin ƴan ƙauye dukka sai in shiga kasuwa a yi canjin kasuwa in zaɓa musu masu kyau, tunda naga kin samu dayawa" Ai kuwa kin kawo shawara me kyau." Tattaro mata nayi kusan
Chapter 66 · 0% Book details