← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 72

Sashe 14

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Robar ƙarin ruwane ɗaure a hannun malam, numfashinshi yana sauka da hawa a gurguje sosai. Daktar ne tsaye a kanshi yana ma ƙarin ruwan dake ɗaure a hannun malam allura. Tasi'u da Jamilu ne a kusa da malam kusan a tsaye suka kwana akan malam. Iyayensu kuma a zaune a ƙofar ward ɗin suka kwana ciki harda Baba Suwaiba wacce ta zama itace ummul aba'isin faruwar komai. Kafin ƙarfe bakwai na safiya iyalan Malam kab sun hallara, ko wacce uwa na zaune a gefe guda da bataliyar yaranta a gefenta. Tsakanin Amaryan malam, Baba Suwaiba, Baba asshi babu komai face harara da jan dogayen tsaki. Yaran maza da mata sunyi tsit kamar ruwa ya cinyesu kowa da tunanin da yake yi. Buɗe ƙofa akayi gadon jan marasa lafiyane ya fito malam na kai baisan a wacce duniyar yake ba. "Ina za'aje dashi wannan yaron?" Baba Fhatsima ta tambaya a tsorace. Hawaye Yaya Tasi'u ya share yace. "Na nemi a sake mishi ɗakine, sannan Malam yana bukatar adda'ar matanshi da yaranshi. Auwala ku haɗu dukkanku ban ware kowa ba aje a sauke ma malam Qur'ani ayi sadaka." Hawayenshi ya kuma sharewa yabi bayan ma'aikatan jinyar a baya. Jamilu kuma ya tsaya tattsunawa da uwarshi da ƙannenshi. "To ai kowa yaji abinda Babban wa uba yace. Sai mu tafi ai ko?" Cewar Auwala kenan. Buɗar bakin Muntari sai cewa yayi. "Ni babu inda zani, ku dai da kuke tunanin Malam ku kaɗai ya haifa, kuma uwarku mowace sai kuje kuyi mishi" Yinƙurowa Auwala yayi kan Muntari da zafin nama. Da sauri Baba Suwaiba ta miƙe ta shiga tsakankaninsu. "Kul Auwala karka sake ka tayar mana da fitina a wajennan. Ka barmu muji da bala'in da uwarku ta jefani a ciki. Saukace dai yace bazaiyi ba ku da kuke jin zaku iya kuje ga hanya" Saroro yaran suka yi suna kallon Baba Suwaiba. Ɗaya bayan ɗaya suka shiga zamewa suna ficewa. Banda yaranta su suna zaune tare da'ita. A mota Hadiza sai kuka take yi na baƙin cikin irin zaman da akeyi a gidansu. Wannan rayuwa da muni take, Malam na da rai ma kenan kai yaƙi haduwa ina ga Malam ya bar duniyar kuma, yaya gidan zai kasance ina makomar zumunci tsakankanin ƴan uwan junan?" Gwadabe ya dafata yace. "Hadiza wannan kukan ya isheki haka. Malam adda'a yafi buƙata, Allah zai tashi kafaɗunshi." Auwala dake gaba a zaune ashe shima hawayen yake yi yace. "Ka barta ta koka irin rashin haɗin kan gidanmu Gwadabe. Nima kukan nake yi, ace mahaifinka yana kwance rai a hannun Allah. Amman kai bata lafiyarshi kake yi ba. Kaji fa abinda Muntari yake faɗi. Kaji irin goyon bayan mahaifiyarshi. Me Malam yayi daya cancanci irin wannan hukuncin daga diyoyinshi?" Idanu Gwadabe ya lumshe, rayuwar gidansu na haskawa a kwaƙwalwarshi da irin tsanar da ƴan uwanshi suke mishi,hatta Babala bata fatan ta buɗe ido ta ganshi. Ai halin da yake ciki akan danginshi yafi nasu ciwo. Matsalolin ƴan uba abune sananne wanda yazo a cikin tarihin Annabi Yusuf da ƴan uwanshi suka zaɓi jefashi rijiya, sabida ƴan ubanci, da zafin nuna fifiko" Amman tashi matsalar mai rikitarwace sosai" "Auwala ayi haƙuri komai ai mai wucewane wata rana sai labari. Duk daren daɗewa abubbuwa zasu zo suyi sanyi kuma su warware. Fatanmu Allah ya ba Malam Lafiya" Haka suka ci gaba da tattauna manyan matsalolin gidan har suka iso gida. Ayau dai su Sabitu babu fitina har aka kammala saukar Qur'ani kasancewar tare da manyan gardawan malam aka haɗu akayi sai abun bai ja lokaci ba aka kammala. Su Auwala ana gamawa suka sake komawa Asibitin. Su Hadiza kuma suka tsaya girkin abincin da zasu kai asibitin. Sha biyun rana Hadiza ta gama lafiyayyen tuwon shinkafarta miyar kabewa yaji naman rago. Ta jera komai a babban basket ta fito. Daidai fitowar Shafa itama a shirye take tsab tanaso zata bi Hadiza asibitin taga halin da me jikin yake. Tare da Anti Badi'a suka dunguma suka tafi. Acan suka tarar da Matar Jamilu. A wajen wata baranda suka shinfiɗa kapet huɗu, ko wacce mace da yaranta mata da ƴan uwanta. Haka abinci ma kowacce nata dana jama'arta daban sabida tsabaragen rashin haɗewar kai. Sai da yamma Yaya Tasi'u ya leƙo yace. "Baba kizo Malam ya farka sai ambaton sunanki yake yi." Da sauri Baba Fhatsima ta miƙe, Baba Asshi ma ta miƙe ta bi bayan Baba Fhatsima" "Baba kaɗai yace yana son gani. Dan Allah Baba Asshi ki koma kar ganinki ya ɓata mishi rai" Cewar Yaya Tasi'u, cikin girmamawa yayi maganar. Ita kuma cikin hargowa tace. "Ko tare da uwarka kake yawo baka isa ka hanani shiga ɗakin mijina ba. Kisa ya sakeni kamar yadda kikai sanadin fitar Suwaiba" Ta dubi Baba Fhatsima tana harararta. Murmushi tayi kawai. Ta girgizama Yaya Tasi'u kai halamun yai shiru. Tare su ukun suka shiga ɗakin da Malam yake kwance. "Asshi kar ki shigo inda nake. Ban kiraki ba bana buƙatar ganinki. Tasi'u ka fita da'ita in dai ba kana daga cikin masu son in mutu suci gadona bane" Turus Baba Fhatsima da Baba Asshi sukai a tsaye a ƙofar ɗakin. An rasa me shiga, da me fita. "Bakomai Malam, ba dai ni ka jefa da wannan furucin ba? Daga ni har ƴaƴana babu wanda zai sake tako ƙafarshi yazo dubaka. Da sakina kayi na huta da baƙin cikin Fhatsima data kwashe shekaru tana ƙunsa mun" Tana gama faɗar haka ta fice da kuka nan ta tattare kan yaranta tana kururuwa suka fice daga asibitin. A ranar ta sanar ma ƴaƴanta duk wanda ya sake shiga harkar Baba Fhatsima da yaran ɗakinta bata yafe mishi ba. Wannan dalilin ya zama tsani na ƙullatar Baba Fhatsima da yaran ɗakinta. Baba Asshi ta haddasa gaba mai ƙarfi a tsakankanin yaranta da ƴan uwansu. Ƙafarsu bata sake taka asibitin ba har Malam ya kwana shida a asibiti jikin yayi kyau aka sallamoshi. Ko da aka sallameshi Baba Asshi da yaranta babu wanda yaje ya duba malam da jiki harkokin gabansu kawai suke yi. Ta ɓangaren Baba Fhatsima da Malam kuma. Haka taita tausarshi tana kwatanta mishi ba'a gyara ɓarna da zafi. Matakin daya ɗauka ba matakin gyara bane. Da ƙyar tun yana asibiti tasa ya dawo da Baba Suwaiba, da matar Malam ɗakinsu, kuma suka tare kafin a sallamo Malam ɗin. Zaman gida ba daɗi matar malam take ji ba. Baba Suwaiba kuwa sai yawo take yi a tsakankanin gidajen yaranta. Ta bangaren gidan Yaran Malam kuwa, babu jituwa a tsakanin matan gidan, sakamakon rashin haɗin kan dake a tsakanin mazajen nasu. Zuwa kwsnciyar Malam a asibity da sallamoshi suka san duk abinda ke gudana a tsakanin ahalin gidan. Lamarin sai ya zama yau in ba'ai hayaniya akan shara ba. Gobe akan wanke bayan gidan tsskar gidan za'ayi, gidan ya zama tamkar masu ganin hangin junansu. Ga gasa, ds yin bajinta a ƙoƙarin ko wanne ɓangare na son nuna shi ɗin shine. Malam ya ɗauki ido ya zuba, ya hana Yays Tasi'u cewa komai yace a barsu yana son ganin iyakarsu. Ta ɓangaren Hadiza da Shafa kuwa, babu yabo babu fallasa. Da safe kafin dukkanninsu su fita aiki suna haɗuwa su gaisa. Haka da daddare suna haɗuwa a ɗakin wacce bata da kwana aci abinci a ɗan taɓa hira kuma sai ku ma wacce akayi hira a ɗakinta sallama. Hadiza basa rabo da faɗa da Gwadabe dan ƙes ta gani wanda baiyi mata ba saita sashi gaba da maganar, hakan yasa ta zama mai yawan ƙorafi da yawan fishi. Saɓanin Shafa da take danne abubbuwa da yawa, kafin tayi ƙorafi sai abun yaci tura. Kwatsam wata ranar juma'a tun a makaranta Hadiza tai ta faman sheƙa amai dama kwana biyu bata gane kanta ba. Ya tabbata zargin tana da ciki ya tabbata. Ana tashi tayi gida dan zazzaɓi ne ƙaƙas ya rufeta. Tana zuwa gida ta kwanta gashi a ranar ita ke da girki, ta tashi ta dafa ta kasa, ta ce Shafa ta dafa kishi ya hanata. Sai ɓarayin Yaya Tasi'u taje Anti Badi'a ta cika mata babbar kula da farar shinkfa da romon gandar naman kan rago. Har Gwadabe ya shigo bata iya yin wanka ba, ɗakin nata ma bata yi shara ba, a haka ya shigo ya taddata a kwance a ƙasa. "Lafiya kike kwance a ƙasa Hadiza, ko dai babu lafiya ne?" Ya tambayeta bayan ya ajjiye mata kayan marmarin da ya zamar mata jiki shansu. "Wallahi jikinne sam babu daɗi. Kaga abincima sai ɓarayin Yaya Tasi'u naje na karɓo bazan iya girkawa ba" Kallonta yayi da kulawa, duk da yaji babu daɗi akan maganarta ta ƙarshe sai bai nuna ba yace. "Inane yake miki ciwo, kin kuma sha magani?" Dariya tayi tace. "Ciwon bana shan magani bane, ƙaruwa muka samu, ina nufin nan da watanni ƴan biyu zasu samu ƙani ko ƙanwa" Kabbara yayi tare da rungumeta cike da farin ciki yace. "Alhamdulillah dake da ƴar uwar taki ƙila babu nisa a tsakaninku. Itama kwanaki bata ji daɗi ba, sai ta shiga asibitin da take ba da kati aka mata gwaje_gwaje aka tabbatar mata tana da ciki" Sai Hadiza ta ɗan rage fara,arta. (Ku fahimta da Hadiza, da Baba Fhatsima wasu irin matane masu kishin sunfi son komai ace sune gaba. Bawai kishi take kar Shafa ta samu ciki ba, ta dai fi so ace itace ta soma laulayin kafin ita Shafar. Sai gashi a bayanin gwadabe da halama ɗanta ko ƴarta sai dai su biyo na Shafa, in ba wani ikon Allah ba.) Gaga_gaga lokaci yaita shurawa abubbuwa marasa daɗi sukaita faruwa, dambe tsakanin matan wannan gida, haka mazan dambe a tsakankaninsu. Zaman sulhu anyi yafi sau a ƙirga, haka zaman meeting ba'a denashi ba. Rarrabuwar kai sai sake ta'azzara yayi kamar yadda Baba Fhatsima da Yaya Tasi'u sukai hasashen haɗuwar ba lallai ta haifar da Alkhairi ba alai kuwa abinda ke faruwa kenan. Ƴan unguwa sunsa ma gidajen suna kusan kashi uku tsabaragen yadda suke shiga rabon faɗa a kullum. A haka dai akaita tafiya ranaku a cikin watanni. Har matan wannan gidan masifa suka soma haihuwa, duk taron suna sai anyi uwar watsin da kowa zai tafi rai babu daɗi. Jikin Malam kullum a cikin tashi yake, dan ashe a baya ba tashin hankali akayi ba, yanzune akeyi
Chapter 14 · 0% Book details