Sashe 58
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Shafa ce tsaye a tsakar ɗakinta tana ta jijjiga yarinyarta mai suna Iyabo yar wata Takwas yarinyar akwaita da kuka, bacci ma basa iyayi. Gashi Allah ya jarabci Shafa da samun wani juna biyun na uku kenan, watan cikin biyu a jikinta sai ɗan karen laulayi ga fitinar Iyabo mai kukan banza. Ƴan biyu ne suka dawo daga makarantar yamma ta malam suna jaye da hannun Abba suka shigo da alawa a hannunsu malam ya basu.
Kamar daga sama Shafa ta jiyo kamar Hadiza na ƙwalo mata kira.
"Zo ku zauna Toye karku fito. Zanje ɗakin su ummi yanzu zan dawo." Tana gama fadin haka ta fito da sauri. A falo ta samu Hadiza tana murƙususun naƙuda.
"Shafa kije ki kira mun Anti Badi'a dan Allah naƙuda nake yi."
Da sauri Shafa ta nufi ɓarayin Anti Badi'a ta sanar mata halin da ake ciki.
"Abinda za'ayi Shafa ki shiga cikin gida ki karɓo rubutu a wajen Malam sai ki sanar musu halin da ake ciki." Tare suka tawo Shafa ta wuce cikin gida, Anti Badi'a ta shiga wajan mai naƙuda.
Ciwon naƙuda har magriba haka su Gwadabe suka dawo suka tadda wannan lamari. Sau uku Malam nayo rubutu Baba Asshi na kawowa abu har bayan isha ana abu ɗaya.
Dole aka tafi da Hadiza asibiti a motar Yaya Tasi'u ranga_ranga. Tafiyarsu da kaɗan Allah yai ma Baba Fhatsima cikawa gida ya ruɗe aka fasa kukan mutuwarta. Su Gwadabe suna hanya Malam ya kira Yaya Tasi'u yana shaida mishi halin da ake ciki. Haƙiƙa anyi babban rashi a cikin wannan zuria. Rashin daya taɓa kab ahalin gidan, mutuwar data sauya zukata daga ƙiyayyar juna zuwa haƙuri da dangana. A rayuwa komai yana da mafari, kuma komai yana da ƙarshenshi.
Su Yaya Tasi'u suna shiga asibiti aka shige da Hadiza, amman likitoci sun bayar da sanarwar tiyata za'ayi mata. Gwadabe hannunshi na rawa yasa hannu a takaddar amincewa, da gaggawa aka shiga da'ita. Yaya Tasi'u ya matso kusa da Baba Asshi, da Gwadabe, da Anti Badi'a yace.
"Allah yayi ma Baba rasuwa muna fitowa. Ɗazu a mota kiran da malam yayi mun kenan. Tata ta ƙare Baba, sauran namu ya rage inma mu haɗe kawunanmu mu zama zuria ɗaya, imma mutuwa tai ta yi mana ɗauki ɗaiɗai"
Abun mamaki mutuwar Baba Fhatsima ta jijjiga Baba Asshi dan rikicewa tayi da kuka kamar ba kishiyarta ba. Yaya Tasi'u ya share hawayenshi ya riƙe hannayen Baba asshi yace.
"Ki yarda ki zame mana makwafin Baba. Ki amince a kawo ƙarshen wannan tashin hankali mutuwa ci take kamar rana."
Baba Asshi yau itace ta sa kanta a ƙirjin Yaya Tasi'u tana kuka. Dukkansu a wajen kuka suke yi. Gwadabe abu ya rikice mishi ya haɗe mishi biyu, ga mata a wani hali, ga suruka kuma uwa ta rasu. Da Yaya Tasi'u da Baba Asshi suka koma gida, akabar gwadabe da Anti Badi'a sunata kaikawo idanunsu jawur kamar garwashi. Sai misalin ƙarfe sha ɗayan dare aka fito da Hadiza daga ɗakin tiyata tare da ɗiyarta macce zuwa ɗakin hutu. A lokacin ne Gwadabe ya samu sassauci daga tashin hankalin da yake ciki. A haka suka yi kwanan zaune asubar fari Gwadabe ya kama hanyar gida.
Yaje ya tarar ƙofar gidan Malam dafifin al'umma ne kawai suka cika ƙofar gidan, Malam na da jama'a sosai, haka Baba Fhatsima matace ta mutane kowa nata ne banda ɗan banza.
A cikin gidanma cike da mata anata koke_ koke kab yaran gidan sun zo, ko wanne ka kalla yana cikin tashin hankali marar misali mutuwar ta doki waɗanda ma ba,ai zato ba dan a kuka harda su Sabitu sai haƙuri ake bashi. Sabitu a tsakar ɗakin Baba Fhatsima ya gama rarrafenshi, goyo kuwa Tasi'u ne kaɗai ya fishi more bayanta, sai shi yazo a na biyunshi.
Gwadabe ya kutsa kai zuwa turakar Malam inda duk yaran gidan suke, matan guda biyu manya suna ciki ana ma Baba Fhatsima sutura.
Zama Gwadabe yayi yana sharar hawaye.
"Tasi'u kuzo ku fito da makarar zuwa falo kui mata adda'a a kaita makwancinta" Malam fa yana zaune babu yadda yake tsabaragen damuwa, ciwonshi ma tun jiya yayi tsanani ya bari a kaishi asibiti yaƙi yace shi zai sallaci gawar ƴar aljanna, ya sata a kabarinta.
Yaya Tasi'u da Gwadabe ne suka fito da gawar suka ajjiye a gaban Malam. Malam ya girgiza kai yace.
"Fhatsima Allah ya baki sa'ar tafiya. In dai sai miji ya ɗaga ƙafa ake shigewa aljanna to Fhatsima ke ƴar aljanna ce. Annabin Rahama yasan da zuwanki"
Yayi mata adda'a sosai. Sai yaran gida kowa yayi mata, sai su Baba Asshi da jiki yayi tiɓis tsoron Allah da nadamar abubuwan da suka faru ya shigesu. Cikinsu babu wacce batai nadama ba, domin babu wacce bata cutar da Baba Fhatsima ba. Banda zarginta da asiri da suke yi.
Yaya Tasi'u da Yaya Jamilu ne suka fito da gawar Malam na biye dasu sauran yaran suka mara musu baya. Nan gidan ya kaure da salati da kuka har aka fita da gawarta. Duk wanda zaiyi magana a kanta halinta nagari yake faÉ—a, duk wanda zaiyi magana zai ambaci mai yawan kyauta. Gardawa ma sun ci kuka domin uwarsu ce.
Tsabar al'ummar da Baba Fhatsima ta haɗa sai a ƙafa aka tafi da'ita zuwa makwancinta, gidanta na gaskiya. Daga haka jikin Malam ya rincaɓe dole akayi asibiti dashi cikin wani mummunan yanayi malam ya shiga, yanayin da dole a cire rai da tashin shi. Yaya Tasi'u da Amaryar Malam ne a asibitin. Su Yaya Jamilu da Baba Asshi suka ci gaba da karɓar gaisuwa. Ga Hadiza a kwance inda take ma bata sani ba. Abba da Toye suna wajen Shafa. Baba Asshi ce ta yafito Shafa ta zo inda take.
"Shafa maza kije ki haÉ—a kayan karyawa aba Gwadabe ya kai musu asibiti. Matar wanku tana can bata ci komai ba. Ki haÉ—a akaima wan naku ma nasu. Kuje da Zaliha maza"
"To Baba"
suka tafi da Zaliha ruwan tea suka dafa, sai suka yi tuwon shinkafa dama Shafa na da lafiyayyar miyar kuɓewarta mai kyau tasha naman rago da bushasshen kifi. Fitowa su ka yi da kayan Abincin. Zaliha taje ta kirawo ma Shafa Gwadabe yazo.
"Ga kayan abinci. Wannan Yaya za'a kaima. Wannan su Yaya Tasi'u za'a kaima. Yayan ta sauka ne?"
"E ta sauka tun jiya da daddare ta samu mace. Nayi waya da su Bara'u da Tamu tun cikin dare asussuba suka kamo hanya. Ance su Babala da Yaya Hambali ma suna hanyar zuwa baki É—aya.
Shafa tace.
"To Allah ya kawo su lafiya"
Abincin ta bashi, ta koma cikin gida akaci gaba da amsar gaisuwa. Baba Asshi dawowa tayi ɗakin Baba Fhatsima da zama tare da su Ine. Dan duk wanda yazo gaisuwar ɗakin yake nufa. Surukan gidan aka wakilta ɗaura abinci a can gidansu. Domin baƙi daga nesa da zasu zo.
Amman maraÉ—i garine na karamci in anyi mutuwa fanteka_fanteka ake shigo da abinci har sai anyi bakwai.