Sashe 20
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Hajiyannan har uwar ɗakinta ta kaimu muka zauna a cikin ƙannenta. To kunsan mu yarbawa bamu da son jiki, saina sake na shige dangin Hajiyannan mukaita aikin girki, muka gama kuma na wanke musu wajen tas. Hama kuwa tunda ta zauna saita noƙe ta sake takurewa. Kafin a taru na ba Hajiyarnan zanin gadonnan gudunmawata, Hama kuma ta miƙa mata omo data ƙunso a jakarta, kafin Hamma ya tafi ya bamu ko wacce dubu akan ta bada gudunmawa. To tunda ko wacce na da abin bayarwa saita miƙa ta soke dubunta. Da naga taro yai taro an cika an batse saina kunce haja. Allah cikin amincewarshi wallahi kaya suka ƙare kab har ana nema saida nayi cinikin nera dubu arba'in ku kunji rabo. Wannan Hajiyarma tace in kawo mata zanin gado amman in bata sari tana da shago a kasuwa na zannuwan gado da su ledar tsakar ɗaki da kafet. Wata baiwar Allah ma tace in mata kwatancen gidana zata zo sarin riguna tana shiga ƙauyuka cin kasuwa. Na mata kwatance, gidana ta sanar dani gobe zata shigo. Haka wunin sunan ya kasance dai, akwai wata baiwar Allah ita kuma magungunan mata ta kawo, nima har na sai wani magani da naji anata yabon kyanshi. Hama ta kalleni ta kawar da kanta. Amman dana juya baya saida ta miƙa dubunnan ta kwashi kaya itama. Da yamma da Yaya Hamma yazo kwasarmu Hajiyannan ta cika mana kuloli biyu da abinci babbar kular farar shinkafa ce, ƙaramar kular kuma miyar naman saniyace a ciki, banda lemo da ruwan roba, da cincin duk saida ta haɗa mana. Mu tara gobe in Allah ya kaimu MRS BUKHARI