Sashe 64
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kamar ta haɗiye zuchiya ta mutu. Ko yau ma hakance ta faru da rana fatse_fatse Hama na zaune tana ma yaranta tsifa ta saki wuyan riga nono duƙui a waje, ni kuma na fito shanyar kayan ƴan biyu da Cubu ta gama wankewa dan itama ba daɗi take jiba. Sai ga su Uwani suna dambe da kujeru. Bafa wasu kujeru masu kyau bane irinna ɗakinta ne amman wallahi sai kawai Hama ta fashe da kuka da kururuwa tayi ɗaki a guje. Dariya muka kwashe dashi ni da Uwani kawai. "Marar mutunci ni da nice kishiyarki tsirara zaki fice sabida duka, ƴar baƙin ciki, yara dai gasu Allah ya nufa sun zo duniyar, haka da zaran Hamma ya dawo zai sake ɗirka mata wani cikin ƴan biyun. Cikin awa guda ɗakin me jego ya fito fes, har sabuwar leda suka siyomun komai yayi shar dashi, atampopim kuma aka kai mun ɗinkinsu maƙotanmu. Washe gari Baɗɗo ta daddage ta yarfamun kitsona kaina ya fito shar dashi, su Dada da su Yafendo suma sai tasu hidimar suke yi. Da yamma saiga mijin Baɗɗo da raguna maza tiƙa_tiƙa biyu ya shigo. Baɗɗo dama tun bayan gama mun kitso ta tafi Girai ta siyo kayan miya da duk abun buƙata, shinkafa na bata kudi ta siyo mai kyau harda soɓo da kayan haɗinshi jallof muke so muyi da soɓo aci a more. Da yamma sakaliya sai ga Amaduyal tafe da Anty Mulka, da Iyaa Beji, da Bose. Da kayansu na gara rigi_rigi abun sha'awa." Mrs Bukhari