← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 72

Sashe 62

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salati nake yi a hankali ina shan yaji tare da karkaɗa ɗan yatsana. Kamar an tashi Yafendo ta taso ta'iso inda nake ta dafa mun kai. "Jabu haihuwar tazo kenan? Alhamdulillah bari inje maza in taso Unguwar zoma tazo ta kula dake" Tayi maza ta fita, bata jima da fita ba saiga Baɗɗo tare da Hama sun shigo. Ɗago idona da suka yi ja nayi nasa a cikin na Hama. Sai naga ranta fes tana tsaye a kaina tana murmushin dana kasa fassarashi. Sauke kaina nayi naci gaba da roƙon Allah akan ya saukeni lafiya yasa in haifi mutum ba wani abunba. Kafin Yafendo ta shigo ita da unguwar zomannan na gama jiƙewa da zufa sharkab. Da unguwar zomannan ta shigo sai tace. "Ni a ƙa'idata bana karɓar haihuwa da mutane a ɗakin. Dan haka duk ku fice ku barmu daga ni sai ita" Fita suka yi aka barmu mu kaɗai. "Sannu Jabu ki saka dauriya zaki sauka lafiya. In baki ji nishi ba kar kiyi, hakan ke galabaitar da mata da yawa. Nishin zai zo da kanshi sai kiyishi iya karfinki nan da nan zaki haihu" Ni da unguwar zoma mukaita fama haihuwa dai tazo da tangarɗa kafin wayewar gari na fa galabaita bana ko motsin kirki. "Kaɓoji aje a nemo mota a kai yarinyar mutane asibiti kar tazo ta mutu, ko abinda ke cikinta ya mutu. Ni tsawon shekaru Ashirin dana shafe ina unguwar zoma banma taɓa karɓar haihuwa irin wannan ba. Cikin yana sama bai faɗo ba, kuma naƙudar take yi" Kafin Yafendo ta fita ta dawo jini ya ɓallemun. Baddo da Hama ne a kaina, in Hama ta faki idon Baddo saita danna mun cikina da iya ƙarfinta ni dama ganinsu sosai ma banayi. A gurguje a acaɓa aka tafi dani asibiti ni ina tsakiya Yafendo na baya ta riƙeni tamau, su Baɗɗo na biye dani. Ya ilayi ranar naga duniya, naga azabar da ko maƙiyina bazan mishi fata ba. A haka aka sake tarairayoni aka sakani a cikin akori kura zuwa cikin Girei Duk motsin da motar tayi da wani shiga rami sai inji kamar hanjina zai zazzago dan azaba. Muna shiga asibitin aka bani gado ma'aikatan jinya biyu suka rufu a kaina. Can a waje anata yima su Yafendo faɗan damme zasu bari in galabaita haka. Ni dai awana biyu a asibitin da kaina na haifo kyawawan yara maza ƴan tagwaye. Dishi_dishi nake ganin yaran ga gashi lub a kansu, gasu kamar yaran turawa da yaran a zuchiyata naji dif duhu ya maye gurbin hasken da nake gan. Ban sake sanin inda nake ba sai washe gari da safe na buɗe idona naga ƙarin jini a hannuna, ga jariraina a gefena, yara tsabar kyau kamar na aro. Juyowa nayi na ɗaga kaina na dubi Baɗɗo, na dubi Kari. Na lumshe idanuna inajin tsantsar farin ciki da Allah ya ƙadartama wannan yara zuwa Duniya yaran da kusan asibitoci sama da huɗu suka duba basu gansu a cikina ba. Allah yayi ikonshi gasu sun fito duniya. Inama Yaya Hamma yananan yaga kyawwawan abokananshi masu tayashi kiwon Shanu. Murmusawa nayi a lokaci guda wasu zafafan hawaye suka zubomun. Na farin cikine kukan na tsallake siraɗi. Murmushin kuma na taya Yaya Hamma farin cikine burinshi ya cika ni dashi mun haɗe mun zama abu guda, jininshi ya tsaga ya fito ta jinina yaran kamar an tsaga kara da ubansu. "Adda sannu yaya jikin?" Cewar Baddo ta yo kaina. Murmushi nayi mats duk da jikina babu ƙwari amman zuchiyata fes take. Da sauƙi jiki Baɗɗo. Sannunku, an sanarma Dada kuwa?" Dariya Kari tayi tace. "Sannu Adda. Dada ta sani tun jiya. Yau kwananki ɗaya a asibiti" Wata yinwace ta murɗa mun cikina da nake jin yanai mini ciwo_ciwo. Baɗɗo yinwa nake ji sosai" Da sauri Baɗɗo ta ɗauki kofi ta cikomun da kokko mai zafi. Kari ta taimaka mun na zauna, na jingina bayana da kan gadon. Ina shan kunun ina kallon yarana da aka lulluɓesu a cikin tawul ɗaya . Ma'aikaciyar jinyace ta shigo ward din tana bi gado_gado har ta iso gadonmu ɗakin duk masu jegone a kwance da jirajiransu abun sha'awa. Jinin da ake ƙaramin ta cire mun dama ya ƙare yanzu. Ta dudduba yaran dai haka, nima ta tambayeni ko akwai abinda ke damuna nace da'ita babu. Sai tace dani. Zuwa da rana zasu sallamemu ni da tagwaye muna cikin ƙoshin lafiya. Ta ɗauki yaran taita yabon kyansu dai haka ta ajjiyesu ta matsa gado na gaba. Yaran na ɗauka na ɗaurasu akan cinyata ina kallonsu da kyau. Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna. Ni da kaina nayi musu kiran sallah a kunnensu. Na dinga musu adda'a ina tofesu dashi. Ina cikin haka sai ga Hama, Safiya, Daso sun shigo da kwanukan abinci niƙi_niƙi. Ko ranar da da aka kaini gidan Hamma a matsayin kishiyar Hama, banga ɓacin rai makamancin wanda take ciki yanzu ba a fuskarta. Dani da yaranma sai naga tana wani harararmu, idanunta sunyi ja kamar ma tayi kuka. Safiya da Daso duk sukaimun ya jiki tare da yi mun barka. Wallahi babu abinda Hama tace dani. Anata kururuta kyan ƴan biyu tare da mamakin girma da kamanninsu da mahaifinsu. Funfurumfus Hama tayi ta zizarama idanunta kwalli taba banza ajiyarmu. Murmushi nayi cikin ƙarfin hali nace. Baɗɗo miƙama Hama yaran ta gansu" "A_a bassu bakya ganin nima ji nake yi da kaina." Murmushi nayi dama nasan ba ɗauka zata yi ba. Na gwadata ne kawai. Baɗɗo jakar hannuna an tawomun da'ita kuwa? Inason in kira Uwanine, da Debisi in sanar musu" Jakar Baɗɗo ta miƙo mun daman. Na ciro wayata na kunna. Burodami Debisi na soma kira na sanar dashi haihuwar. Sannan na kira Uwani itama na sanar mata. "Ai kuwa gara da kika sanar mun dan yanzu haka muna hanyar Adamawa tare da Bara'u abokin Gwadabe mijin Sakina" Sai naji gabana ya tattake ya faɗi da jin sunan Bara'u. Uwani ince dai lafiya dai ko?" Na tambaya a raunace. Hama idanunta ƙam a kaina tana karantata. "Lafiya lau sai alkhairi ke dai sai mun karaso kawai" Mu kai sallama na sauke wayata. "Jabu ga fa abinci Hama ta dafo miki. Baɗɗo ki zuba mata ko?" Cewar Daso kenan. Jin haka yasa nace. A'a ta bar abincin bakina babu daɗi sam. Baɗɗo in kina jin yinwa zaki iya ci, ni kam ko zanci sai anjima. Na koma nayi kwanciyata yarana suna kan cinyata ina jiyo ɗumin abuna. Miƙewa Hama tayi da fullanci tace. "To ni kam zan tafi gida, sai kun dawo" Tana faɗan haka ta kara gaba, Daso tabi bayanta. Safiya ce taimun sallama cikin mutunci. Suna fita Amaduyal yana shigowa da kwano a hannunshi. Farfesun kazar hausane Dada tayi tace a kawo mun. Nako ci da dama nasha romon sosai shima take bacci ya ɗebeni bani na farka ba sai wajajen azahar. Na farka ba da daɗewa ba aka kawo mana takaddar sallama da kuɗin da zamu biya. Baɗɗo ce taje biya dan Yafendo ta bata kuɗi daman ko za'a buƙata. Ina zaune jigum saina hango Bara'u a gaba rike da Taiyo da kahinde, Tabalbalin na biye dasu ga Toye a gefenta. Idanu na lumshe, Allahu Akbar naji daɗin ganin yarana fiye da tunanin masu karatu. Jina nayi kamar an tsundumani tsuungum a Aljanna. "Tsuntsun soyayya ƴan biyun aka sake haifo mana? Masha Allah" Miƙa mishi ɗaya nayi, Uwani ma ta amshi ɗaya. Sakkowa nayi na rungume su Toye dukkansu. Wato akwai ciwo rabuwa da yara, Toye ne kaɗai ya ganeni, su dai su Kahinde sunyi lub a jikina kawai. Naji daɗin ganinsu a cikin shiga mai kyau, da dukkan halamu Gwadabe ya samu rufin asari ba kamar yadda na sanshi ba. "Iyabo ashe Allah yayi yara sun fito duniya? Kai masha Allah ji yara tubarkalla kamarsu sak da ubansu." Ɗan murmushi nayi ma Uwani tana fama da ƙaton ciki hancinta duk ya buɗe. Bara'u barka da zuwa, yaya bayan rabuwa, yasu Sakina?" Dariya yayi yana jinjina kanshi. "Duk suna lafiya Iyabo. Da fatan kin samu kai lafiya. Banga maigidanba ko a waje." Ɗan murmushi nayi nace. Sun tafi cirani kiwo kamar yadda akasan fulani da fita kiwo." Murmusawa yayi yace. "Allah ya dawo dashi lafiya. Yara kuma Allah ya rayasu cikin aminci. Ga yara Gwadabe ya aikoni dasu tun daga Maraɗi yace a kawosu su yi wata guda, sai in dawo in ɗaukesu da yardar Allah." A Maraɗi kuma Gwadaben ya koma da zama?" Na tambaya da mamaki. " E Maraɗi yake da zama kusan shekara bakwai kenan. Gidan Baba Magaji wansu Babala. To yana auren Hadiza yarinyar Baba Magaji. Da Shafa ƙanwar Abokinmu Tamu, yaranshi huɗu ciki harda takwararki." Mamakine ya kamani. Gwadabe da mata biyu? Iko sai Allah, dama yana da ra'ayin mata biyu kena, ko bayan rabuwarmu ne ya samu ra'ayin? Kafin in gama tantance fari da baƙi Bara'u ya miƙo mun hoton diyar Gwadabe takwarata. Nasa hannu na amsa na zuba mata idanu kyakkyawa fara da'ita. Nayi farin ciki da Gwadabe yasa sunana ashe dai bai mance dani ba. "Kin ganta wannan itace Iyabo. Shafa kanwarmu itace ta haifeta, shine yasa aka kaita gidan ɗaukar hoto aka ɗauketa dan a kawo miki ki ganta." Allahu Akbar. Naji daɗi sosai Bara'u Allah yabar zumunci" Baɗɗo ce ta dawo daga biyan kudi. An gama komai sai tafiya. Sallama nayi da matan ɗakin muka wuce. Tare duk muka rankaya zuwa gida. Baɗɗo nasa ta kai Bara'u gidan Dada, ni kuma aka wuce dani gida. Wajajen bayan Isha can, bayan nayi wanka naci tuwo, Amaduyal yazo ya ɗauki abincin Bara'u da nasa akayi mishi, Da tsaraba Amaduyal yazo yace Bara'u ne yace a kawo mun. Su Toye suna ɗakin Yafendo ta janyesu. "Iyabo na ƙosa ki bani labarin bayan rabuwa. Da ganin ɗakinki abubbuwa da dama sun faffaru. Naji kince Hamma ya tafi cirani. Meke faruwane, ga kishiyarki naga sai dukan yaranta take yi tana baloƙoƙo?" Hmmm Tabalbalin meye ma bai faru ba?" Nan na shiga mata labari daki_daki harna dire mata. "Iko sai Allah Iyabo. Kina ganin rayuwa kekam iri_iri. Amman watarana fa duk sai labari, amman da kikayi gobara da saiki sanar mini kema kinsan zan turo miki da duk abinda kike buƙata, kuma zanzo ki ganni kiji daɗi. Baki ga yadda kika fita hayyacinki ba.
Chapter 62 · 0% Book details