Sashe 10
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kunsan masu ƙiba yadda sutura take amsarmu, haka kwaliyarma take amsarmu. Abunka kuma da Amaryar birni a ƙauye. Ni dai harna iso gun_gun matan dake kallona basu dena ba. Ina kwananku" Nai musu jam'u dan Hama ma tana cikinsu. Tsirari daga cikine suka amsa, na yi wucewata na bar musu ƙamshin turarena a iska. Danƙari na ji wata baƙuwar murya ta faɗa ko me take nufi da hakan oho. Sallama nayi a ƙofar ɗakin Yafendo na shiga. Duk ƙannen Dada suna ciki karyawa suma suke yi, su Iyaa Kokodeen ma suna ciki. A ƙasa na zube na bisu ɗaya bayan ɗaya na gaishesu. Ko wacce da fara'a ta amsani. Saina nemi gefen gadon bono na takure kaina a ƙasa nayi shiru kamar ruwa ya cinyeni. Can Yafendo A'i tace. "Jabu sai kin ƙara da haƙuri dan zama da kishiya ba abu bane mai sauƙi ba. Musamman ka haɗa miji da bafulatana, bafulatanar ma ta Camaron basu ɗauki kishi da wasa ba. Mu ma da kika ga mun yi ƙarko har zuwa yanzu, haƙuri da kawaicine, da ƙarfin adda'a. Kema ina baki shawarar ki riƙe wannan abubbuwan zaki samu riba duk daren daɗewa. Ki zamto mai kawo haɗewar kai ba mai ƙoƙarin ganin an samu rabewar kai ba. Hamma dai ɗan uwankine jini ba ruwa bane, kar ki bari wata ta kutso kanta cikin rayuwar aurenki ki kula sosai. Kuma kin nuna mana soyayya, kin yi abun a duba Hamma zai nuna miki shi ɗan halak ne" Ta jima tana nusar dani tare da bani satar amsa dangane da yadda zafin kishin fulani yake mazansu dama matan nasu. Daga ƙarshe tace inyi komawata ɗakina" Sallama nayi musu na fito. Kaina a ƙasa na wuce matan da suke tsaye cirko_cirko dan son sake ganina. Uhm bance dasu ba nayi kwanar lungun ɗakina nayi shigewata. Uwani na gani akan turmi tana ta faman zagaye mun ɗaki da farin citton me les les. Yayi matuƙar kyau sosai. Ashe kun dawo Tabalbalin? Sannunku da ƙoƙari" "Mun dawo har mun shiga aiki. Ance yau ango zai shigo ɗakin Amarya ai gara mu samu mu kammala komai a nitse. Kinga wasu fararen labulaye masu kauri dana siyo inaso ko yayane mu raba ɗakin biyu ta yadda ko an shigo ba za,a ga wanda ke kwance a gado ba ko ya kika gani?" Lallai wannan dabarace mai kyau na kuma ji daɗinta sosai na baku wuƙa da nama" Anti Ramata da Cubu kuma kujeruna suka fitar dukka waje muka haɗu muka sake ma ɗakin fasali babu laifi yafi na farko kyau. Kujerar doguwa guda ɗaya kaɗai aka mayar, sauran nace Baɗɗo ta ɗauki 2 sitter ɗin sauran 1_1 ɗin akai gidan Dada a ajjiyema Cubu in aurenta ya tashi sai a kai mata. Muka gyara komai abincin gara na ɗebi wanda zan ɓoye na tura ƙarƙashin gado, dama na sai maggi dunƙule katan guda, na daka yajin barkono da yajin daddawa, na sai kayan tea na dayawa, na sai tocilolina masu batura hatta baturan na sai abina, Uwani tayo mun miya, mun tawo da risho da kalanzir, ƙananun abubbuwan buƙata dai wanda nasan zanyi amfani dashi duk na sai kayana na adanasu. Cikin awa uku ɗaki yayi shar dashi gwanin ban sha'awa. Mata masu zuwa ganin ɗaki har daga maƙotan ƙauyan zuwa sukaita yi basu taɓa ganin kaya irin nawa ba, yadda aka raba ɗakin biyu shima ya burgesu sosai. Haka dai aka wuni cur ana sha'anin biki. Wuninnan cur kuwa ruwa akaita makawa. Sai magriba ruwannan ya tsaya na samu nayi wanka na sake kwalliya. Anayin isha su Uwani suka watse suka barni ni kaɗai a ɗakin ƙwalam akan kujera na ƙurama tocila idanu. Ɗaga kai nayi na kalli yadda su Uwani suka rufe azarar saman ɗakin da farin labule cikin hikima. Na daɗe a zaune ina karanta wasiƙar jaki ga turaren tsinke sai ƙamshi yake fitarwa daga saudiyya na siyo. Wajajen goman dare har bacci ya soma surata akan kujera na jiyo shigowar Yaya Hamma. Da sauri na buɗe idanuna dan na tsorata sosai. "Tsoro kikaji ne Jabu naga kin tashi a zabure?" Saye yake da wani yadi green yala_yala ɗinkin ƴar shara, kanshi babu hula sai suma data zame mai ado ta kwanta ta laɓe a dogon wuyanshi. Sai ƙamshin turaren sasarobia yake yi, hannunshi riƙe da leda mai zane" Da sauri na miƙe tsaye ina shirin amsar ledar hannunshi. Saijin hannunshi nayi ya riƙe ƙuguna ya jawoni na faɗa jikinshi. Ƙam ya riƙeni, nima na riƙeshi ta baya riƙo na ƙwarai. Munkai kamar minti biyu cur muna shaƙar numfashin junanmu. Ni dai wani abune ya shiga yi mun yawo tun daga dunduniyata har zuwa kaina. Ji mukayi an bankaɗo labulen ɗakin an shigo. Ga wani irin kukan jinjira na fitar hayyaci. Da sauri muka saki juna. Hama ce a tsaye riƙe da jaririyarta dake canyara kuka. Wuf Hamma ya amshi yarinyar yana tambayar Hama meke damunta. "Baccinta take yi lokaci ɗaya saita soma firgita tana zabura tana miƙewa, sai kuka ka dai ganta" Jijjiga yarinyar ya dinga yi, amman yarinyarnan kamar ƙara zugata akeyi sai canyara ihu takeyi bakinta na rawa. Kafin kace me matan gidan duk suka yo ƙofar bukkata suna tambayar ba'asin wannan kukan. Hamma ne ya fita da yarinyar rataye a kafaɗarshi. Ina jiyoshi yana musu bayanin da Hama tayi mishi da fulatanci. Ni kuwa ina tsaye a inda suka fita suka barni, ga ledar kaji tarwatse a ƙasa. Tun inajin muryoyinsu harna dena jiyowa, kukan yarinyar yayi nesa sosai. Wallahi saida nayi awa guda cur a tsaye in kai mari in kai gwauro ina tubkewa da warwarewa. Labulena aka ɗaga Hama ce fuskarta a sake tace. "Amarya sai haƙuri auren mai mata angone yace in sanar miki zamu kai yarinya gidan magani, wai ki kwanta kiyi baccinki, in mun dawo zai kwanta a ɗakina sabida jikin yarinyar" Numfashi naja sama nace. To Ubangiji Allah ya bata lafiya, gaskiya ya kamata ya zauna tare daku har sai ta samu sauƙin jikin nata" Labulen ta sake. Ni kuma wasu siraran hawaye suka gangaro a kumatuna lumshe idanuna nayi na kaɗa kaina na zauna a kan gado ina karanta wasiƙar jaki. In ƙulla fari in ƙulla baƙi zuchiyata bata gamsu da kukan yarinyarnan ba wallahi. Duk da naga yadda take kukan fitar hayyaci. Amman babu komai ai hama ba zata dauwama tana cin nasara a kaina ba. Wannan dai ta shammaceni. Bari mu gani gobe kuma dame zata zo. Kwanciya nayi ina kallon sama sanyi na ratsani. Irin wannan weda ta ma,auratace, naso yau yadda wedarnan ta bada haɗin kai mu raya wannan dare. Amman babu damuwa gobe ma ranace. Da tunane_ tunane bacci yai awon gaba dani mai cike tab da mafarkai marasa daɗi. Ƙarfe ukun dare na miƙe a bahun na ɗaura alwala na soma sallar nafila har zuwa ketowar alfijir. Saida na sallaci asuba na kwanta a kujera dan tsabar bacci kaina kamar zai fashe. Kamar a mafarki nake jiyo muryar Baɗɗo da Uwani a kaina. Ina buɗe idanuna ilai kuwa sudinne. Uwani riƙe da takaddar kajin da Hamma yai watsi dasu. "Iyabo ya kaza haka a yashe a ƙasa ga Amarya kuma akan kujera, Allah yasa lafiya?" Uwani ta tambayeni. Sai da nayi Ajjiyar zuchiya kana nace. Ina kuwa lafiya Uwani. Har ɗaki aka shigo aka janye ango har yanzu banma sashi a idanuna ba. Ke jiya ni naga bariki." Shewa Uwani tayi, ta nemi waje ta zauna niko na labarta mata halin da ake ciki. Hararata tayi tace. "Kin bani kunya. Karfa ki bari zaman saudiyya da kikayi ki bari ya tashi a banza. Wacce yaudarace baki gani ba. Ga zaman gidan Gwadabe wanne siraɗine baki tsallakeba? Ko da yake nifa Hama burgeni tayi, ai baki ga komai ba Iyabo" To Uwani ya zanyi ni mamakine ya hanani kataɓus. Amman bawai zan bari ta takani yadda taso bane sam. Jiyanma ta shammacenine wallahi. Na kuma barta ne kawai in halinta ne zata sake. Zigata akeyi shi yasa duk take wannan abubbuwan." "To gaskiya karki sake bari hakan ta faru. Yanzu dai wannan kajin ai sai mu zauna muci mu kora da lemu rabonmu ne" Wanke bakina na fito nayi a ƙofar ɗakina na koma ciki, muka zauna mu uku saida muka ta da kajinnan biyu ƙananune sosai muka kora da lemun kwalba. Ko da aka kawo mana ɗumamen tuwon masara bamu ci ba mayarwa mukayi. Rishona na fitar ƙofar ɗaki na dafa ruwan wanka nayi, na sha kwalliyar les fari tas. Su Anti Ramata ne suka shigo da shirinsu na komawa gida tsab. Nasiha suka sake yi mun dai a gurguje. Burodami Kokodeen ma ya shigo yai mun nasiha suka kama hanya. Haka dai muka wuni a ɗaki maƙota sai shigowa ganin Amarya suke yi ba ƙaƙƙautawa. Da rana Hama ta girko shinkafa da miya aka kawo mana, miyarnan baƙi sosai kamar anyi sauwarta da ruwan rubutu. Daga ni har Uwani bamu ci ba. Yafendo ce ta aiko mana da fura da yawa. Dada kuma ta aiko mana da farfesun kaza, shi muka ci muka ƙoshi. Wajajen azahar yaran Baffa Musa, da yaran Yafendo A'i, da su Karima harda Daso duk suka taru akaita hirar zumunci. Mafi yawan hirar da fulatanci suke yi sai hausa jifa_jifa. Daso dai ba komai take sa musu baki ba, niko na sake sosai a cikin ƴan uwana. Sai da sukai sallar la'asar sannan ko wacce ta kama hanyar gidanta. Ritsona na fitar gefen ɗakina na ɗaura ruwan zafi. Uwani ta shiga gyara mun ɗakin dan duk ya hargitse. Ruwan zafin na tafasa na cika filasaina du biyun na sake mayar da wani ruwan na wanka. Kafin ayi sallar magriba na fito daga wanka. Saida nayi salla kana nayi zaman dirshan na shafe jikina da mai, nayi kwalliya mai sauƙi na sanya doguwar rigar yadin boyel me ruwan baƙin bulu ( blue black). Na saka ɗankunne da sarƙata fashion ja kasancewar akwai ƙaramin keb a wuyan rigar boyel din anyi da jan zare. Na feshe jikina da turare shar. "Bari in nemo miki gaushi ki soma amfani da turaren wutanki ɗan saudiyya wallahi ba dai ƙamshi ba." Fita tayi da kaskon turaren wutan. Tana fita Safiya matar ƙanin Hamma ta yo sallama ta shigo hannunta riƙe da langar tuwo da miya ta ajjiye.