Sashe 23
Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zuchiyata tana cikin ƙunci. Yau nice miji yasa hannu yaimun shegen duka haka? Babu komai akwai Allah" Hawayena na share, na ɗauki mayafina daya faɗi garin duka na yafa na fito hannuna ɗauke da tiran abincin jiya da daddare. Ina fitowa naga gilmawar Hama ta fice a guje daga lungunmu, nayi imani laɓe tayi mun. Ba yau bane kaɗai ba, ina zarginta sai dai yau ta tabbatar mun da zargin. Ko a zuchiyata na tuna Hama ita ta shiga ta fita tayi asirin farraƙani da Yaya Hamma. Amman sai nayi saurin tuba bisa furucina. Ba mai yi sai Allah. Hawayen daya cicciko a idona na mayar da dabara na fito tsakar gidan gabana na faɗuwa. Sai nake jin inama ƙasa ta tsage in faɗa da wannan abun kunya. Aiko da Hama na soma cin karo ta kafa ta tsare. Banko bi ta kanta ba, na dai jiyo tana waƙar fulani. Ni dai ta kaina nake yi, wani irin mugun sarawa kaina yakeyi, idona inaji kamar zai zazzago. Ina hura wuta Baɗɗo ta shigo. Tana kallona ta riƙe mun hannu. Sai hawaye shar_shar a idanunta. Cikin jarumta nace. Ki dena kuka babu komai Baɗɗo. Bari in gama dumamennan ki sameni a bayan layi sai muyi magana." Tukunyar tuwon dana yayyanka na ɗaura, ɗaya gefen na ɗaura miyar. To ni a gaskiya inna ɗaura abinci a wuta bana ko motsawa ina zaune har saina raba. Dan gudun kar a cutar dani, irin magungunan da Hama take sassakamun yayi yawa. Saida na raba dumamen matan gida suka soma shigowa. Da suka ga yadda halittata ta sauya, sai wannan ta kalli wannan, wannan ta kalli waccan. Haka kuma ina jiyota da Yaya Hamma a tsakar gida sai dariya takeyi. Ni dai na gama abinda zanyi na ɗakko namu abincin na fito. Amman me Yaya Hamma harya fice abunshi. Na gyaɗa kai tare da haɗiye yawu mai ciwo. Koda na shiga saina sau kuka kawai. Ina cikin rera kukannan sai ga Baɗɗo da Amaduyal a guje sun shigo" "Adda Adda shanu sunata mutuwa kizo ki gani" A guje ni dasu muka fita. Allahu Akbar lallai an sabautani dan duk manyan shanun sun faɗi sun mutu sai kumfa ke fita a bakunansu da halama wata gubar aka saka musu. Ragowar ƴan madaidaitan da basu ƙarasa mutuwa ba Amaduyal yasa kansu gabas ya yanke. Matan gida dana maƙota duk suka cika gidan tam anata tayani jaje, ga gulmar ganin bakina da idanuna da suke ta tayi. Ana cikin haka saiga Yafendo ta kutso ta iso. Ga shanaye a kwance riɗa_riɗa sun mutu shanaye masu tsada ƙosassu. "Ko wani abun suka ci a wajen kiwo Amaduyal? Wannan lamarin da girma yake, shanu manya haka? Maza je ka kirawo Baffanku" Da sauri Amaduyal ya fita, Yafendo tana kalloni taga a halin da nake. Sai ta dafani" "Jabu me ya samu idanki duk ya kaɗe jini ya taru, ga bakinki a fashe?" Munafurci irinna matan ƙauye duk sai su kayi tsit suna jiran amsata. Faduwa nayi a banɗaki na taka sabulu" Hama najin haka ta saki murmushin da karaf a idona tayi wucewarta. Hannuna Yafendo ta ja izuwa ɗakinta ta zaunar dani a gado. "Kuna faɗa da wannan yaron ne Jabu, ki sanar dani gaskiya dan ina lure da abinda yake faruwa a gidan. Bana son in yi managane dan kar aka dan ku yaran yata ne ina tare muku. Hamma ne ya bigeki?" Hawaye ya zubo mun shar_shar ga raɗaɗin jiki, ga raɗaɗin zuchiya, ga raɗaɗin abinda ya faru da dabbobina nayi asarar dukiya mai yawa. Amman nayi tawakkali ina fatan Allah yasa wata musibace da zata sauka a kaina ta sauka a kan dabbobin. E Yafendo shi ya dakeni" Salati ta soma tana tattafa hannayenta. "Wannan yaron ne ya dokeki, yaushe ya zama lusari ni ban sani ba, a kanki dukan zai soma? Nasan wannan baya rasa nasaba da Hama nayi imanin tana da sa hannu akan wannan dukan, da mutuwar shanunnan naki. Bafa komai bane face baƙin ciki. Abinda dai nake so dake shine kiyi haƙuri kinji am? Ki zama mace mai juriya da ɓoye sirrinta. Hamma wankine, kuma nasan yana matuƙar sonki fiye da Hama. Itama kuma tasan haka ba zata barki ki zauna lafiya ba. Jabu kishi da fulatanar daji ba sauƙi. Da zan baki labarin irin wahalar da mahaifiyarki da Ai'i Yafendonku suka sha a hannun kishiya da zukatanku sai sun fashe. Ki duba irin yadda su Yusufu suke a ɗofane su da gidan ubansu duk sabida sharrin kishiya. Mai Nagge yaso Daso sosai mu munfi kyautata zaton asiri kishiyarta tayi ta farraƙa tsakaninsu, inaga irin asirin da Hama tayi a tsakaninki da wannan yaron kenan tunda har wannan yaron ya iya cire hannu ya dokeki." Fasali ta ja. Ni kuma tuni ƙwaƙwalwata ta lula tunanin kenan nima haka zan rayu irin rayuwar da Dada tayi a gidan mai nagge, yarana suma haka zasu kasance kamar yadda su Yusufu suke kenan, ciwon zuchiya da hawan jinine zai yi ajalina daga ƙarshe, koma Hama ce zata kasheni ta huta? Ya Allah ga baiwarka bata da kowa bata da komai. Allah kaine gatana ya Allah ka karkato mun da hankalin mijina ya dawo zuwa gareni muci gaba da shimfiɗa rayuwa kyakkyawa mai albarka. Maganar Yafendo ce ya dawo dani cikin hankalina. "Amman mai haƙuri shi ke dafa dutse har yasha romonshi. Na haɗaki da Allah kar neman mafita ko tudun dafawa ya kaiki ga bin malaman tsubbu Jabu. Ki dogara da Allah, zan dage in tayaki da adda'a. Bana son wannan maganar dukan da canjin Hamma ya je kunnen Adda Daso. Itama Baɗɗo da Amaduyal zan ja kunnensu." Muna cikin haka sai ga Baffa Musa ya shigo duk a ruɗe. Ɗankwalin kaina nayi maza na cire saina yafa kamar mayafi na rufe fuskata. Shi yama ɗauka kuka nake yi sai ya shiga rarrashina. "Tashi jeki Jabu" Cewar Yafendo. A hankali na fice na koma ɗakina, daɓas na shirgu a kujera saida ta yi ƙara tsabar ƙiba. Tunani na shiga yi. Kaddarata ta wannan karon ta muguwar kishiyace, jahilar kishiyar da ko alwala ba daidai take yi ba. Na tsallake siraɗin uwar miji da ƙyar, na sake faɗowa tarkon kishiya. Idanuna da nake ji kamar zasu faɗi na lumshe wasu hawaye masu zafi suka zubo, ina tuno sanda Yaya Hamma ya dunƙule hannu ya naushi idona, wanda hawayen daya tarwatse a cikin idon ni na ɗauke tsiyayewa idanun ma yayi. Tun ina jiyo hayaniyar matan gidan har na dena jiyosu, Baɗɗo dai yau bata je tallenba ɗan uwa abun wuya. Ita taimun duk aikina hatta abincin rana ita ta dafa mun ta raba, jikina ko ina ciwo yake yi, ciwon bayan dana kwaso a bautar gidan larabawa shima ya tashi sosai bayan har tururi yake yi mini. Zuwa yamma lis Amaduyal ya kawo mun kuɗin shanun daya yanka an siyar. Na buɗe adaka na ɗebo kuɗi masu yawa. Ka riƙe ka ba Baffa Musa a hannunshi a siyo wasu shanun. Ka ɗauresu a gida kawai a hakan. Wannan ragunan da kajin ka kaɗasu ka mayar dasu gida" Shiru Amaduyal yayi da kuɗaɗe a hannunshi yayi jimm "Adda wannan kuɗin ba kuɗin da kike juya kasuwanci bane, kuma naga kayan sun ƙare anata nema. In aka siyo shanun ke da wanne kuɗin zaki juya?" Murmushi nayi mishi. Babu komai akwai ragowar kuɗaɗe a hannuna. Uwani zata cikace mun zan saro kaya kar ka damu, a soma kashe wannan wutar tukunna" Kai ya gyaɗa kawai, har zaice wani abun sai kuma ya fasa, abincin Dada na bashi ya kai mata. Na koma na kwanta Baɗɗo kuma na sallar la'asar ina kallon abun mamaki dan ba daidai take yin Allah ba. Baɗɗo ba daidai kike sallah ba subhanallaah. Ki shirya da zaran na warke dake da su Cubu zan kafa muku makarantar dare zan koyar daku ɗan iya abinda na sani game da addini, kuma mu dinga karatun Qur'ani" Jikinta a mace mutus ta amsani da to. Ita tayi girkin dare ta raba ta fitar dana kowa, hatta ruwan wanka ita ta kaimun jiki yaƙi daɗi. Ina zaune na gama kai kukana ga Allah sai na jiyo sallamar Yaya Hamma. Ba shiri na miƙe tsaye ina mishi sannu da zuwa, banza yayi mun ya nemi waje ya zauna. Ina wuni barka da dawowa Yaya Hamma" Na durƙusa har ƙasa da ƙyar gani dama ba kaɗan ba. Hanci naga ya toshe naci wani ciwo a zuchiyata. "Jabu ɓera ne ya mutu a ɗakinne?' Yayi maganar da zafi. A'a wari ɗakin yake yi ne?" Na bashi amsa a taƙaice tare da mikewa na zauna a gefenshi. Kamar na soka mishi allura a takashinshi haka ya miƙe tsaye yana matsawa baya harya fita daga ɗakin. "Bazan iya zama a cikin wannan warin ba. Kema kije ɗakin Dada ki kwanta gobe ki duba abinda yake warin" Labulen ɗakin ya saki, sai naji kamar zuchiyata ta rushe dan bala'i. Kwanana ya miƙa ma Hama inaji ina gani. Kishi zai yi ajalina, duk da a cikin fishi da taka tsantsan nake dashi, amman duk bala'i gara ya zauna a ɗakin, ni na gwammaci ya kuma dukana daya kai kwanana ɗakin kishiya taga wallena. Baza ku gane ba nasan, wannan kishin da jiin zafin ya shafi mai kishiyane kaɗai, da waɗanda suke cikin takalmana ma'ana da matan da aka taɓa yima fin ƙarfin kwana suna ji suna gani. Tuttura tuwon da Baɗɗo tayi na dingayi na danne tuwon da madarar shanu, na haɗiyi fanado dama ina dashi da rana ma na haɗiya sanda Baɗɗo ta damamun fura. Duk ciwon da nake ji, da ƙagewar da bayana yake yi, a wannan daren saida na hautsine ɗakinnan na birkitashi. Illahirin ɗakin banga komai ba, ni ƙamshi ma nake ji a ɗakin dan ni ma'abociyar ta'amali da turarukane mada'in ƙasashe daban_daban. Duk iya bincikena dana binciko banga komai ba. Na kwanta ina nishi gami da tunanin to me ke faruwa kenan, ko dai tsabar Yaya Hamma yana son tozartanine yasa ya tsiro da zancan warinnan? Ni dai kwana nayi cur ina tubkewa in warware abuna, abin duniya yabi ya dameni ga idanu ya matsamun lamba abinda yafi komai tayar mun da hankali shine kafin gari ya waye ba sai idona me ciwon naga kamar ya dena gani ba? Sai insa