← Book details Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 72

Sashe 28

Nama Ya Dahu Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read

suke a zube Abba sai kuka yake yi sabida zafi. Shafa tun rana take sa ran zuwan Gwadabe abincin rana ma data girka ma su Hadiza saida ta ɗebar mishi ta adana da taga har an ɗaura sanwar dare bai shigo bane ta cinye abincin. Gaggaisawa akayo da matan gida, Shafa ta miƙo mishi Abba dake ta raraka kuka "Kukan zafinne haka? Ga ƙuraje duk sun feso mishi, me kike shafa mishi to?" Gwadabe ya tambayi Shafa. "Hodar moju nake barbaɗa mishi, bari in ɗakko a kuma shafa mishi" Ta tashi taje ta ɗakko hodar Gwadabe da kanshi ya shafe jikin yaron da hodar, baifi minti huɗu ba yayi baccinshi a jikin Baban. Matan gidan sai suka tashi suka koma zaure dan cikin ɗaki gaskiya baya shiguwa. Tuwo Shafa ta kawo musu suka taɓa dan sun san su Sakina ma suna can suna jiransu da abinci. "Gwadabe dama ranar da muka zone saina shiga gida wajen Babala. To gaskiya abinda ya faru ya mugun ɗaure mun kai. Yadda Babala taci mutuncinmu, har Abba bata ƙyale ba dan ashe an faɗa mata sunan Baba yaci. Wai bata yafe ba da kasa sunan Baba. "Ya'isa Shafa. Kuma kar in kuma jin bakinki akan wannan maganar. To fa wata sabuwa su Babala manya. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.[9/13, 11:40 AM] +234 803 969 6400: NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE
Chapter 28 · 0% Book details