← Book details Na Fado Daga Bene Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 35

Sashe 8

Na Fado Daga Bene Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallar ma a zaune na yi ta sabida jirin dake
ibata.

Ina jiyo muryar Sani da Dauda, da su Shafi'i, suna gaisawa da saurayin Amina.

Da sallama suka shigo gabaki
ayansu, banda Amina.

Sani na ri
e da tire
auke da abinci da ruwa.

A gefen daddumata ya zauna.

"Umma yaya jikin naki, umma naga kin rame lokaci
aya, Yaya shine baka sanar dani halin da ake ciki da wuri ba?" Murmushi nayi, Dauda kuma ya harareshi.

Shafi'i yace.

"Umma ya jikin?

Muna ta zuwa dubaki sai mu ga kina bacci "
Jiki da sau
i nagode.

Autana zo mana" Dauda yace.

"Sani zai barshi yazo ne, ya mayar da kanshi ma shine autan gidan" Su Sulaiman suka fashe da dariya.

Salis ya matso kusa dani yace.

"Umma ya jikin ki?"
Da sau
i ya karatun Auta, kana ganewa?" Sai naga su Shafi'i na mishi dariya.

Nace dasu.

Menene kuke ma autana dariya haka?" Balaraba tace.

"Umma bashi da
ari a makarantar boko.

Bai iya komai ba.

Amman kanshi na ja a madarasa, yafi
an ajinsu iya karatu a madarasarmu ta Kaduna." Kafin ince wani abun Sani yace.

"Ummanmu kici abincin.

Bari mu barki ki huta."
Kai da Dauda ku tsaya zamu yi magana.

Ku kuma ku tafi can gidansu Inno.

Ku sanar musu zuwan ba
on Amina."
"Umma ai Umma Habiba tace sai sun soma zuwa gidansu
Inno, kafin su zo nan" murmushi nayi.

Habiba Bala tana sona da dangina baki
aya.
an ta
a abincin ka
an nayi, Sani ya
allomun magunguna na sha.

Sai na gyara zamana.

Ku saurareni da kyau nasiha nake son yi muku akan rayuwa.

Ku maza ne ya zama dole in fa
a muku, kuma in muku garga
i sosai akan rayuwa.

Kai Dauda kana da budurwa, kuna soyayya kana son ka aureta.

A yanzu bayan ni,
an uwanka babu wacce kake so sama da wannan budurwa taka.

Shin ka shirya aurenta, ko tukunna?

Dan bana son ta
in banza, ita kanta Amina saurayinta ya fito kawai a ha
e ku mu kawar daku yafi." Murmushi yayi mun.

"E Innata ina sonta.

Kuma mun gama daidaitawa da'ita.

Nayi magana da Umma tace babu damuwa in
an bata lokaci tukunna, zata sa ayi mata bincike akan gidansu yarinyar, da irin a
idaar da iyayenta suke kai.

To dama ina da
an wasu ku
e dana tara sabida hidimar bikin in ya tashi." Da
i naji sosai.

Dauda akwai hankali sosai..

To abinda zan fa
a muku shine kuji tsoron Allah akan matan da zaku rabosu da danginsu, da iyayensu ku dawo dasu
ashin cewarku, da kulawarku.

Bazan laminci ku auro yara ku zo ku na tozartasu ba Dauda.

Ban yarda da raina mace ba, domin mata sunfi gaban raini a idanun duniya baki
aya.

Duk isa da burun
asar namiji mace itace a tsaye a bisa rayuwarshi.

Nasan ai ba zaku so a wula
anta muku Amina ko Balaraba a gidan miji ba ko?

To muddin bakwa son hakan ya faru, to ku ri
e yaran mutane tsakani da Allah.

Sannan kar dan mace ta hayayyafa, ta sukurkuce kuce zaku rainata, ko tunanin kunfi
arfinta.

Wannan ba hali bane mai kyau.

Duk yanda matarku zata zama kuyi ha
uri ku gyarata yafi muku sau dubu akan ku sake kawo wata.

Mu mata tamkar fulawa muke.

Yanayin yanda aka kula damu yanayin kyan da zamu yi.

Yanayin yanda aka
i kulawa damu yanayin yamushewar da zamu yi.

Bazan yafe ma
aya a cikinku ba in kuka wula
anta yaran mutane, kuka mayar dasu bola kamar yanda iyayenku maza su ka mayar dani a baya.

Ku ji tsoron Allah, ku hidimtama iyalanku.

Ku basu damar yin karatu, ku taimaka musu da aikin gida a yayin da suke karatu.

Ku basu damar fita su yi aiki, ko kuma ku basu jarin da zasu dinga jujjuyawa, ta hakanne zaku samu abinda ku kan ku kuke so.

Kar ku tauyesu da yawa.

Amman bance ku sake su sakaka ba fa.

Ku sa idanu sosai akan matayenku.

Ku tsaya tsaiwar daka akan addininsu.

Jahilci shi ne matsalar da yawan
an arewa, da rashin wayewa.

Ilimi dama shi ke kawo wayewa.

To mu a Arewa ba mu fiye damuwa da ilimi ba.

Musamman ilimin
a mace.

Kai Dauda a nan gidan zaka zauna, ka soma gyaran
akin da su Amina suke ciki, ciki da falo da ban
aki ai ya isheku.

Su sai su koma dayan
akin su ci gaba da ha
uri kafin suma su tafi nasu gidan mazajen.

Gobe zamu je Shanono gidanku, kaga
an uwanka suma su ganka, ka ga wancan karon da nace zamu je, aiki bai bani dama ba" Shiru su ka yi kamar ruwa ya cinyesu.

Ashe dukkansu hawaye suke yi.

Dauda ne ya soma magana cikin kuka.

"Innata ko da wasa bazan wula
anta
ar mutane ba.

Domin bazan so ai ma mahaifiyata, ko
annena haka a nasu gidan auren ba.

Mun miki al
awarin kiyaye hakan da izinin Allah.

Innata kiyi ha
uri ki dena tuno irin cin zarafinki da su Baba su ka yi a baya.

Dubeki a yanzu Innata.

Kin samu ilimi, kinyi kyau, kina tare damu yaranki, kin inganta rayuwar iyayenki.

Babu abinda zaki nema a duniya ki rasa in dai muna numfashi.

Zamu sake ha
e kammu domin baki farin ciki" Kuka ne yaci
arfinshi dole yayi shiru.

Nima hawayen nake sharewa ina jin zafi a zuchiyata.

Sani kuwa dake mai zuchiyane ya
i magana fur sai zuchiya yake ha
iyewa kawai.

Ku yi shiru ya isa haka.

Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka" Dauda ya ri
e hannun Sani gam suka fita.

Habiba Bala ce ta shigo ta same ni ina share hawaye.

"Shanono ki fito ku gaisa da surikin naki.

Masha Allah baki ga surikin namu ba Shanono.

Yarinya tayi babban kamu" Da
i ne ya lullu
emun zuchiyata.

Ba shiri na yafo mayafina na fito falon.

Babban mutum ne sosai, ya sha malum_malum na blue
in yadi, harda
ar furfurarshi ka
an.

A shekaru zai kai shekarun Amadudu.

Yana ganina ya zube har
asa ya gaisheni cikin girmamawa.

Da fara'ata na amsa mishi.

"Yaya jikin naki Umma?

Amina tace mun baki da lafiya.

Jiki Alhamdulillah.

Ya wajen iyayen naka kowa yana lafiya ko?*
"Suna lafiya.

Mahaifiyata ma tace in mi
a sa
on gaisuwarta gareki" Kai na girgiza nace.

Ayya ina amsawa nagode" komawa yayi ya zauna a kujera.

Habiba Bala tace.

"Amina bamu waje zamu gana da Khalid ko?"
akina ta shige, kanta a
asa sai kunya take ji.

Shigarta ke da wuya Habiba Bala tace.

"Khalid yarinya ta sanar damu kana son zaka turo magabatanka domin a tsayar muku da maganar Aure ko?" Murmushi yayi yace.

"E haka nace mata.

Sabida mahaifiyata ta matsa sosai a kan batun auren"
"Okay.

Amman kafin a kai da maganar magabata muna son ka bamu lokaci dan mu gudanar da binciken daya dace.

Kaima kana da damar gudanar da bincike ta
angarenku.

Muna son ganin asalinka, aikinka da unguwar da kake zaune.

Kayi ha
uri kar kaji cewar ko muna son yi maka titsiye ne.

Kasan sha'anin aure dole sai an tsananta bincike sabida yanayin zamanin, yanzu babu wuya kaji Aure ya mutu" Zama ya gyara yace.

"Hakane Umma babu komai ai.

Nima iyayena suna can suna gudanar da nasu binciken a kanta.

Ni dai haifaffen garin Kaduna ne.

Iyayena
an unguwar ma'azune.

Mahaifina Alh Adamu mai agogo sanannen mutum ne a garin Kaduna.

Ko yaro aka tare daga bakin layinmu yasan gidanmu, ina da tarin yayye da
anne, mahaifina yana da mata hu
u.

Nayi karatu tun daga primary har zuwa mastas, a
angaren injiniyanci, ina aiki da wani kamfani a Lagos a matsayin safety injiniya.

Ina da mata da yara biyar.

Matata tana zaune ne a family house
inmu.

To ita kuma Amina in Allah yayi matatace to zata zauna tare dani a Lagos." Ni dai nayi shiru ina tausayama Amina.

Dan Aure mai mata kuma
an dangi akwai
alubale a cikinshi sosai.

Musamman ga yaran talakawa, duk da dai Kaila yafi
arfin a kirashi talaka, sai dai ta nawa
angaren.

Kuma da dukkan halamu suna tsantsar son junansu sosai.

Habiba Bala ce ta katsemun zancan zuchina da cewa.

"To masha Allah.

In sha Allah zamu neme ka da zaran lokaci yayi, ka
an bamu sati
aya tukunna.

Zamu baka izinin zuwa gidan mahaifinta ka kai ku
i da zaran mun gama bincike."
agowa yayi yace.

"Umman ba acan take bane?

Amina tace mun aiki umma take yi a nan garin?" Kallon kallo mu ka yi ni da Habiba.

Gabana ya yanke ya fa
i ganin irin yanda fuskarshi ta nuna."
"E aiki take yi a Kano.

Amman sun da
e da rabuwa da mahaifinta.

Kasan Aure raine dashi.

Gara a sanar maka da gaskiyar lamarin.

Tunda dai ka fito ka nuna da gaske aurenta zaka yi.

Nan shine inda mahaifiyarta take rayuwa.

Kakanninta na wajen uwa suma ka gansu.

Talakawane masu
arin rufa ma kai asiri.

Ina fatan hakan ba zai zama matsalaba ko?" Murmushin dake kan fuskarshi take ya ragu, na fahimci ya
e yake yi.

A haka muka gama ganawa dashi muka koma ciki.

Amina kuma ta fito ta sameshi.

"Shanono Khalid na fahimci yanayinshi ya canja da na sanar mishi ba kya tare da Kaila.

Anya wannan neman auren kamar ba zai yi
arko ba fa.

Baki ga yanda ya kasa
oye damuwarshi ba"
Habiba Bala.

Ai ni kina gama sanar mishi.

Yanda ya nuna sai naji jikina yayi sanyi sosai da sosai.

Gashi na lura ita Aminan tana son shi da yawa.

Ni bana yi mata sha'awar auren mai mata ta je a ta biyu.

Bana mata sha'awar shiga gidan yawa.

Matsala ake samu sosai.

Sai kiga ana gorantama yaro akan abinda bai taka kara ya karya ba.

Habiba Bala, ni fa jikina yayi sanyi, hankalina bai kwanta da ha
innan ba" Dafa kafa
ata Habiba Bala tayi tace.

"Mu yi adda'a Shanono.

In da Alkhairi Allah ya tabbatar mana.

In babu Alkhairi Allah ya kawo mata mafi alkhairi." Amina ce tayo sallama, na bata izinin shigowa.

A sanyaye ta shigo.

"Umma Habiba kina da ba
o a falo" Kallonta nayi nace.
Chapter 8 · 0% Book details