← Book details Na Fado Daga Bene Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 35

Sashe 11

Na Fado Daga Bene Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki yarda dashi ki bashi dama Shanono.

Ki amince da aurenki da yake so yayi.

Wannan itace alfarma guda
aya dana ta
a nema a wajenki.

Dan nasan zaki iya sadaukarwa domina ne yasa har na ro
i alfarmar.

Shanono wallahi ina da dalili mai
arfi.

Zan miki bayani mai kyau daga baya, kin amince, ko zaki tula mun barkono a idanuna Shanono?" Wawuyar Ajjiyar zuchiya na sauke, hawaye ne shararararararara yake zuba a idanuna ba tare da ina da ikon hanashi zubar ba.

Habiba Bala ta gwara mun kai, ta birkita mun tunanina, ta kuma
aureni tamau da jijiyoyin jikina.

In nace mata na amince bansan ya hala
ata da yarana zata kasance ba.

Bansan da wanne idanu ita kanta duniya zata kalleni ba.

In kuma nace mata ban aminceba, na cika butulu mai mancewa da dukkan alkhairi.

Kuma Habiba Bala zata kalleni a matsayin wacce bata san Alkhairi ba.

Gaba kura baya sa ya
"Shanono baki amince ba ko, kinji ba zaki iya auren yaro ba ko, sabida su Sani right?

Duk zan zaunar dasu da kaina in yi musu magana ta fahimta.

Sani farin cikin ki yake so.

Kuma zai yi alfahari da wannan Auren da yardar Allah, zai kuma amshi Jega a matsayin mijin uwa."
Na amince Habiba Bala.

Ko da hakan yana nufin mutuwatane.

Ban isa nace miki A'a ba Habiba Bala wallahi ina jinki a raina fiye da yanda nake jin Yaya Use da Yaya Karime." Murmushi tayi mun ta share hawayen daya zubo mata.

Ta kama hannuna bata ce dani uffan ba muka nufi cikin asibitin.
ofar wani
aki ta tura muka kutsa kanmu.

Ni dai binta nake yi tamkar ra
umi da akala.

Jega na hanno a kan gado yana baccinshi hankali kwance.

Ga robar
arin ruwa sar
afe da hannunshi.

Matarshi Khadija tana kujerar dake kusa da gadon ta kifa kanta a jikin katifar gadon.

Tausayi ta matu
ar bani ainun sai naji kamar in zubar mata da hawaye.

A fa
a ma za'ayima kishiya ba
aramin tashin hankali mai girma bane.

Sai da akaimun kishiyoyi sau
aiya har sau takwas.

Kaidi da makircin kishiya babu wanda ban haddace shi a wannan kan nawa ba.

Ni naga yanda ake makirci da ma
e a wajan miji.

Kishiya na bani tsoro ainun.

Wasu dattawa biyu na gani a zaune a 3 sitter sai wata
ar dattijuwar mace daga gefensu.

"Amarya wannan itace Shanonon?" Wani Tsoho tukub ya tambayi Habiba Bala.

Da gani shine mahaifin Alh Nura, ga kamannin na jini ya nuna.

"E Alhn Sama itace."
"Tawo jikata ki zauna mu yi magana" Jikina a sanyaye na isa kusa dashi na zauna akan tabarma.

Wannan Dattijuwar mace ta dubi Khadija tace.

"Khadija tashi kinji ki tafi gida, ki samu ki
an yi wanka yaran su ganki.

Ga ki da yaron ciki.

In an gama abincin dare sai ki tawo dashi" murmushi khadija tayi tace.

"Goggo in ya farka zai neme ni.

Ba damuwa zan zauna, yaran suna gidanmu"
"A'a jeki ki huta kema, za'a kula miki dashi" A yanda na fahimta tabbas bata san abinda ke faruwa ba.

Kuma ba'aso ta sani yanzu.

Hakanma da su ka yi sun girmamata sosai.

Jakarta da basket
in kayan abinci ta
auka ta fita.

Alhn Sama ya dubeni yace.

"Jikata naji duk abinda ya faru.

Nayi fa
a kamar zan ari baki.

Shima kanshi Nura na ci mishi mutunci sosai akan hukuncin daya yanke.

Kin ganni nan?

Na auri mahaifiyarsu ina da shekara talatin a duniya.

Ita kuma a lokacin shekarunta arba'in cib.

Ta auri mijinta na fari Allah bai yi zaman su yana da yawa ba.

Mahaifiyarshi tasa ya saketa.

Wai bata haihuwa.

Haka A'i ta fito ta fa
a zawarci, gaga_gaga masoya su ka sake far mata.

Da ke tana da kyau farace wanke hannu ka ta
a.

Allah yai mata katari ta auri wani hamsha
in mai arziki a wannan zamanin.

Allah cikin ikonshi ko shekara bata rufa ba Allah yai ma Alhn rasuwa.

A'i ta fito da tuminin takaba mai yawan gaske, motoci da gidaje, dan mijin nata mai sukunine sosai.

A kasuwa Allah ya ha
a ni da A'i lokaci
aya ta shiga raina ainun.

A lokacin ni keke ne dani, ita kuma mota marsandi take ja fara bazan mance ba.

Haka nabi A'i a kekena har gida naga waje.

Da daddare na sha jar dara da tabarau, da turarena
an duwala na kama hanyar gidansu A'i.

Kinji na rantse sai dana tarar da maza biyar suna jira A'i ta sauraresu ni na zama cikoton na shida.

Tana ganawa da wani babban mutun yazo a babbar motarshi ta masu ku
in zamanin.

Haka A'i ta dinga bin mazannan
aya bayan
aya tana saurarensu.

Na fa
a miki Allah yayi mata kyau, gata da farin jinin masu arziki.

Ni kam da A'i tazo kaina ma dariya tayi bayan na fallasa mata asirin zuchiyata.

Ta kama hanya ta tafi ta barni a wajen.

Na miki tsallake Shanono.

Kafin in iya furta mata kalmar so sai da nayi namijin
ari, dan gabana tattakewa ya dinga yi yana fa
uwa.

Nasan ta fi karfina takota ina.

Ni kuma gashi na jarabtu.

Ba'a ma so fishi.

Gaga_gaga kullum sai nazo gidansu A'i wata ran ta fito, wataran ta koro
an aiken.

Ni dai ban gaji ba, banji halamun sarewa ba sam.

Yau da gobe kuma da kike ganinta tafi
arfin wasa.

In Allah ya
addara maka sai ka auri mace.

Baka da tsumi.

Wata ranar juma'a da yamma lis na nufi gidansu A'i sai na samu an cika a
ofar gidansu kamar hayaniya akeyi.

Ina
arasawa na tarar maneman A'i ne musayar yawu ya shiga tsakaninsu.

Har mahaifinta yana fa
in shi dukkansu babu wanda zai ba auranta.

Ina zuwa wajan sai A'i ta ka da baki ta ambaci sunana.

Bu
ar bakin mahaifinta yace.

"Ahmad in kana son A'i kuma a shirye kake kazo da magabatanka zuwa gobe da safe a
aura muku aure.

Wallahi Hakanne ya faru kamar almara washe gari aka
aura aurena da A'i ba dan fa tana sona ba.

Shanono, na sha wuya a hannun A'i har tsawa take daka mini.

Shinfi
arta kuwa ban isa naje ba.

Ni kuma na nuna mata soyayyarta a jinin jikina yake yawo, ba farar fatarta ko kyawun fuskarta nake so ba.

Shekararmu biyar muna zaman doya da manja.

Kyautatawa, da tausayi, da nuna tsagwaron soyayya yasa A'i ta yi mubayi'a ta mika mun zuchiyarta na kula da'ita.

Na bata lokaci na bata soyayya, na bata girmanta.

Yaranmu uku da'ita Allah cikin ikonshi A'i ta tafi ta barni.

Har abada babu madadin A'i a duniyata.

Yaran data haifamun sune rayuwata." Kukane yaci karfin wannan Dattijo mai kama da majnun wajen iya soyayya, ko kuma in kirashi da diyago na paloma.

Ni kaina wannan soyayya ta A'i da Ahmad ta burgeni ainun.

Wannan Dattijuwar tace.

"Alhn Sama sai ha
uri Anty A'i sai dai mu bita da adda'a mace ta gari kenan.

Mu kammu muna jin jikin mutuwarta ballantana kai.

Allah ya ji
anta da duk musulman da suka kwanta dama." Kowa a
akin muka amsa da
"Ameen" Kafin
ayan Dattijon yace.

"Shanono babu haramci a aurenki da Ahmad.

Ko da kinfi haka tsufa ne, shima ko da yafi haka yarinta.

Wannan kyakkyawan koyi ne mai kyau.

Kuma babu inda kika ji an rawaito dole bazawara sai dai ta auri magidanci, ko bazawari
an uwanta.

Shi saurayi, ko mai
arancin shekaru kamar Ahmad bashi da dama da ikon auren mace kamarki kenan?

Ko kusa yana da dama, kema kina da damar aurenshi matsawar yayi miki.

Sai dai in baya cikin zubin mazan da kike son yin rayuwa dasu ne, wanna
n kuma wani abunne daban.

Bazawara ba abar
yama bace, bazawara abar a tausaya matane.

Amman a nan
asar Hausa mun fi zagin Zawara akan karuwa ma.

Kuma shi mutuwar aure ba haramun bane.

Haka siddan namiji zai iya sakin mace.

Kamar yadda haka siddan mace zata cukume miji tace sai ya saketa.

In dai tayi rantsuwar ba zata zauna dashi ba.

Ya zame mishi dole ya saketa.

Shanono mu dai mun amince da nemanki da Ahmad yake yi.

Amincewarmu ta isa a shafa fatiha.

Mu ro
on da muke miki ki yi ma Allah ki bashi dama ku fahimci junanku.

In yayi dai_dai da irin namijin da kikeso falillahi hamdu.

In bai yi miki ba shikenan." Alhn Sama yace.

"Jikata in dai da
in soyayya kike son sani to ya
are a wajen matashin daya auri babbar mace.

Ba ke ba takaicin
a namiji.

Ni nake fa
a miki wannan magana.

Ki daure ki bashi dama, ni dai har ga Allah ina sonki kuma babu wanda ya isa ya ci mutuncinki in barshi.

Yanda nayi tsaiwar daka wajen ganin na kare martabar A'i.

Kema zan miki hakan.

Ahmad ma yana tare dake.

In na ganki sai inga kamar A'i ce" Nan ma kukan ya kuma sawa wannan karon har dani a rarrashin nashi.

Kaina a
asa kunya na neman halakar dani.

Duk sun yi tsit ni suke saurare su ji me zance.

Baba ba damuwa na amince.

Zan kuma bashi dama in sha Allah.

Nagode da kulawarku a gareni.

Ha
a Habiba Bala kin more da dangin miji masu farar zuchiya" Kuka na saka musu nima.

"Jega ka farka?" Cewar wannan dattijuwar.

Kukan da nake yi na yi saurin ha
iyewa.

Alhn Sama yace.

"Habiba a kira likita ta duba shi." Da sauri Habiba Bala ta fita.

Alhn Sama ya dafa kaina yace.

"Allah yai miki albarka ya raya miki yaranki rayuwa irin ta addinin Musulunci.

Share hawayenki kinji?' Kai na
aga mishi na share hawayen nawa.

"Zo ki zauna ga wuri.

Bari mu fita daga waje likita zata shigo dubashi." Fita su ka yi suka barni a zaune a
asa na juya ma gadon da Jega yake baya.

Sai da naji rufe
ofarsu kana na mi
e, na zauna a saman kujera.

Kallon kallo ne ya shiga tsakanina da Jega.

Bai san ni bace a zaune a gaban su Alhn Sama ba.

Kuma da ganin fuskarshi bai ji duk abinda muka tattauna ba.

Sai na yi farin cikin hakan.

Ya kasa ce mun komai sai kallona yake yi kamar zai cinyeni.
Chapter 11 · 0% Book details