← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 92 OF 100

Sashe 92

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"please yaya !ta fad'a tana wani irin kuka mai d'aga hankali kalmamin mumy da ta dinga fad'a a wannin data gabata wanda mami ta fad'a mata ne ya dinga dawo mata daki daki ,tunda har mami ta amince da aurenta da yaya hisham bazata ta'ba kin auren nan ba, domin tayi imani ace yaya hisham ba na gari bane mami bazata yarda da hadin ba hannunsa yasa ya d'agota yana share mata hawaye dake gangaro mata sannan ya rungume ajikinsa yana d'an dukan bayanta" wannan shine karo na farko da yayanta yayi mata haka a tun tasowarsu " daman haka yake tsananin sonta ?daman akwai ranar da zai nuna damuwarsa da kulawarsa gareta "?shiru tayi ajikin yayanta tana sauke numfashi ."

Ahankali ya zareta ajikinsa ya zuba mata idanuwanshi itama shi take kallo hawaye na sake cikowa a idanunta "shikenan auta allah yasa albarka yana gama fad'ar haka ya juya Jiki babu kwari ya fice daga d'akin cikin wani irin yanayi na tashin hankali "shi dai har ga allah wannan hadin bai yi masa ba babu yadda zaiyi ne kawai ."

Sunkuyar da kanta kasa tayi ta kasa hada idanu da jamar dake falon babu wanda bata burge ba hatta baba qarami ya jinjina mata domin yasan ba kowa bane zai iya yin abinda tayi haka muke fata a kowani lokaci idan mukayi umarni ya kasance kunyi mubaya'a wannan shi zai sake tabbatar mana da irin tarbiyar da muka baku mun gode da biyayya da hukuncin da muka zartar akanki dan haka ina miki albishir da cewar zaki samu farinciki inji cewar hajiya zulfa'u ta kamota zuwa jikinta "my dear dan Allah ki ramin bala direba zai kai wani waje " kai kawai ya gyada mata sannan ya ciro wayarsa ya soma neman layinsa yayinda tayi hanyar waje da nana hauwa'u ta barsu suna cigaba da tautaunawa har d'akinsu inda ta d'aukota ta maidata tana cewa "bani wasu mintuna zan dawo yanzu kai kawai ta gyada mata sannnan hjy zulfa'u ta juya ta fita daga dakin alokacin bala direban ya iso yana tsaye a haraban gidan ya juya kan mota yana jiranta yana ganin fitowarta yayi saurin fitowa ya bude mata gidan baya ta shiga motar ta zauna tana bashi umarnin inda zai kaita ya amsa mata da "tô!."ya rufe mata murfin motar ya shiga mazaunin direba ya tada mota suka fice daga haraban gidan ."

Hjy zulfa'u na fita daga dakin nana hauwa'u ta kwanta lamo ranta duk babu dadi tunani ne ya lullubeta ita kanta tasan gsky yayanta ya fata mata aure ana ginasa ne akan soyayya domin samun zaman lafiya kuka nana hauwa'u ta fashe dashi wanda har maryam da diyana suka shigo bata sani ba mrym ce ta isa wajenta tare da dafe qirji tana cewa " Sister lafiya me ya faru ?kuka ta cigaba dayi batare da ta bata amsa ba dan girman allah ki fada min me ya faru ."

Diyana ta riko hannunta "me ya sameki hk kike wannan uban kuka haka "nice zan maye gurbin nuzla a wajen yaya hisham "what ?suka had'a baki ta kwanta ajikin mrym da tafi diyana shiga tashin hankali hawayenta take ji ajikinta ta ma rasa me zatace "nima shikenan rayuwata tazo karshe nasan yaya hisham bazai so ni ba tunda nuzla yake matukar só? mrym ta d'agota daga yadda ta kwanta ajikinta "wai wa ya zarta da wannan hukunci ?"shigowar da mumy tayi d'azu nan tayi musu bayanin komai "am very sorry kema da laifinki taya zaki amince mata inji cewar diyana ."

"yaya zanyi bazan iya zuba mata qasa a ido ba mumy ta wuce hk awajena bani ba nasan ko ke tayi wa mgn zaki amince mata bugu da gari mami ta amince diyana bata sake cewa komai ba tunda taji mami ma ta amince ,mrym kam rarrashinta take tana karkafa mata gwiwa "tunda mami ta amince ki kwantar da hankalinki kece fa ke bani kwarin gwiwa kina són naji bani da wannan kwarin gwiwar né ."?ta girgiza kai "tô dan girman allah kiyi hakuri kiyi shiru mu barwa allah komai ."

bangaren ATA zuciyarsa a cunkushe ya shiga d'akinsa bakinciki abinda nana hauwa'u da auren dole da mahaifiyarsa zata masa na sake ninkuwa ,wani irin zafi zuciyarsa ke masa zuciyarsa na matukar zafi ya bud'e qaramin fridge dinsa ya d'auki gorar ruwa tare da kafawa a bakinsa sai daya shanye tas sannan yayi wurgi da roban."

Ahankali ya zame ya zauna akan kujerar kushin "wai me yake faruwa dani né komai ya zama worst agareni shine tambayoyin daya cigaba dayiwa zuciyarsa sam ruwan bai sanyaya masa ransa ba dan damuwarsa na nan bata ragu ba babu abinda yake bukata kamar sigari dan irin sarawar da kanshi yake a yau din nan dole ya had'a da sigari idan ta kama har da giya a hada masa dan yana buqatar ya bugu iya bugawa ya kira daya daga cikin yarasa yace ya kawo masa ta'ba sigari kwali ashirin yana gama wayar ya kwanta yana jiran Peter ."

Bai dade da kwanciya ba aka soma knocking kofar falon yana daga kwance runtse idanushi daga shi sai wondo baki da riga hamles ash colour ya bada umarnin shigowa peter ya shigo cikin falon hannunsa rike da leda cike da girmamawa ya rusuna ya gaisa da ogansa ATA ya yunkura ya mike zaune ya amshi ledar had'e da bude wata durowa dake gefensa ya zaro bandir din fararen yan dubu day day ya mika masa sannan ya bude ledar ya zaro kwalin sigari ."

karba peter yayi ya cigaba da tsayuwa "kaje ka siyo min giya kwalba biyar mai kyau ka kawo min yanzu yanzu ."ya fad'a yana d'aura sigari abakinsa Kallonsa peter yayi cike da mamaki dan tabar ma ya jima bai aikesa ba ".

"amman boss ....." just leave "babu shiri peter ya juya da sauri ya fice daga falon sigari ya soma zuka ko kafin peter ya dawo ya shanye kwali biyu yana kan na uku cike da girmamawa zai ajiye masa yace ya bashi kwalbar giya biyu yasa sauran a fridge ya nuna masa fridge sannan yace d'auko masa glass cup ya d'auko ya mika ya kama gabansa yana janyo masa kofar ."

ATA ya kashe wayoyinsa gabadaya sannan ya balle kwalba giya ya tsiyaya a glass cup ya kai bakinsa bai ji komai ba dan babu abinda yafi bukatar alokacin kamar ya bugu ,yana son ya manta komai ciki kuwa har da mafarkinsa ya shanye tass ya sake tsiyaya wani yana sha yana zukar sigari wani irin zuka yayi wa sigarin yana kwantar da kanshi akan kujerar da yake zaune sai daya dauki second biyar sannan ya d'ago ya kalli sigarin hannunsa daya kusan qarewa ya sake kaiwa bakinsa ya zuga da kyau ya d'auki cup din giya ya shanye yana fesar da hayakin sigari ."

sosai ya bugu ya fita haiyacinsa can ya mike yana layi ya shiga d'ayan d'akinsa ya d'auko tanga memen hoton zanen princess dinsa ya rungume tsam a qirjinsa yana jin wani tsantsar soyayyarta na ratsashi "ina ...ina sonki princess wai a ina zan ganki ne?
" ki fada min inda zangaki mana yana magana yana kallon hoton ya fito falo ya zube akan kujera rungume da zanen a qirjinsa daga nan wani bacci mai nauyi ya daukesa bai sake sanin halin da yake ciki ba ."

Hisham yana zaune yana faman kiran layin nuzla mahaifiyarsa hajiya zulfa'u ta amshe wayar hannunsa tana dubansa "zaka kashe kanka ne akan yarinyar data gudu saboda bata sonka ko me ?"haba mumy ko nuzla ta gudu dan bata sona still akwai yan'uwantaka a tsakaninmu" ban son iskanci ba yanuwantaka ba kune ma kashin awaki qarewar yan'uwanta duk yan'uwantakan dake tsakaninku ya kai ta nida mahaifinta ?

"karka manta nida mahaifinta uwarmu daya uban daya dan haka wallahi Kayi maza ka cireta aranka ai dana san gantalliyar yarinyar nan bata sonka bazan kashe kaina akanta ba "mumy ki barni naji da damuwa dake damuna please "damuwa ai ta qare kamar yadda aka saka ranar daurin aurenka a gobe tabbas a gobe zaa daurashi "Yauwa mumy har kin sa naji dadi bari na tashi na fita nemanta ko allah zai sa na ganta ."

Wani dogon tsaki taja tana dubansa "hisham ka natsu da kyau zaa daura aureka ne amman da wata ba nuzla ba kuma acikin family din nan kamar yadda muka yanke hukunci "what mumy ? haka nake nufi dan allah mumy karki min haka wallahi ni nuzla kawai nike so bazan iya rayuwa da wata ba ,dan allah kar abinda tayi yasa ki yanke wannan hukunci akwai kuruciya a tattare da nuzla wallahi bata da wayon kanta ."

" min shiru a nan kuma karka sake min maganar wata nuzla idan ba haka zaka hadu da mummunar baci raina da baka ta'ba gani bata da wayon kanta tasan ta gudu ta bar gida "? tana gama fadar hk ta tashi zata bar falon ya riko hannunta cikin nashi duk ilahirin jikinsa babu inda baya rawa hatta hannunsa dake rike da hannun mahaifiyarsa kirrrma yake yana sake damke hannunta da kyau "ki tausaya min ,ni zaki duba mumy da halin da zan shiga nuzla wata abace mai daraja acikin rayuwata karki maye min gurbinta da wata cike da jin haushi ta fixge hannunta "for the last time karka sake min maganarta sha sha kawai da bai son ciwon kansa ba yarinya ta gudu ana gobe daurin aurenku amman ka tsaya kana fad'a min tana da daraja acikin rayuwarka tunda ta gujeka na tsaneta Ka shirya karka manta karfe hud'u daidai zaa tafi diner "what? ai kasan da zuwa wajen diner dan hk karka bata lokaci tana gama fadar haka ta bar dakin kai tsaye wani haddaden office din gyaran jiki ta nufa ."

Nan da nan ya kira salim cikin tsananin tashin hankali bayan sun gaisa ya fad'a masa halin da yake ciki salim din ma kwantar masa da hankali ya dinga yi" kayi hakuri da hukuncinsu hisham ya rude ya rasa abinda Ke masa dadi amman me yasa zaa min haka bayan an bada cigiyarta a kafafen sadarwa to dawa zaa hadani auren "?shiru salim yayi na second goma sannna yace "nana hauwa'u "
Chapter 92 · 0% Book details