Sashe 43
Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
*****
Bayan kwana biyu da faruwar wannan alamarin maryama tana tafiya cikin kayan islamiyya ta Ardus-salam yayinda hannunta ke rungume alqurani , yammaci ne duk mazan unguwarsu sun dawo daga aiki duk inda ta wulga sai an kalleta da shaawar tafiyarta tmkr bata son taka qasa tana cikin tafiya taji tafiya abayanta bata juya ba dan hakan baya daga cikin d'abiarta , sai ma qara saurin da tayi ta cigaba da tafiyarta saboda tasan kowaye ita yake bi zarginta ma cikin samarin unguwarsu ne dan akwai masu nuna suna sonta acikinsu ."
"maryama wannan uban sauri haka da kike zabgawa ko dan gudun kar na biyoki ne ?ta tsaya cak lokacin data fahimci muryar malamin islamiyyarsu ne na Ardus-salam mlm yahuza ta juyo a natse ta dubeshi cikin nikaf dinta tare da girmamawa ta gaishesa ."ya gyara tsayuwarsa yana kallonta , kunyarta ita tafi komai tsoratashi ,duk iya takun saurayi in har ya had'u da mace mai kunya yana samun karaya matuka a zuciyarsa ."
yayi dan murmushi irin nasu na ustaz "maryama har kullum zuciyata bata da sukuni jiddan wala khairan ,na kasa mantawa dake ,bani da wani sukuni face na samu amsarki game da bukatata dana kawo miki ."yayi shiru tare da tsayawa yana sauraron yaji me zatace nan take tayi kicin kicin tamkar wacce aka tsare da wuka zaa yankata sai da ta dauki second goma sannan tace "uhm !sai kuma tayi shiru ta qasa qarasa abinda zata fad'a maganar ta makale acikin zuciyarta shi kanshi ganin motsa lip's dinta bai sawa ranshi cewar zatace uffan ba bayan abinda ta furta ba ."
ba yau bane farko haka zalika yasan ba yau bane zai zama karshe ya saba tareta a hanya ta kasa ko ambaton sunan shi bama shi kadai ba kusan mutane suna yawon fad'ar haka akanta bata da yawon surutu da saurin sabo da mutun duk wanda ka ganta dashi tana d'ar d'ar alamun tsoro shima dan matsayin da yake dashi na malaminta ne yasa har ta tsaya akan hanya babu wanda ya kai ta tsaya dashi akan hanya ".
"Maryama idan na lura da yanayin fuskarki ba soyayyata bace baki amsa ba amman kuma bazan tabbatar akan cewar kin amsa ba ,tunda a kwayar idanunki kawai nake iya karantawa shine kunya ce ta hanaki ki fad'ar abinda Ke cikin zuciyarki maryama ki daure ki sanar dani menenê acikin zuciyarki akaina ko zuciyata zata samu sukuni da natsuwa ?".
shirun dai da baya só shi tayi dan bata da abinda zatace masa ,bazata iya wata soyayya ba da'ace ta d'aurawa kanta soyayyar samari da lokacin da suke guduwa suna barinta da ba qaramin tashin hankali zata shiga ba gara ta qarasa rayuwarta haka tunda soyayya ba dole bane arayuwar mutun haka ma aure sunah ne matukar mutun zai iya rike kanshi domin acikin
Sahbbai ma akwai wad'an da suka mutu basuyi aure ba dan haka mutun zai iya zamansa haka kuma aure da haihuwa bashi bane karshen duniya a ganinta ko babu shi mutun zai iya rayuwarsa ."
"hakika maryama duk cikin unguwar nan kai garin nan ma gbdy har cikin islamiyyarmu banga diya macen da take burgeni kuma zuciyata take dawainiya da tarin soyayyata kamar ki ba ki samar da amsar soyayyata a cikin zuciyarki ko zan samu farinciki da sukuni koda ta wata sigace da zan fahimta ."sosai hankalinta ya kai kololuwar tashi tama qasa tsayuwa bisa kafafunta , kafafunta suka shiga karkarwa ,yana son ya bata dama ta wuce gida saboda halin daya karanta atattare daita amman kuma bai gaji da kallonta ba kuma shi yasani ko zai kwana tsaye atare daita bazai gaji ba , sakina da kanwata ne suka zo zasu giftasu malam yahuza yayi sauri yace "sakina ku tsaya ga maryama tsaye ku wuce gida tare ."
Shukura ta kallesa tana jin wani irin tuttukin bakinciki acikin zuciyarta abun yayi matukar bata mamaki maryama tare da mlm yahuza malamin da take matukar só amman tsoro da shakkansa ya hanata fito da soyayyarsa
"malam ! kawai tace tayi gaba tana jan tsaki acikin ranta dan tasan muddin tayi a fili ta kad'e har ganyenta dan mlm yahuza babu wasa wajen disfila d'alibai da iya karatu da d'aukar wanka ga tsantsar kyau shiyasa kowani d'alibi ke matukar jin tsoronsa a kaf ardus-salam babu malamin da'ake shakka da só kamarsa da yawa yammata na qaunarsa ."sakina kam jikinta a matukar sanyaye ta wuce batare datayi mgn ba maryama ta bita da idanuwanta wani abu ya soki zuciyarta domin tun safiyar yau ta lura sakina ta canza mata abun ya matukar d'aure mata kai amman tayi mata uzuri da cewa yanayin rayuwa ne ."
Mlm yahuza bai sake magana ba sai tunanin kunyar shi da sakina taji dan ganinsa da maryama yasa ta kasa tsayawa dan haka yace "maryama sai gobe idan mun had'u a makaranta amman fa kisani bazan ta'ba daina tsaidake anan ba har sai ranar dana samu na cire kunyar nan kika amince min "Kanta kawai ta gyada masa muryata a matukar sanyaye tace "sai da safe ta juya ta cigaba da tafiya a natse bai bar wajen ba sai da tayi nisa sosai ta 'bacewa ganinsa ."
yana juyawa sukai ido biyu da mlm umar mai hausa atare sukai murmushi "wato kai har kullum bazaka daina wahalar da kanka akan maryama ba ko ?"Mlm yahuza ya qarasa inda mlm umar yake ya tsaya yana cewa "ya zanyi umar allah ya jarabeni da soyayyar maryama bazan iya hakura daita ba "kai kuma allah ya jarabi mata dayawa da sonka ba ?"wannan kuma damuwarsu ce ,ai dama haka zaka fad'a duk kuna son maso wani ,kai ma ka tausayawa masu sonka sai allah ya duba lamarinka ".
"Allah ma ya sani babu wacce nasan tana sona bare na tausayawa ya fad'a yana wani sham kamshi "Uhm uhm mutumina banda fad'ar son rai duk wanda ka fadawa haka zai d'auka bakasan abinda kakeyi ba ,"kaga umar rabani da wannan zance mu barta matsawar bata sarauniyar mata zaka min ba "karka duba yanayin gidansu maryama amman dai kai kanka kasan tafi karfin aurenka , maryama macece daya kamata wani hamshakin mai kudi yayi wuf daita ."
dan murmushi mlm yahuza yayi yace "haka ne amman ai duk mace bata fi karfin auren nmj ba kuma kowani mutun yana da nashi matsayin da zai iya burge mace , kuma ina dashi ina da quality da mace zata soni koda kuwa bani da kosisi bugu da qari ita mace ba kudi take bukata a soyayya da kulawa take so ni nan kuma zan kula da maryama ."
"da me zaka kula daita ?karka manta ita din cikakkiyar 'yar boko ce , yarinyar da idan ta fara aiki yanzu sai ta d'auki nauyin ciyar da mutanen gidanku gbdy dan haka banga abinda zai sa ka dinga wahalar da kanka kana 'batawa kanka lokaci akanta ba , kayi hakuri ka rabu daita domin dai babban goro sai magogin karfe ."
Mlm yahuza ya dan ji zafin maganar malam umar dan haka ya rage farar fuskashi "wai me kake nufi ? kana nufin dan ita din yar boko ce tana da kyau na bugawa a jarida kana tunanin zata samu aiki nan gaba zai sa ta iya fin karfin halittar ubangiji "? yahuza abinda nake son ka fahimta duk wad'an nan abubuwa da kake gani fifiko ne a tsakaninka da maryama kawai abinda nake so kaji aranka tafi karfinka tafi karfin aurenka ."
"kaga dan allah mlm ka barni ka zuba min ido ba wahalar banza nake yi ba ina cikin zuciyarta kunyar da take yawon nunawa akaina ta wadatar dani cewar nayi mata , nan gaba kad'an zata fahimtar dani ."Ka dai bi a sannu kar wata rana kana zaune wani hamshakin mai kudi ya shigo har cikin unguwar nan ya aureta .".
"bari kaji babu wani mai kudin da zai aureta domin suma masu kudin sunfi son ya'yan masu kudi yanuwansu , ita maryamar da ba galihu ne daita ba ,ai ba uban da zai shigo cikin wannan rubabbiyar unguwar ya kwashta ai duk wannan kyawun nata akan irinmu zai qare "yana gama fadar haka ya juya dan baya son ya sake 'bata masa rai ."
Tafiya kawai maryama take zuciyarta cike da kunci da tunani barkatai ba kuma akan mlm yahuza ba sai sabon sauyin data gani akan fuskar sakina dan na shukura mai sauki ne idan da sabo ta saba ita da yaran aunty hassana haka suke mata amman sakina fa basu saba haka ba suna matukar qaunar junansu tun suna yara su din masoya ne na hakika ."
da wannan tunani ta qarasa cikin gidansu kai tsaye ta nufi bangaren su sakina domin tambayarta dalilin sauyawarta ashe wahala ce ta shigo daita tana sallama aunty salma tace " Yauwa maryama d'auki tsintsiyar ki share min d'akuna tas shine amsar sallamar da aunty salma tayi mata kamar tace bazatai ba amman ta kasa ta ajiye alquranin dake hannunta ta d'auko tsintsiya ta fara shara batare da wata damuwa ba ."
tana shara aunty salma na zaginta ita da shukura amman sakina na zaune batace komai ba sa'banin da da bata yarda a zageta ko sakata aiki akan idanunta ,tana shara wani gurin da simiti wani gurin babu ga kuma sakina na zaune ta d'ago idanunta a natse ta kalleta taga kurar sharar na zuwa inda take muryata a sanyaye tace "sakinata ina ganin sai kin d'an tashi kinga kurar tana zuwa inda kike ta wani watso mata harara "ai gudun ruwanki nake kallo naga zaki shareni ko kuwa ."?
maryama tayi shiru tsaye tana karantarta akwai wulakanci acikin maganarta "ke kika kyaleta aunty sakina amman banda jakanta irin nata tana kallon mutane suna zaune zatace su matsa , banza shasha kawai mai siffar mayu ." inji cewar shukara dake zaune kusa da aunty salma abun bai yiwa aunty salma dadi sosai ba domin kuwa sakina taso ta furta ma maryama haka ba shukura ba ,sakina kam tun maganar farko datai bata qara ba ta tashi cikin bacin rai ta shige daki tana jin wani zazzafan kiyayyar maryama ."