← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 11 OF 100

Sashe 11

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Naunayen ajiyar zuciya nuzla da maryam suka sauke atare suna dafe qirji "marsi wallahi ba qaramin tsorata nayi ba ,koni kusan nafiki tsorata wallahi kadan ya rage ban saki fitsari ajiki ba qaramin saa muka ci ba da yau mun sha maruka suka kwashe da dariya "kinga bari na wuce bazan iya jiran Aunty shahida ba daman nazo karban test din hjyrmu ne nace nazo mu gaisa kinga wucewata sai mun hadu a gida ta zame hannunta dake cikin na maryam ta wuce tana daga mata hannu , maryam ta koma cikin office zaman jiran Aunty shahida ."
Bai Dade da wucewa ba doctor shahida ta dawo ta ga wayam bashi Babu alamunsa "sarkin zuciya halan ya gaji ya wuce "eh Maryam ta fada muryarta a sanyaye "okay ta shiga tattara kayayyankinta muje kou daman akwai maganar dana so muyi mu uku Amman zanzo gobe inshallahu idan na tashi daga aiki muyi a gida "magana kuma aunty.?"ta tmbyeta a tsaro ce .
"Eh!
" wacce magana ce haka Kuma har da ya adam zaayi ?aunty shahida tace ",magana ce me mahimmam ci , dan girman Allah aunty shahida wallahi bana son duk abinda zai hadani dashi nifa tsoro yake bani culmdown my sister ki cire wannan tsoro ba wani Abu bane face alkhairi shiru mrym tayi tana nazarin maganar aunty da tunanin wacce magana ce wannan da har sai anyita da ya Adam Kuma tace alkhairi ne ...?
suna fitowa haraban asibinti suga direbansa na jiransu "a ruwa Ina mai gidanka ? sai daya rusuna mata sannan yace "ya kira anzo an daukesa da wata motar aunty shahida ta girgiza Kai ta shiga mota ita da maryam inda take fad'a mata zuwan nuzla "Ayya kanwata ai kuwa na gode sosai itama kuwa ina son ganinta nan hankalin maryam ya dan kwanta jin har da nuzla sai dai har sanda a ruwa ya sauke aunty shahida a kofar gidanta zuciyar mrym bata bar Saka da warwara ba Allah Allah take gobe tayi taji ko meye .."

washegari da misalin karfe goma na safe sakon mutuwar sadiya ne ya riski doctor shahida, tayi matukar firgita da Jin wannan mummunar labari saboda cewar da akayi yankar rago akayi mata ta zabura ta mike daga zaunen da take jikinta na rawa ......."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
Arewabooks username
Ayshabagudo

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page4

"Wani  irin   gumi  ke tsatsafowa   ajikin  aunty  shahida   yayinda zuciyarta  ta  dinga bugawa da  karfi  fiyye  da  kaida ,nan  take ta mike tsaye ta shiga zariya  a office   ta kasa  zaune ta kasa tsaye  tana  sake jin wani sabon tashin hankali   tana cikin wannan halin sai ga doctor  sa'a   ta shigo  a  rud'e  ta tsaya  suna  kallon  juna  yanayin  doctor  shahida  ya  tabbatar  mata taji abinda  ya  shigo daita office  din  dan  duk ta fita  haiyacinta ,a matukar  tsorace  aunty  shahida  take kallonta qirjinta  na  dokawa  "nasan  kinji  abinda  ya  shigo dani ? wai  an yiwa  sadear  yankan rago a gidansu."
har  lokacin  fargaba da  tashin hankali bai bar gangar  jikin  aunty  shahida  ba ,da kyar  ta iya motsa labbanta  "yanzu   doctor zinnira  ta kirani   take  fad'a min wannan mummunar tashin
hankali alamarin nan ya  d'aure  min Kai  matuka ,
hakika  mutuwar  sadear  ya gigitani  jiya  fa  iwar haka muna  tare  daita  har  tana  cewa  zatayi magana mai mahimmanci  dani yau idan mun
had'u ko me  zata  fada  min ? ta   k'arasa  maganar idanunta na ciccikowa da ruwan  hawaye "gbdy  mutuwar  mubina ce ta dawo  min , Allah sarki rayuwa , Allah  ya  jikansu ya  tona asirin duk wanda yayi  sanadiyyar  barinsu duniya  , "duniyar  nan ma guda nawa take da zaka kashe dan'uwanka ?cewar  doctor sa'a  "ya  kamata  muje gidansu   yanzu ko ? "Eh ! wannan  gaskiya  ne ya kamata muje " da sauri aunty  shahida ta tattara abubuwanta dan bata   Jin  zata dawo asibiti  daga can gidan hajiya  zata  wuce doctor sa'a  ta  nufi  kofar  fita itama  aunty  shahida ta biyo bayanta da s auri ta rufa mata baya suka jera tana kokarin neman number doctor  zinnira  suje tare ."

"Kai  tsaye gidansu sadear    dake  ijora olopa
suka  nufa   a kofar  gidan  suka  iske 'yansanda   suna tambayar  aminu   yayan   sadear  yadda  abun ya kasance  "to ni dai bazan qarar da komai  ba , kawai  dai na  tashi da asuba  na shiga d'akinta  Inda take kwana tare da yarana guda  biyu  domin suyi sallah kawai   naga gawarta   cikin   jini  amman  babban yarona  sadi  yace  yaga  bayan matar Kuma ya ganeta   duk  da   jikinta lullube yake da  bakin  kaya  ba'a iya  ganin  komai   nata ".ya qarasa maganar Idanunshi  na  sauya kala." yauwa haka muke so yanzu    Ina  yaron yake ?  police  officer ya tambayi aminu yana gyara tsayuwarsa "  kan aminu  na kasa  hawaye  na tsiyaya daga idanunshi  cikin rawar murya  yace "yana  ciki   gida  " girgiza Kai  aunty  shahida  tayi  cike da  tausayawa masa   ,."

a tsanake  suka   gaisa   sannan     gbdy   suka had'a  baki  da doctor sa'a  da  dr   zinnira sukai masa gaisuwa   "aminu  ya  qarin  hakurinmu  Allah  ya  jikan sadear Allah  yayi  mata  rahma halinta na gari ya bita  "Ameen  ya   Allah , na gode  Allah  ya  bada  lada  "Allah  ya  tona  asiri duk wanda keda  sa  hannu  a kisan sadear  ya sake amsawa da" amen
na gode Kwarai da gaske yana kukan an cucesa an rabashi da yar'uwarsa tilo ,  a  lisafinsa  yanzu   tayi  awa hud'u  a  kabarinta   shiru yayi yana juya girman  alamrin zuciyarsa na zafin da bai san ranar dainawa ba ."

"Nan su aunty shahida   suka  barsu tsaye suka  shiga  cikin  gidan suka nufi  bangaren   yayan  sadear Inda  suka tadda  tsirarun  mutane zaune 
a  cikin d'akin ana karba gaisuwa  ,a natse  suka  gaisa  da mutane tare da yi musu  gaisuwa   suka  zauna  Inda  ake  ta jimamin mutuwar kowa  na fad'ar  albarkacin bakinsa  ,wasu  na cewa ai  hadiza ce ta kasheta tunda  daman  ta furta cewar itace zataga bayanta a bayyanan  nasi    ,yayinda wasu na cewa  ba  lallai  bane ya kasance itace ta kasheta ."
Suna  zaune  police officers suka shigo tare da
aminu da yaronsa  sadi dan kimani shekaru goma shabiyu yana musu bayanin wacce ya gani ."
'yansanda na  sauraron  yaron   daki daki gefe  guda kuma  suna  dudduba   gidan  a karshe suka tsaya a kofar   d'akinsu  hadiza   tare   da   tambayar   wacce   ake   zargi da aikata kisan ."

batare da 'bata lokaci ba akayi sallama a bakin kofar  d'akinsu, hadiza  kam  tunda taji sallama police  cikinta ya duri ruwa ta soma juya Kai zuciyarta  na  tsinkewa    dan tunda  akayi mutuwar take  cikin  tsoro da matsanacin  firgici mara iyaka gabadaya komai nata ya tsaya cak ."mahaifiyarta  ce  ta amsa   sallamar  tana fitowa daga  cikin  d'akin "muna son ganin hadiza ko  tana  ciki ?"."eh  ! tana ciki   ta fad'a muryarta na d'an rawa  "hadiza  ki fito ana son  ganinki  da  kyar hadiza  ta  fito kamar wacce  kwai ya fashewa aciki   ta tsaya a bakin kofar  d'akinsu , kana kallonta  zaka fahimci  a tsorace take , sai da suka mata duban tsanake sannan daya daga cikin police  din yace "kece  hadiza  ko ? ta  gyada masa Kai alamun "eh! gabanta na faduwa da sauri da sauri suka ce "muje akwai wasu tambayoyi da zamu miki a office dinmu ."

"akan wani laifi kenan?   mahaifiyarta  tayi 
karfin halin tambayarsu".  idan  muje office
dinmu   kwaji   akan wani laifi ne " suka  tasa  keyarta gaba mahaifiyarta   ta biyosu  da sauri 
tana cewa "bazan bari  ku tafi min da yarinya ba ku zubar mata da  mutunci  ba ." jin maganar  mahaifiyarta yasa  hadiza ta tsaya cak  taki  cigaba da tafiya police suka ce "muje ko!" "shiru  tayi  jikinta  na rawa  taki motsawa daga Inda  take   aiko daya daga cikin  yar sanda mace ta rike tsintsiyar hannunta "zaki   da girma da arziki ko kuwa mu tafi dake ta karfin tsiya  ? "cike da tashin hankali hadiza ta  fixge hannunta daga hannun yarsanda  tare da marairaice  fuska  kamar zatayi kuka "ni bazani koina ba har sai na san dalilin da yasa zaku tafi dani office dinku ". zata sake magana suka daura bakin bindiga keyarta "idan kika sake furta wata Kalma zamu sakar miki  wuta  mu tasheki aiki," oya  muje  "tsimi tsimi  hadiza ta soma tafiya  mutane  gidan na kallonta  cikin tsananin farinciki dan daman taadabi kowa acikin gidan  kowa tsoronta  yake ."

"wani mummunar tashin hankali   ya   shigi mahaifiyar  hadiza  da hadizan  karon kanta, ana  k'okarin turata cikin motar  'yansanda su aunty  shahida  suka  fito suka   kama   gabansu zuciyoyinsu   cike  da tsoro  da  fargaba ,direban  aunty shahida ya  sauketa a kofar gidansu  sannan  ta bashi   umarnin   ya kai  doctor   sa'a  da zinnira ya dawo, suka yi sallama da abokan aikinta  da  zumar  sai  sun had'u gobe , Jiki  a sanyaye  aunty shahida  ta  shiga  cikin tangamemen  falon mahaifiyarta  parlour'n   shiru babu   alamun  akwai wani  bil adama   acikinsa  hatta    'yan aikin  gidan bata  ji motsinsu  ba ."
Chapter 11 · 0% Book details