← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 23 OF 100

Sashe 23

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

a hankali ya yaye rigar jikinsa sama kad'an ya d'aura hannunsa a daidai saman mararsa yana shafawa a hankali yana furzar da iska mai zafi yayinda sha'awarsa ke sake motsawa wani irin yanayi ya dinga ji a sansar jikinsa ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa a haka bacci ya daukeshi cike da mafarkinta, cikin mafarkinsa ya ganta tana gudu sosai tana haki tayi gudu sosai sannan ta tsaya ta dafe gwiwowinta da hannuwanta can sai ga wani hayaki ya llubeta ta koina a jikinta can sai kasa ta dinga budewa ta soma yin kasa tana ihu tana daga hannuwanta sama domin neman d'auki  a daidai wannan lokacin wasu mutane su uku mata biyu maza biyu suka k'araso gurin a lokacin da kasa ta rufeta mutun biyu acikin wadan mutane kuka suke sosai suna  kokarin taimaka mata ."

shi kuwa dayan wanda ya kasance babban mutun Tare da mace suka   cigaba da tsayuwa rungume da hannunwa a qirji suna dariyar mugunta "a matukar firgice ya farka yana dafe grjinsa gumi ya rufesa kmr babu ac a d'akin zuciyarsa cike da mamaki mafarkinsa na yau "Anya kuwa mutun ce wannan yarinya ?Anya maganar yan'uwa da abokan arziki bazai tabbata ba kuwa ?ba mutun bace aljana ce yarinyar nan ya furta a fili "da sauri ya girgiza kanshi "Allah bazai sa haka ba inshallahu a mutun zata kasance ,idan km mutunce hakika a duk Inda take tana cikin damuwa da tashin hankali nan take shima ya shiga damuwa da jin tsoro , ranar dai bai iya komawa bacci ba dakinsa ya koma ya dinga juyi cikin tsananin damuwa ."

washegari sukusuku ya tashi jikinsa babu kwari kana kallonsa kasan bashi da natsuwar zuciya shirun nasa ya qaru fiyye da sauran lokutan baya, mami duk ta damu da ganin yanayinsa sai dai tambayar duniya yace babu komai ya boye mata saboda muddin taji abinda ke damunsa sai ta fishi shiga damuwa yau kwana biyu kenan bai sake d'aura  maryam a cikin kwayar Idanunsa ba bai damu ba dan damuwarsa tafi rashin qaunar data nunawa yan'uwansa tana yi masa  ."

yana zaune a part dinsa yayi shiru yayinda
MB ke zaune a gefensa "ka daina damun kanka da tunani kada wani ciwo ya kamaka kasa mu shiga uku meye ma matsalarka?sai daya furzar da iska yace  "ka kasa fahimtata ne kawai  amman matsaloli gasu nan takoina kuma ace mutun bazai ji babu dadi ba.
"friend abinda zaka dinga dubawa Allah ya baka Lafiya ya baka tarin dukiya bila'adadin wanda Kai kanka baka san adadin kudadenka da gadarorinka ba ,Allah ya baka komai da komai me yakamata kayi sai ka gode masa  ?komai mai wucewa ne inji cewar MB  "to alhamdulillah na gode masa amman bangaren damuwata ba mai karewa bace.
"kaga duk wannan mai sauki ne ni sai nake ganin kamar har da rashin amincewa da aurenka da mrym yasa damuwar tayi maka yawa koma nace   yana cikin abinda ke damunka karka ji komai zanji dashi.

"Me zai sa damun tunda ba sonta nake yi ba kawai zan auri maryam ne saboda darajan mahaifiyata kuma zata kare rayuwarta a gidana sbd darajanta "Kai yanzu kana ganin zaka aureta?" zan aureta saboda sweetheart "angama zan san abun yi sun dade suna tautaunawa kafin daga baya ya mike ya fito a parlour ya iskesu har hjy zulaiheart yayi mata sallama "har zaka wuce muhammadu bello bazaka tsaya Kaci abinci ba ? a'a mami a koshe nake da zai fice daga falon yace "Maryam muje na dan ganki tace "to ! tare da d'aukar mayafinta ta yafa ta fito a haraban gidan suka tsaya ."

"wato maryam kinsan abinda yasa na kiraki ?ta girgiza masa Kai "ba'a kan komai bane sai akan maganarki da ATA me yasa bazaki amince da aurensa ba ?"banason ki rufe min komai idan kin boyewa su aunty nasan ni zaki fada min gasky menene dalili ? Numfashi ta sauke tana lumshe ido"ina jinki ? a natse ta fara mgn cikin raunanniyar murya "abu na farko ya Adam bai sona sannan abinda na fahimta kamar dole akayi masa ya aureni , ni km bazan iya auren mijin da baya sona ba gsky .

"da zai fada miki da kanshi zaki yarda ki auresa ?"a'a bazan auresa ba saboda bana son shi shima km baya sona "shiru yayi yana kallonta "ki dai yi tunani ba yabon Kai ba abokina yana da nagarta da za'a auresa ke ya'yan manyan kasar nan fa binsa suke suna rokonsa ya auresu babu wacce ya amincewa zai aura sai ke "gsky sunyi kokari da son aurensa   ni Kuma kaga banason shi zaka iya fada masa gara ya zabi daya acikinsu ya aura "bazaki duba darajan mami ba dan itace me son had'in ko shi baya so sbd mami ne ?ya fada cike da Jin haushin furcinta ."gaskiya da wahala duk ta Inda
MB ya bullo mata sai ta kawo masa hujja haka ya gaji yayi mata sallama sai dai yasan ko giyar wake ya sha bai Isa ya fadawa ATA cewar mrym bata bashi had'in Kai ba ."

washegari ranar mr ATA yayi tafiya zuwa hollond Kan harkokin kasuwancinsa gbdy   ya manta wata aba maryam a rayuwarsa harkokin gabansa kawai yake da tunanin princess dinsa ."Kwana biyu da tafiyar ATA maryam ta soma hada kayanta da abubuwa amfaninta ta fad'awa hjy zulaiheart da nana hauwa'u cewar ranar juma'a inda Allah ya kaimu zata Abuja zatayi sati biyu ta dawo "Kinsan sati biyu zakiyi shine baki bari mun tafi tare ba ?inji cewar nana "kiyi hakuri sister nayi kuskure nest time inshallahu iya haka kawai ta fad'a saboda taikaita maganar .

Ranar juma'a jirgin karfe goma tabi zuwa Abuja tana sauka ta tarar da kannenta da mahaifiyarta sunzo tarbarta dake sun san da zuwanta daya byn daya ta rungumesu ajikinta suna murnar ganin juna "nayi kewarku sosai "muma mun yi kewarki inji cewar izza ta k'arasa ta rungume mumynta dake tsaye tana sakar mata murmushi "mumy na sa
meku lafiya ? Lafiya qalau maryam ya mutanen lagos ?tayi mata tambayar tana shafa bayanta da gani kasan akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu,
Ta zareta ajikinta ta rike hannunta suka d'auki hanyar gida tun akan hanya mumy ta fara mata magana akan ATA tayi matukar mamaki da Jin tasan komai "eh haka naji sai dai gaskiya ni bana son shi dan bazai yi caring din mace ba shi kenan kullum cikin dacin rai no yayi gaba ya nemi mata nima Allah zai bani nawa mijin ."

"karki soma wannan maganar ke Ina ruwanki da dacin ransa tunda yana da kudinsa ,shi fa mai kudi sai a hankali har suka karasa gida mgn daya suke yi Koda mahaifinta ya dawo yayi murna da ganinta nan ya shiga zolayarta "Hjy mrym ko ace maryamu damtso ko amaidashi irin na turawan nan ace mary
duk ke kadai gilashina a she babban kamu kikayi alagos ? Kin tashi daga diyata kin zamo surukata matar d'ana da nake ji dashi gskiya naji dadin wannan had'in, kwarya tabi kwayar kenan kinyi sa'a da dace miji na gari .mrym ta zumburo masa baki "Allah dady ka daina cewa hk ni yarkace ba wata suruka ba km ni babu wani dacen miji danayi tsokanarta sukayita yi har dasu izza..."

"zamanta a Abuja taji dadinsa tana zaune cikin yan'uwanta cikin kwanciyar hankali da annasuwa babu tsana babu tsamgwama Kuma kullum suna waya da nana hauwa'u da hjy zulaiheart sati daya sati biyu mrym shiru taki komawa lagos tun abun bai damun hjy zulaiheart har ya fara damunta wani tunani tayi tasan halin d'anta Allah yasa ba wani abun yayiwa maryam ba kafin ya tafi hollond yasa tayi musu wayo ta koma gurin iyayenta ".

da yammacin ranar asabar hjy zulaiheart ta kirasa yana dauka tasa masa kuka "wallahi muddin baka auri mrym ba babu ni babu Kai Adamcy "subhanallah sweetheart ki kwantar da hankalinki menene ya faru kike kuka da fad'ar haka ? ni dai ka auri maryam shine kawai abinda nake bukata ,Idan km kana son kwancinyar hankalina Kuma tabbas ni ce rayuwa agareka kmr yadda kake fada lallai kayi wani Abu mrym ta dawo gidan nan sannan ka hanzarta aurenta acikin kankanin lokaci na ganta acikin gidan a matsayin surukata ". Sai daya sauke numfashi sannan yace "shikenan naji ki daina kuka zanyi yadda kike so nayi miki wannan alkwari zan aureta sai da yayita rarrrashita sannan ta sake , suna gama waya Kiran MB ya shigo wayarsa byn sun gaisa mgnr minti biyar sukayi sukayi sallama .

kullum abu daya ke damunta har yasa gidan ya fita ran mrym kullum sai mahaifiyarta ta dameta da batun ATA cikin zafin rai tace "mumy nifa inada Wanda nake so jira lokacin nake zan bashi dama ya turo" ke ban son zance banza da wofi ni na haifeki ko yar riko ce ke arzikin rikon danayi miki nace ki auri Adam zaki min alfarma ballanata ni na haifeki acikin cikina har nace ga abinda nake so kiyi min gardama to ki d'auke soyayyar wancan ki maye na adam agurin dan dashi za'a yi babu fashi munafukar Allah butulu kawai , shiyasa kika wani tattaro kika dawo nan? " to dan ubanki sai kin koma tana gama fad'ar haka taja tsaki tana zuba fada ."
Chapter 23 · 0% Book details