← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 5 OF 100

Sashe 5

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Maryam dake kitchen wacce daman idanunta da hankalinta yana parlour ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, da sauri ta qarasa inda nana take tsaye "sister na shiga uku nah" ta fada tana riko hannun nana cikin nata "me kuma ya faru allah ya rabamu da shiga uku sister ?"kalli can ki gani sister ta nuna mata parlour'n "me ya faru ? "sakon Ana's ne daman ya turo min text message zai zo ya kawo min gift gsky al'ameen bai kyauta min ba maimakon ya kirani ya bani a hannuna tana magana idanunta na cikowa da ruwan hawaye hjy zulaiheart ta juyo a natse ta dubesu "ku kuma lafiya kuka tsaya kuka hade kai wa ya mutu ? a matukar firgice suka juyo suna dubanta maryam na 'kokarin dauke hawayenta a d'an rikice suka girgiza mata kai alamun "babu kowa " to meke faruwa daku ?babu komai suka sake hada baki "to allah yasa babu komai din amman ni dai na fahimce da komai tsayawa sukai suka qasa cigaba da aiki ."

shi kuwa Mr ATA naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske yana shan yaji kamar yadda ya saba sosai ya tsurawa box din dake dauke da sunan maryam da kallamar happy birthday yana lissafa abubuwa dayawa acikin ransa "wai gashi inji Ana's sakon hjy maryam "ya maimaita abinda al'ameen ya fad'a , kafin daga baya ya kwabe baki tare da kai hannu ya bude box din ,da wani hadadden freme idanunshi ya soma cin karo mai matukar kyau da d'aukar hankali an rubuta sunanta da larabci da kuma hausa ."
"shiru yayi yana jin wani iri a gabadaya ilahirin jikinsa na tsantsar bakinciki ,a hankali ya dinga kallon abubuwan dake cikin box din mug, pray mate ,Casbaha alqurani da wani qaramin greating card na sokon taya murnar birthday sai kuma qaramin yellow takarda mai dauke da kalaman soyayya "ya dauka yana tabe baki kamar yaga wani mugun abu ya soma karantawa ."

hjy Zulaihat ta fito daga kitchen tare da masu aiki mutun biyu zuwa dining maryam da auta suka biyo bayanta jikinsu duk a sanyaye dan basu san abinda zai faru ba "na shiga ukuna sister ki taimakeni karanta sakon fa yake " maryam ta sake fadan hk cikin tsananin tsoro "to sai me idan ya karanta ? " wallahi kin cika abun ban haushi kamarki dan an aiko miki da sako zai zama abun tashin hankali? Ke yarinya ce karki manta master's gareki kuma dole zakiyi aure "ni sister rabani da wani master's na yarda kowa ya karanta sakon amman ban dashi "bangane banda shi ba ? shi waye naki da zakice ban dashi ? tayi mata tmbyr tana kallonta "haba sister ya kike yi kamar baki san abinda nake nufi ba kema kinsan ba haka nake ba ni ba matsoraciya bace amman wallahi shi mugun tsoronsa nake ji ,sannan kinsan halinsa da disgi ."
"Dana san halinsa fa ? shi zai auremu?Ko kuwa munyita zama haka kenan bazamuyi aure ba ?"Kinga idan zaki cire tsoro ki cire dan ni wallahi ina samun miji aurena zanyi na barki bazan zauna ba aiki ba aure ba dole zanyi daya ta qarasa mgnr tana jan tsaki maryam tace "banza kamar kema ba tsoronsa kike ba "ina jin tsoronsa amman ban kai ki ba dan dani anas da abbas suke mutuwar só da son aure da tunin ina gidan daya daga cikinsu "ta fad'a tare da qarasawa wurin Hjy Zulai ta rabe a gefenta."

daga can inda hjy zulai take tsaye ta hangosa ya baje kayan sannan yayi zurfin cikin karata yellow takarda "Lafiya adam !? ta furta tana cigaba da dubansa ,a tsanake ya mike tsaye fuskarsa a yatsine ya nufo wurinta yana cewa "wani haukan shirme nake karantawa ".maryam tayi wuf ta koma kitchen da sauri tana daura hannuwnta duka bisa kanta itama auta tayi nesa da hjy zulaihat "haukan shirme kuma adam ? hjy Zulaihat ta maimaita abinda ya fad'a "yes sweetheart wannan bashi da maraba da haukan shirme ,wai nmj né zai zauna yana wannan haukan abun kunya kawai "yayi maganar yana yatsuna face dinsa kamar yaga wani mummunar abu "wannan ai iskanci ne ba soyayya ba ya sake mgn yana jan dogon tsaki  ."
hjy Zulaihat tayi shiru tana duban mr ATA cikin tsananin tausayawa kanta dashi kanshi ,"bata san ranar da zai canza wannan mummunar halin nasa ba ,bata san ranar da zai bude baki yace ga matar da yake so ya aura ba ko fad'awa soyayya "duba ki gani sweetheart ya mika mata letter yana sake jan tsaki kamar wanda akayiwa dole sai ya karanta."
Jiki a matukar sanyaye mami ta karbi letter daga hannunsa tana dubawa gabadaya bata ga inda zantuttukan dake rubuce sukai kama da haukan soyayya ba ,illa ma maganar soyayyar mai sanyaya zuciya da kwantar da hankalin abokin rayuwa , byn ta gama karantawa ta kalli nana hauwa'u fuskarta dauke da tmby, kai ta gyada mata "mami sakon maryam ne "wani mugun kallo ya wurga mata wanda ya hargitsa hantar cikinta da mugun sauri ta bace masa da gani ."

sai lokacin Hjy Zulaiheart ta fahimce abinda yasa taga hankalinsu a tashe a kitchen ,numfashi ta fesar tana kallon bayansa dan tuni ya juya ya koma inda kayan suke tare da rike kugunsa ,qarara ake iya ganin bacin ransa bancin alqur'ani dake cikin kayan daya banka masu wuta gabadaya ya kona dan takaici ." wannan shine soyayya ta gsky da gsky yaji sautin muryar mahaifiyarsa tana magana tana tahowa zuwa in da yake "duk abinda ka gani anan kyautatawa ce ta soyayya tare da nuna kulawa "okay yanzu ta haka ne zai nuna emotiona dinsa ?kai gsky dai wasu mazan jakai ne, ya fad'a yana jan tsaki tare da nufar hanyar step har yayi taku biyu yaji mahaifiyarsa ta kira sunansa "adam !."
cak ya tsaya tare da juyowa ya tsura mata kwayar idanunshi da suke cike da bakinciki" zaka iya kin yarda da wannan kalaman amman at least kayi respect din emotion din wani ,karka wulakanta soyayyar wani domin bakasan yadda taka soyayyar zata kasance ba ,idan kai baka raayin soyayya karka ji haushin masuyin soyayya domin soyayya maganar Allah ce ."shiru yayi lokaci daya emotion din mafarkinsa ya shiga kai kawo a gabadaya ilahirin jikinsa ,mafarkin ma ya daukesa da mahimanci fiyye da komai arayuwarsa  wannan tunanin yasa ya bude bakinsa da kyar "alright sweetheart amman yana da kyau idan har soyayyar gskiya ce ya turo magabatansa "ya fadi haka ne saboda ya gaji da ganin fuskar maryam din acikin gidan  dan bai san dalilin dayasa ta tare masu a gida ba ,a natse ya juya ya cigaba da taka step fuskar yarinyar mafarkinsa na yawo acikin kwayar idanunshi yayinda mami tabi shi da kallon tausayi  tana girgiza kai ."

Sallamar abida né yasa mami ta dauke idanunta daga kallon hanyar da mr ATA ya bi ta maida bakin kofa tsaye take hannunta rike da hannun yesmin sanye cikin doguwar riga yar saudiya mai tsansi sosai cike da sakin fuska mami ta amsa sallamarta tana mata sannu da zuwa "yauwa mami fatan kin tashi lfy ?" ta fada tana zama cikin daya daga cikin kujerun falon .mami ta qaraso ta zauna kusa daita tana kamo hannun yesmin a lokacin mrym da nana hauwa'u sun gama tattara kayan ."
a mutunce suka gaishe da aunty abida sannan suka bar wurin zuwa dakinsu nana hauwa'u na cewa "ai kin dai ji abinda ya Adam yace ?me yace sister ? ban gane me yace ba yanzu ke bakiji yace idan soyayyar gaskiya anas yake miki ba ya turo magabantasa ba ?"oh ! abinda ya fad'a kenan ai gabadaya rudewar da nayi bai sa naji komai ba?ta numfasa sannan ta cigaba da magana "wannan ai ba matsalarsa bace idan naga dama na zauna har karshen rayuwata babu aure bai shafesa ba ,yadda bai son ana shiga lamarin rayuwarsa bai dace shima yana shiga rayuwar mutun ba ".

oh! ai bansan wuyanki ya isa yanka haka ba amman zo muje ki fad'a masa kar ya sake shiga rayuwarki"
nana hauwa'u ta riko tsintsiyar hannunta ta nufi step din da zai kai mutun samansa ,nan take maryam ta zaro idanuwa waje "haba sister kar muyi haka dake mana wannan ai maganarmu ce " a'a babu wani maganarmu ce Ke dai muje kinga daga yau zai kiyaye ,maryam ta fixge hannunta da karfi sauran kadan kwalin hannunta ya subuce "haba sister ! haba sister Ko gskiya? shegiyar masoraciya kawai iskancinki baya qarewa akan kowa sai akanmu yake qarewa dasu anas."maryam ta kwashe da dariya "ai kema Kinsan oga nada ogansa, ina ni ina tarar aradu da fad'in kai ai sai ya tarwatsani , barni na tsira da raina da lafiyata kar ya rage min sadaki suna tafiya suna magana kuma duk akan mr ATA ne ."

shiru aunty abida tana zaune har kusan mintuna shabiyar sannan ta dubi mami da kyau "wai ina ATA ne nasan yau asabar yana gida dan duk kwanakin nan bana ganin shigarsa da fitarsa ?"kullum sai yesmin ta tmbyeni shi shiyasa ma yau nace bari na kawota ta gaishesa tunda weekend ce ta fad'a tana murmushi ,mami ta gyara zamanta tana kallon fuskar yesmin "Adam yana nan galau yanzu nan ma ya hau sama ,kwana biyu da bakya ganin shigarsa da fitarsa yanayin aiki ne kwanakin nan duk bai dawo wa gida da wuri haka zalika da wuri yake fita amman yau kam yana gida bana tunanin ma zai fita dan ma ya dauko rigima ai da kin samesa a kasa .
"Rigima kuma mami kamar wani qaramin yaro ?ta fad'a tana murmushin farinciki".
"wallahi fa nan mami ta zayyane mata abinda ya faru, dariya aunty abida tayi sosai "lallai kam rigima amman ai wani lokacin akan gsky yake abubuwansa ni wallahi yana matukar burgeni yadda yake gudanar da rayuwarsa babu ruwansa da kowa sannan baya daukar raini kamar su abban yesmin koda yaushe hakoransu a bude Kmr masu tallar close up ."
Chapter 5 · 0% Book details