← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 34

Sashe 9

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Page 17&18
Tana idar da sallah office din dr zubair din ta tafi knocking tayi shigo kawai ya furta dan yasan ita ce waya yake magana suke dashi sai kuma ya katse wayar ya kalleta inaya me kika fadawa innarki shiru inayar tayi zubair ne ya kara jefomata tambayar inayace tace dr nafada mata abinda ya faru hade rai yayi ke inaya wayace ki fada matane ita ta tambayeni yallabai to dan ita ta tambayeki sai ki fada mata inaya kisan abinda kike fa dr dan allah kayi hakuri yanzu ya jikin innarta wa da sauki ya bata amsa yana mai kallon wayarsa yana dannawa hawayen da suka zubo mata ne yasa tace bara naje naganta ko kallonta bai ba yace ba barinki zasuyi ba saboda nace kar wanda suka bari ya shiga yallabai dan allah tsawa ya daka mata tashi ki bani guri dan allah dan allah yallabai inaya kifita nafada miki ko tashi tayi ta fita ta zauna akan kujerar dake kallon office din nasa kifa kanta tayi tana kuka wiwi...
Can kuma ta tashi tana tafiya dakin da aka kwantar da mahaifiyarta lekawa take amma bataga kowa ba ganin haka ne yasa ta juya da niyyar tafiya gidan su intisar amma wata zuciyar na hanata wata zuciyar na tinzira ta fitowar ta tayi dai dai da shan gaba da wani saurayi yayi mata cike da murmushi tsayawa tayi kawai tana kallonsa inaya ya furta hakan cikin sanyi murya amsawa inaya tayi naam am dama dama kallonsa tayi cike da takaici kaga malam dama me yi magana kai tsaye mana cike da murmushi mai kayatarwa yace ea inaya tin ranar dana fara ganinki zuciyata ta kamuda sonki inaya ina matukar kaunarki inaya murmushi tayi to bawan allah nagode amma ban katseka ba shin a ina ka ganni har kasan sunana sannan kai ya sunanka saurayin ne yace ni sunana Ibrahim kuma naganki ne a lokacin danai miki horn har kika bani hakuri sannan na san sunanki ne kodan basai na boye miki ba kinmanta da cewa shi masoyi inaya ce ta katsesa shikenan nagode amma yanzu zan je wani waje zuwa gobe sai mu hadu ok shikenan inaya amma baki bani amsa ba sai gobe kawai ta furta ta kara gaba.....
Intisar na zaune tana nunawa hajiya indo dinkinta data karbo gani take tana cewa yanzu intisar saida kika wannan dinki har biyu to tinda waccen yar matsiyatan kunyi haka yanzu wazaki bawa kallonta tayi umma zan bawa hafsat ne fa hajiya indo ce tace yayi kyau ai yanzu kingane karatun ko sallamar da akeyi ce ta katse su da hirar intisar ce tace umma kamar fa muryar inaya umma ce ta tashi dan tabbas ta gane muryan shigowa inaya tayi tana shigowa umma ta daka mata tsawa kifice min daga gida ko yanzu nasa a koreki inaya ce tai murmushi umma kisani fa shi arziki nq alah ne kun konemin dakin daga baya kuka rugumana gida intisar ce ta matso ke dallah dakata cewar intisar tsayawa inaya tayi ke har kya fadamana gida inaya na kone dakin meye a dakin naga dik a dakin meye na amfani naga ai ni nai miki dinkin ko dan haka wallahi dan mun ruguje gida wannan ba abin mamaki bane aikin banza wai ke inaya meye a gidan idan ba tsiya ba ai kamata yayi kimin godiya dana ruguje inaya ce ta kalli intisar tace tsiya fa kikace intisar wai intisar meye yake damun kwakwalwarki ne ko kin fara haukane bani da labari intisar ce tace ni kike kira mahaukaciya to ki sani uwarki ce mahaukaciya bani ba cikin zafin nama inaya ta fizgota ta shako mata wuya wallahi intisar sai kinyi dana sanin hajiya indo ganin ta shake wa intisar wuya zuwa tayi ta fara kokarin janye wuyan yarta ganin abin yaki cinyewa ne yasa ta komawa ta fara kiran waya...
Dr zubair ne a zaune sai kuma yake tinanin ko ina inaya tayi nakasa jin motsinta tin dazu wata zuciyar ce ta sanar dashi ai dama abinda kayi mata baka kyauta ba wata zuciyar na fada masa ya tafi ya dubota amma wata zuciyar na hana sa tashi yayi ya fito harabar hospital din amma wayam to ina yarinyar nan ta tafi ne ya ambaci hakan sai kuma ya koma zuwa office din sa....
Inaya kawai sakin intisar tayi tana mai goge hawayen face dinta yayi intisar nagode ni kikewa zagarwa iyaye kisani bazan rama ba saboda nasan darajar iyaye kuma kisani wannan uwar taki ita kika zaga aikin banza fitowa tayi daga cikin gidan tana goge hawaye tana tafiya tana kuka dik da ba sosai take ganin gabanta ba tafiya take a hankali wata mota ce ta taho ta hasketa take ta rufe fuskanta da hannuwanta sai ji kake kitt......👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°

Page 19&20
Dr Zubair yana zaune yanasa ran ganin inayah amma shiru jin shirun yayi yawa yasa shi fitowa wani massenger ya kira ya basa wata takarda ya kwatanta masa inaya sannan yasa kai ya fice....
Intisar mamamkin inayar take da har ta iya shake mata a wuya a gaban mahaifiyarta kodan ta kyauta ai tinda ni na zagi mahaifiyarta sai kuma taja tsaki aikin banza aikin wofi wallahi inayar yanzuna take wasan....
Ikram ne ya fito a mota yanawa inaya sannu dago kai tayi tare da murmushi yallabai kayi hakuri laifinane da na shiga gaban mota kuma ai kanata min horn ni bansan ba kanayi ya hakuri dan allah tsayawa kawai yayi yana kallonta sai kuma yace ai bakomai nima ai da laifina murmushi kawai tayi to ni zan tafi ok badai kiji ciwo ba eaa tabasa amsa tana mai wucewa ta kusa da shi murmushi yayi aai kuma ya koma mota yana tafe yana sake sake yayin da inaya tayi hanyar ta ta komawa asbitin.....
Inaya tana isa office din dr zubair ta nufa a zuciyar ta tana cewa ai dai yanzu nasan ya huce ba tana shiga taga wayam ba kowa fitowa tayi kawai tayi tana kallon wajen tayi massenger daya bawa sako ne ya taho sai da suka gaisa sannan ta mika mata takardar sannan ya juya bude takardar tayi abinda ke ciki inaya dan allah kiyi hakuri dazu nadau zafi ne nai miki wannan fadan amma ina mai baki hakuri akan hakan amma dan allah kisan abinda zaki fadawa innarki saboda ciwon hawan jinin dayake damunta kinji inaya ki kula da innarki ni zan wuce ne gida wannan kudin kuma kije kisayi abinci da ruwan da zaki ci sai kisaiwa innar sannan kuma kije pharmacy ki bashi wannan takardar ta nade zai baki wasu magungunan idan taci abinci ki bata maganin tana zuwa nan tai murmushi linke takardar tayi ta dau karamar tai hanyar pharmacy sai murmushi take ita daya....
Dr zubair ne suke waya da ikram zubair ne ke cewa aa ikram wallahi bata fadan yadda abin ya faru ba naje na tarad da mahaifiyarta ba lafiya shine kawai nafasa ok shikenan zubair amma ya kamata fa asan abinyi a gidan daka saka su zubair ne yace eah ba matsala ai wannan ai shikenan sai da safe zubair ya tambaya har zai katse sai ikram yace zubair yau dai shikenan dai kawai sai mun hadu murmushi zubair yayi ikram nasan dai ba zancen mace bane ai ikram bansan ranar da zakayi aure ba kai kowacce mace batayi maka ko murmushi mai sauti ikram din ya fitar bazaka ganeba zubair sai gobe ma hadu idan zamuje wajen bikin ahmad da haka kawai zubair ya katse wayar zubair ne yaja numfashi ni ina mamakin wannan halin na ikram ace kai kowacce mace batayi maka allah kasa ya samu wacce yakeaso ko ya samu yayi aure haba...
Inayace zaune a dakin ita da innar ta suna hira sama sama saida tai sallar isha'i sannan suka fara shirye shiryen kwanciya.....
Washe gari tinda sassafe intisar ce zaune akan gadonta waya take itada hafsat,intisar ce tace hafsat yaushe kike ganin zamuje gidan bikin nan daga dayan bangaren dai banji mai akace ba kawai dai murmushi tayi ta katse wayar...
Dr zubair ne yayi parking a lokacin inayace ta fito ganinsa da tayi ne yasa ta tsayawa da murmushi matsowa tayi yana fitowa tace dr ina kwana kallonta yayi da murmushi lafiya laou inaya ya jikin inna Alhamdullh ta basa amsa tana cewa kawo jakan yallabai to yace amma yanzu ina zakije ne gida zanje nadakkowa innata kaya ok shikenan kinga da kin iya mota da nabaki amma dik da haka karbi kudin napep din nan murmushi inaya tayi ai dr akwai sauran chanjin jiya zasu isheni dr ne yace naji zasu isheki amma kuma abinci fa sosa kai inaya tayi ta fara kame kame dariya abin ya basa allah ya shiryeki inaya karbi ki wuce murmushi kawai tayi ta karba tare da furta nagofe dr allah yasaka maka da alkhairy ya baka mata ta gari murmushi yayi amin inaya....👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
Chapter 9 · 0% Book details