← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 34

Sashe 5

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tsaye take sai safa da marwa inaya take yayin da hajara ke zaune akan kujera abinda ya faru a yau inaya take tinowa ganin magariba tayi ne yasata juyawa zata huce likitan daya fito ne yasa ta dawowa tana furta likita ya mai jikin kallonta yayi ku kuka kawo ta eaa ta bashi amsa kibiyoni office dina ok yallabai tafiya yayi juyowa tayi ta kalli hajara dn allah maman saif bara naje nadawo shikenan inaya amma nima gida zan tafi nasan yanzu su saif sun dawo daga makaranta shikenan maman saif nagode sallama sukai da ita sannan inaya ta nufi iffice din doctor din a zaune ta tarar da shi yana da sallama ta shiga yallabai gani kallon ta yayi yawwa abinda yake damun ta ciwon hawan jini yayi matukar hawa sosai amma mun samu ya sakko yanzu dan haka ki hanzarta ki sayo wannan magungunan yanzu karbi,karbar takardar tayi godia tayi masa sannan ta fito da dan gudunta pharmacy ta shiga ta basu takardar sai da suka hada mata sannan ta basu wasu 2k dake jikinta kallonta mai pharmacy yayi ke baiwar allah kudin maganinki fa 8k naga kin bani 2k karbi kudinki da takardarki ki kara gaba ba yanda ta iya haka ta fito tana ta bulayi unguwar su ta nufa ta koma gida sai a sannan ta tina abinda ya faru da ita na kone mata daki da intisar tasa akayi dakin inna ta shiga tana neman kudi amma ko sama ko kasa babu fitowa tayi ta rasa yadda zatayi makotansu ta shiga gidan hajara a tsugunne ta ganta tana alwala lafiya inaya cewar hajara yawwa maman saif dan allah ki taimakamin da rancen 6k dan allah zan siyawa innata magani ne rike haba hajara tayi ni hajara yanzu inaya ina naga 6k wallahi bani da kudi kuma shikenan maman saif bakomai sai anjima a Soron gidan ta jingina tana tinanin inda zata samu wannan kudaden jin maganar hajara ce tayi matukar bata mamaki fitowa tayi ta koma gidan nasu a wannan daren haka ta karade unguwar tana neman rancen 6k amma ta rasadaga masu zaginta sai masu ce mata allah ya kara wayace tayi kawance da 'yar mai kudi ganin bata samu bane yasa ta nufar asibitin office din dr tai knocking shigo ya bata amsa shiga tayi sai dai ta gansa da wani a zaune ya juya baya dr ne yace yawwa inaya kindawo ina magungunan idanunta ne suka ciko da kwallah dan allah likita ka taimaka min what inaya me kike nufi ne kina nufin sai dai ni nasiya miki maganin karki manta fa ni aikina ceto ne gaskiya bazan iya ba dan haka ki fita rokansa take amma ina yace ta fita dan haka ta fita mutumin dake zaune ne ya juyo fari tar ga manyan idanu kyakkyawa ajin farko a cikn samari masu matuqar kyau kallon hanyar yayi sai kum ya kalli dr haba Zubair bansanka da haka ba kasani murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo dr yayi kasani Ikram bani da halin dazan iya biya mata kudin magani kuma wannan ma fa na sati daya ne bawai na dindindin ba wanda aka kira da ikram din ne yace good ba matsala ni zan sayi maganin daga nan har lokacin da zataji sauki amma a tinaninka meya kamata nayi dr ne yace aa hakan da kayi shine dai dai ikram bakomai allah ya kara Budi dariya yayi kajika sai kace ba abokina ba ni yanzu zan wuce katuramin account number sai nasa maka kudin maganin insha allahu allah ya kara mana lafiya ameen dr ya amsa sanann ikram ya fito shida doctor inaya ya gani a tsaye har zai kirata sai ikram ya masa nuni da aa karka kirata kaji banason tasan ni na taimaka mata kawai nafison ta gani kamar kai ne sai da dr zubair ya rakasa har gaban motor sannan ya dawo har lokacin inaya na tsuggune dr zubair ne yace wa inaya,inaya bani takardar kinji cike da zumudi ta mika masa ganin ya nufi hanyar pharmacy ne yasata share hawayen fuskarta a lokacin nurse ta leko tana mata magana tashi tayi ta shiga inna ce ta farka cike da jin dama dama a jikin nata inaya tana ganinta ta fashe da kuka innata ta furta tana kuka a lokacin dr zubair ya shigo duddubata yayi yaga jikin nata da sauki sannan ya ajiye mata magungunan inaya ya kalla yawwa ki bata abinci yanzu sai ki bata magungunan sai kuma kizo office dina ki sameni to ta amsa tare dayi masa godiya a sannan ta tina da cewa fa ita bama ta kawo abinci ba inna ce tace inaya baki dakko abinci bane ba wai ea ta bata amsa sai dai naje nadakko shikenan inaya kiyi sauri kinji to ta bata amsa ta juya ta tafi......
Intisar zaune akan kujera tana kallon mahaifiyar ta umma nifa wallahi na yanke hukunci a gobe zan fara gasawa inaya kasa a hannu sai tasan ta taba intisar murmushi hajiya indo tayi yawwa inaya ko kefa aini naga kokarinki da kikai kawance da 'yar talakawa me talaka yasani daya wuce kayi musu rana su kuma suyi maka dare ai dik inda marar mutunci yakai to talaka ya wuce me ake da talaka,talaka ko dan iska murmushi intisar tayi ganinan kanki inaya zaki gane cewa kin taba intisar.....👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
Chapter 5 · 0% Book details