← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 34

Sashe 8

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Page 15&16
Inaya ce zaune akan dardumar data idar da sallar magariba inna ce ta tako taho sai kuma ta zauna tana furta sannu inaya,inyace tace aa inna ai ke zanwa sannu yajikin naki ne inna da sauki innar ta bata amsa sai kuma inayar tayi shiru tana kallon innar dan tasan tabbas akwai wata tambayar da inna keson jefo mata kamar daga sama taji innar tace inaya meyasa muka dawo nan da zama inaya mai ya samu gidan mu ne wai inaya ba tambayar ki nakeba shiru inaya tayi tana kallonta....
Ikram ne yace ba komai zubair ni nayi alqawari cewa zan taimaka musu amma ni bazan kyale zalunci ba dik da bansan meya hadasu ba zubair ne yace ya kamata ka tashi muje gidan tare ikram ne yace aa kaga ni bata sanni ba kai ta sani kuma kaga kai ta yadda da kai dan haka nikam bazani ba sai dai kai kaje zubair ne yayi dariya ai shikenan ikram zubair ne ya tashi bara natashi nidai natafi ikram ne yace ina zuwa tsayawa zubair din yayi can sai ga ikram ya fito da kudi a hannunsa zubair na wakiltaka kaji kai musu komai da kaga ya dace a garesu sannan idan kaji musababbin abinda ya faru kazo ka gayamin ko zuwa gobene zubair ne yace shikenan ikram sai da safe ko ikram din ya fada zubair ne yace to gwauro tinda kaki aure ba murmushi ikram yayi sai kuma yace kafi kowa sanin halina fa zubair.....
Intisar ce ta koma cikin gidan hajiya indo ta gani akan kujera kallon up and down tayiwa intisar din take tasha jinin jikinta tsaki hajiya indo taja ko kefe intisar ga yaran masu hannu da shuni amma kin tsaya kina kula wannan shegiyar yarinyar da akomai kin fita yanzu dai ba wannan ba yaushe za a nemo inda inayar ta shiga ne very soon umma abinda intisar din ta fada kenan ta wuce....
Inaya ce tace inna kowa da kaddararsa ko innace ta bata amsa da eah mana inaya lafiya inna kinsan bazan miki karya ba inna wallahi abinda ya faru shine sai kuma inayar tayi shiru innace ta tambayeta wai inaya bada ke nake ba ko dai ba lafiya ba aa inna lafiya amsar da inayar ta bata shikenan to menene inna sun ruguje mana gidanmu inna,innace ta dafe kirji tare da furta inalillahi wa inna ilaihi rajiun inaya me kika ce gyada mata kai inayar tayi ita kuma ta juyar da kai tana kuka juyowar da zatayi innace a kwance ba ta motsi wani marayan kuka inayar ta saki tana jijjigata jin shiru ne yasa inaya tashi da gudu ta dakko buta tazo ta watsa mata ruwan wani dogon numfashi innar ta fitar kai da gani kasan na wahala ne da kyar take iya magana inayace ta furta inna inna inna kina jina kuwa dan allah inna kiyi magana jin shiru ne yasa inayar tashi da gudu tai hanyar fita dai dai kofar gidan aai ji tayi ta bige wani daga kan datayi ne yasa ta gane ashe dr zubair ne hawayen dake fuskanta ta rage dr zubair ne ya kalleta inaya lafiya dai ko inayar kasa magana tayi tana nuna masa cikin gidan shima bai magana ba ya wuce ciki a kwance yaga innar inaya kamata mu tafi asibiti wannan ba mai kinji kamata sukai shi da inaya yasata a mota sannan inaya ta shiga suka tafi asibiti.....
Intisar ce zaune akan bed dinta tana kallon Pictures din wayarta sai a lokacin ta kula da da sauran pic din da sukai ita da inaya kalla tayi cikin farinciki ta ke kallonsu sai kuma ta furta tabbas inaya ina sonki amma daudaukar fansa ba zaisa na kyaleki ba a lokacin kiran suraifa ya shigo wayarta dagawa tayi sai kuma tace ok gani nan katse wayar tayi wardrobe ta bude ta dakko mayafi take idanunta suka kai kan kayan da suke iri daya da inaya rufewa tayi ta fito har lokacin umma na falo intisar ce tace umma zanje wajen suraifa amsar dinki dan allah dan aramin car dinki mana ok shikenan ki dawo da wuri insha allah umma intisar ta fada dauki key din gashinan murmushi intisar tayi ta dauka ta wuce.....
Suna zuwa asibiti direct gado aka dakko musu na marasa lafiya kai tsaye dakin marasa lafiya aka shigar da ita yayin daya tsayar da inaya a waje...
Intisar wajen suraifa taje mamaki suraifa tayi ganinta batare da aminiyarta ba suraifah ce ke tambayar ta ina inaya tabe baki intisar tayi munyi fada intisar ta bata amsa suraifa ce tace intisar kamar ya kunyi fada kinmanta wacece inaya a wajenki ne tsaki intisar taja aikin banza ke dallah suraifa ki tashi ni fa na tsani zancen inayar nan ki tashi ki dakko mini dinki na na kara gaba karbi kudinki suraifa ce tace intisar karki manta kawancen ku tin kuna yara ne karki batasa akan tsaki intisar taja da allah suraifa kibani ni na huce suraifa ce ta tashi ta dakko mata dinki ta warta tayi ta kara gaba....
Inaya ce tsaye jin ana kiran sallar isha'i ne yasata tafiya bakin famfo na cikin asibitin tadauro alwala dawowa tayi ta tsaya can kuma sai ta fara tinanin anya wannan kayan nawaa zasuyi sallah kodan ai ba wata najasa ce a jikinsu ba dankwalin kanta tacire ta shimfida ta tada sallah tana tayarwa dr zubair na fitowa ganin tana sallah ne yasashi shima tafiya office din nasa.....👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
Chapter 8 · 0% Book details