← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 34

Sashe 25

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
57&58
Inna ce bayan ta gabatar da sallar la'asar ta juya ta kalli inaya tana ta latsa waya inna ce ta rike baki tace ohhh ni wai yanzu inaya sai kin lalata wayar nan bazaki tashi ki tafi kasuwa ba ne dariya inaya tayi tace ai inna ke nake jira ki idar da sallah fa shisa kawai nake wannan game din inna ce to naji yanzu tashi ki shirya, inaya ce ta kalli inna tace dama inna inaso muyi magana kinga ikilima ce tazo gayyata ta rabon chewing gum gobe wai na bikinta inna nikuma ina tsoron wannan kawancen inna kinga dai a sanadin KAWANCEN Mu dubi yanzu yadda Mike da intisar fa inna,innace tace haba inaya ai wasu sun banbanta kamr yadda ba hali daya bane tsakanin ikilima da intisar dan haka kawai kije ba abinda zai faru insha allahu ki dai ki dogara ga allah inaya ba wata matsala inaya ce tace to tashi tai ta shiga daki, ajiye wayar tayi ta dauko hijabinta ta saka tare da gyara fuskarta a tsakar gida ta tarar da inna kawai tace to inna natafi sai na dawo ko...
Fitowa tayi sanye da wata shadda brown tasha aiki sai dan karamin mayafi a jikinta jin falon shiru ne yasa ta kalli hafsat tace bara naje naiwa umma sallama ko daga mata kai hafsat kawai tayi tare da zama tana kallon television....A kwance ta ganta intisar ce ta matsa kusa da ita sai tace umma ni zan tafi amma da wuri zamu dawo kallonta tayi tace shikenan sai kin dawo 'ya ta allah ya tsareki ameen kawai tace ta amsa ta wucewarta tana fitowa suka dunguma ita da hafsat suna tafiya....
Ikram ne a tsaye bakin wani katon fili hakan nan ikram yaji wajen ya birgesa kallon attahir yayi yace wannan filin fa attahir ne yace na wani alhaji ne filin nan shekara da shekaru anki a siyar dashi anki kuma a gina sa murmushi kawai ikram yayi yace ni to zan siyesa indai za a sayar min attahir ne yace kamar ya kallonsa ikram yayi yace wannan fikin yayi matuka sosai zan iya amfani dashi wajen ginin campany da zan sakeyi a nan garin attahir ne yace shikenan tinda yayi maka ka shirya nan da gobe sai na kaika wajen mai filin ko daga kai ikram yayi yana kallon wajen wucewa sukai sukaci gaba da zagayawa....
Inaya ce tafiya take a ranta tana tina ashe fa anyi bikin zeeyah amma ita ta manta tsabar ta shiga busy shiru inaya tayi tace tabbas dole kuwa naje gidan ta nan da gobe idan ba haka ba wallahi nasai wa kaina problem wajen zeeyah...Daidai lokacin da zata tsallaka ne wani mai mota ya taho ya kusa bige ta mutanen wajen ne suka fara cece kuce amma ganin motar mai tsada ce yasa suka juya akalar maganar zuwa wajen inaya daya ne yake fadin ke wace irin mace ce ne ba kya kallon gabanki ne wai kallonsa tayi sai kuma tai shiru, parking mai motar yayi ya fito kai da gani kasan yasha yayi tatil sai tangadi yake mutanen wajen ne suka fara masa kirari, kudi ya debo ya basu karasowa yayi saitin inaya ya kalleta yace kee wacece wata harara inaya ta banka masa zuciyar ta kamar ta fito tsabar bakin ciki kallonsa tayi tace shashasha kawai mara amfani ji be ka ayi magana kace kai ai dan mai kudi ne to me kudin ya amfana maka dan shaye shaye kawai, dariya yayi yace yammata tsaki inaya taja ta wucesa ganin haka yaja motarsa ya fice yana layi....
Inaya tin da ta taho take magana aikin banza kawai wai mutum yanzu dan yana da kudi shikenan sai ya kashe mutum ba tare da daukar wani kwakkwaran mataki ba muddin kuwa haka za ai baza a taba ganin daidai ba a rayuwa...
In'am ce zaune akan kujera tana kallo a television dakin wata yarinya ce ta shigo in'am ce ta kalleta tace to ki shigo mana kika tsaya a tsaye yarinyar bata fi in'am din ba zama yarinyar tayi in'am ce tace yaya sunanki ne Hameeda ta bata amsa kallonta kawai tayi ta ci gaba da kallonta...
Bayan sallar magariba ikram ne zaune akan katifarsa yana danna waya kiran inaya yayi amma ba a daga ba sai kawai yaci gaba da uzurinsa inaya ce ta dauko wayar kallonta tayi taga missed call dan zaro ido tayi sai kuma kawai tace ya kara kira bata rufe bakinta ba sai ga wani kiran daga garesa...dagawa tayi tare da sallama a bakinta amsawa yayi ba laifi sun gaisa, ikram ne ke tambayar ta ko da wani abu hakan dai ta kara ce masa ba wani abu kam kallon wayar ikram yayi yace shikenan inaso zamuyi magana amma sai na dawo ko to kawai tace sai da safe sukai ta katse wayar tare da sauke ajiyar zuciya...KAWANCEN MU
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
AUNTYNNMU
Chapter 25 · 0% Book details