← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 34

Sashe 6

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Page 11&12
Inaya tana dawowa sai da komai ya kammala sannan ta nifi office din dr zubair bayani yayi mata yayi da inaya take ta zuba masa godiya shi abin ma har mamaki ya basa harda kuka da kyar ya yasata tafi murmushi yayi yay dialing number ikram kaduba WhatsApp naturo maka wani abu ok ya katse bayan 2 minute sai ga kiran ikram a handsfree yasa wayar hello ikram ikram ne yace zubair wannan addua da godiyar fa daka turo min nawaye murmushi zubair yayi ikram nakane mana ka tina yarinyar daka bawa kudin magani dazu har zuwa lokacin da mahaifiyar zata warke shine fa nake fadamata amma kaduba kaga irin wannan adduar datakeyi maka murmushi mai sauti ikram yayi shikenan zubair yanzu ka bisu kaga inda suke zama idan an sallamesu idan yaso idan akwai abinda suke buqata ka mini magana shikenan ikram abinda dr zubair yace kenan ya katse wayar.....
Washe gari tin karfe 10 dr zubair ya sallami su inaya ganin zasu tafi ne yasa yace aa bara nazo nakaiku tinda kinga ita ba lafiya ba dik da inaya tayi kokarin hanasa amma shi yace sai ya kaisu saboda aikin da ikram ya basa daukarsu yayi ya nufi unguwar tasu tin daga can nesa inaya take hango mutane ba abinda ta ambata sai inalillahi wa inna ilaihi rajiun inna ce ke tambayar ta lafiya amma tace inna bakomai fa inna cike da masifa tace kuma shine kike min wannan sallalami ko ya hakuri inna dik da hankalinta nakan jama'ar data ga ni a kofar gidan nasu parking dr zubair yayi a lokacin ikram ta fito cike da bacin rai mutanen wajen ne suka fara matsa mata hanya abinda tagani ne yayi matular girgizata kenan mai hakan ke nufi gudanmu ta ambata amma ko ina a baje yake da kasa zaman dabaro tayi a kasa tare da furta nashiga uku intisar me nai miki haka mai na aikata miki kikemin haka cikin bajajjiyar kasar ta shiga ta ciro iya kayayyakin data iya gani zubair na hango inaya yasa yacewa inna karki fito ina zuwa to tace dashi yayin da ya nufi wajen inaya tambayar ta yake amma yace bakomai yanzu karka bari inna tasani inba haka ba wallahi zata iya mutuwa dan allah shikenan inaya amma mai ya faru ne zan fada ma abinda ya faru yanzu dai ina zuwa inaya tace dik da yana tambayarta ina zata amma ta wuce mota ya shiga yabi bayanta inna kuwa ganin ta kusa ganewa yasa yayi mata allurar bacci saboda alqawarin da yayi wa inaya...
Inaya tana zuwa gidan su intisar shiga tayi kai tsaye yayin da zubair ya biyota yana kwala mata kira tana shiga direct palourn su ta shiga ta tsaya ganin intisar inaya ce ta kalli intisar hawaye na zuba yanzu kin kyauta intisar mena aikata miki haka har kike min wannan abin mai gidanmu yayi miki da zakisa a ruguje har kibarwa mutane sallahun cewa kece kika aikata intisar why menai miki kukan da take yasa intisar tabe baki bansani ba inaya inaga kinfi kowa sanin abinda kikai min kuma nafadamiki sai na dau fansa wallahi inaya ko ina kika shiga a fadin duniya sai na nemoki mari na fa kikai ke ko ubana bai taba marina bareke banzar bazara dan na zagi uwarki hawaye inaya ta goge naji nagode intisar kisani akwai allah kuma nagani wannan shine sakayyar kawancen mu dake nagode har ta juya intisar ta tsayar da ita ke ki sani wannan yanzu na take wasan wallahi sai na hanaki zama lafiya kinjiko bata ce da uta kala ba taci gaba da tafiya ta fito dr zubair ta gani a tsaye kiranta yake juyowa tayi nagode dr dan allah mukoma ka sauke innata kai sai ka wuce muna bata maka lokaci fa cewar inaya....
Gidan nasu suka koma inaya ce tace kawai ka ajiyemu dr anan ba matsala kallonta yayi cike da tausayi sai kuma yace aa inaya idan na barku anan Ina zaku zauna ina dai zan kaiku hawayen dake gangaro mata ta goge bakomai dr bamu da kowa anan garin 'yan uwan innata dik basa raye sakamakon gobarar da akayi sai kuma 'yan uwan mahaifina nafi shekara 12 rabon dana gansu kawai dai yanzu ka ajiye mu ko ina ne zan nemar mana sai mu zauna sunkuyar da kansa yayi sai kuma ya juya kan motar ya nufi wata unguwa can saman unguwar su inaya dai dai wani dan karamin gida ya tsaya sauka yayi sai kuma yayi wa inaya magana inaya karbi wannan keys din ku zauna anan gidan kinji zuwa anjima zanzo insha Allah kallonsa inaya tayi yallabai karmu zamar maka nauyi fa ga kudin magani ga taimakon da kayi ga kuma gida murmushi dr zubair yayi bakomai inaya komai zaizo da sauki ku zauna anan insha allah bazaku zamarmin nauyi ba sannan zan zo anjima dan jin ya haka ta faru ki kula kinji to ta amsa masa sannan ya saukesu inna kuwa sai raba ido take ganin wani gidan so take ta tambayi inaya amma kuma so take sai ta zauna....
Hafsat ce zaune tana dariya intisar ce ta shigo kiran hafsat tayi,hafsat ce ta tafi intisar ce tace yanzu inaso mu zama kawaye nasan da cewa kin tsani inaya ko inaso mu hada deal mu hanata sakat kinji banason kuma ta sani murmushi hafsat tayi indai wannan ne shi yafi komai sauki yanzu dai yaushe za a fara dan wallahi na tsani inaaya...👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
Chapter 6 · 0% Book details