← Book details Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 34

Sashe 15

Kawancen Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

KING AND QUEEN WRITING
...King and queen writing Chamber...
°**Sarki da Sarauniya**°
31&32
Inaya ce dauke da leda ta shiga cikin gidan tana a shiga ta tarar da inna a zaune kan tabarmar da aka shimfidawa dr zama ita ma tayi kusa da ita inna ce tace inaya ina kika tsaya haka ne murmushi tayi tace innata bakomai pah dama kawai motar tasa ce tadanyi nisa da gida tinda kinga tana akan titi suka tsaya to shikenan inaya yanzu wannan ledar kuma waya baki dariya tayi kawai inna sai da nace bazan amsoba dr yace sai na amsa sai dai idan nadawo ki dakeni haka yace murmushi inna tayi yayin da tayi ta kwarara masa addua inaya na amsawa da ameen bude ledar inaya tayi cije da murmushi katon kwali ne a sama an rubuta cosmetic cike da zumudi ta bude kayan kwalliya ne a cikin wani dan abu gasu nan birjik ajiyewa tayi ta zaro kayan masha allah kayan sawa ne irin dogayen rigunan nan 2 sai abaya itama 2 sai atamfa kuma 1 sai wani hijabs 2 da takalmi 1 inaya murna kawai take tana nunawa inna itama sannan daga baya ta tashi ta nufi dayan dakin ita da innar.......
An kai amarya gidan ta lafiya lou kowa fuskarshi da farin ciki idan ka cire intisar data sha maruka 2 hafsat data lura da ita yasa tace intisar ki saki ranki mana kinji tsaki taja sannan tace wallahi sai nayi masa abinda yafi na inaya zai gane koni wacece hafsat ce ta rike baki aa intisar ko ba komai inaya macece wannan fa namiji ne dariya tayi ke dalla bakisan kaidin mata bane sai na tarwatsa rayuwar sa ni intisar da haka dai suka tsaya sai wajen 11 abokan ango suka zo su zubair ne a gaba sai hayaniya suke shikuwa ikram yana baya ba abinda ya ce musu suna shiga ya hango intisar tsaki yaja wannan dai inaga mayyace haba zama yayi can nesa dasu sai da aka gama siyan baki sannan kowa ya fara watsewa ikram ne ya fara yi musu sallama sai zubair ya tashi tare da fatan alkhairi da kuma zuri'a dayyiba ikram na mota zubair ya shigo yana dariya har zai mai magana ya fasa tada mota yayi intisar ya hango wani kakkauran tsaki yaja kana kallon idanunsa kasan ba mutunci yaja motar ya bar wajen......
Kwance take akan gadonta tayi shiru sanye take da kayan bacci irin riga da wandon nan rufe idanunta tayi sai kuma ta bude su tarr tashi zaune tayi ta janyo wayarta karfe 12:00 dan karamin tsaki taja ta furta wai meye hakan dik wannan marukan dana sha meye sa zuciyata take makale dashi ta tambayi kanta sai kuma tace kuma gashi ba sona yake ba ni intisar ya zanyi da soyayyarsa ganin fa dagaske baccin ba zuwa zai ba yasata mikewa ta janyo wata drawer magani ta dauka tasha ko 10min ba ai ba bacci ya dauketa....
Washe gari tin asuba inaya ta tashi sai wajen larfe 6:30 ta fito kai markade tayi sa'a ba layi har ta dawo ta hada wuta inna tana jinta sai a lokacin itama ta fito inna ce ta karbi sakin kosan ita kuma inaya ta dawo wajen zubawa inayar ta kalli inna tace inna kinga ma kadan na debo waken 2 na raba sa innace tace ea hakan ma yayi inaya ai kinga farkon yi ne eaa inaya ta bata amsa har sai da aka kusa gamawa sannan yan makotansu suka fara zaryar zuwa siya dik da haka bai kareba ganin bai kare bane yasa ta juyesa a bokiti ta fito bakin titi ta zauna tana saidawa a haka har ya kare ta taho gida....
Ikram kwance akan gado idanunsa a bude sanye yake da jallabiya blue fuskarsa dauke da murmushi ya furta inayah sai kuma yayi shiru tashi zaune yayi to kenan wannan itace wadda nake taimakawa a dalilin zubair sai kuma yayi murmushi amma fa labarin nan nasu da rikitarwa amma zan je naji labarin a bakinta dan dik abinda zubair yake fadan jinsa kawai nake kiran daya shigo ne yasa shi kallon wayar MyCwet💕 aka rubuta da dan murmushi ya daga yana aa mycweet yau kin makara wajen tashina wadda aka kira ce cikin sanyin murya tace to naji dai my bro wani wai my cweet so kake budurwarka ta jini ko tasa a kulleki kodan kuma fa my bro bashi da budurwa murmushi ya saki yace kuma dai kinba kanki amsa itama dariya tayi tace my bro dama uncle ne yake nemanka yace nakiraka kazo yau zakuyi magana dashi to ya bata amsa anjima zanzo to bro bye sai kazo da haka ya katse wayar yayi lamo kallo daya zakayi masa kaga yana cikin tinani can kuma ya mike tsaye ya shige toilet....
Inaya tana dawowa wanka tayi ta dauki wannan abayar da zubair ya kawo mata jiya ta saka maron color tayi matukar yi mata kyau hijab din ta janyo tasaka ta fito har gaban mahaifiyarta taje tace to inna ni zan tafi makaranta inna ce tace to inaya haka zaki ba littafi dan murmushi tayi eaa inna idan naje zan ara wajen ilham to inaya sai kin dawo ki kula kinji allah ya tsare ya baki abinda kikaje nema ameen ta amsa ta fito tai hanyar makarantar....👩‍❤️‍💋‍👩💕🖤KAWANCEN MU💕🖤👩‍❤️‍💋‍👩
Writing and Story
🍁Waleedah Muhammad🍁
🌷AUNTYNMU🌷
Chapter 15 · 0% Book details